50

227 42 10
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*(50)*
"me ake nufi kenan?, gaba ɗaya babu abun da na gane ku fahimtar da ni". Cewar Kaka Tabawa. kuma har yanzu kan Ahmad na ƙasa bai ɗago ba, haka kuma Zulai da ke tsaye tun shigowarta bata iya samun wuri ta zauna ba.
Yayarta wadda su ke uwa ɗaya mai suna Lubabatu ta rangaɗa guɗa tace,"aini Alhamdulillah, wannan abu yayi dai-dai...dama ina Amadu ina auren ƴar zina, Allah ai ba azzalumin bawansa bane, shi yasa ya sauya komai tun ba'a cuci kamilin yaro ba, idan auren ya zama dole a yau ga Hannatu nan ƴar'uwarka Allah sa muku albarka". tana yin shiru mahaifiyar Zulai Kaka Tabawa ta amshe,"to ni dai nama rasa abun cewa, amma ni ban gamsu da wancan dalilin nasu ba, meye wani ƙwayar halitta bata zo yanda akeso ba? dama can basu yi niyyar baka ƴarsu bane shiyasa, abun da suka so shi ne su ɓata maka suna su goga maka baƙin fenti, a cusa zargin wani abu a zuciyoyin mutane akanka, ga shi kuma sunyi nasara...amma banda haka sun san da zasu yi wannan binciken tun can farko me yasa ba'ai ba sai a ranar yau...ko kai acikinsu kwai wanda yace maka kaje kayi gwajin ƙwayalar halittar taka?". nan ma Ahmad ɗin shiru yay bai ce komai ba, sai da ta ɗaga masa murya tukunna,"Amadu bafa da kujerar nan nake magana ba, ka bani amsar tambayata". ya ɗago da jajayen idanuwansa ya dubeta yace,"ko kusa babu wanda ya tunkareni da wannan batun, abu guda ɗaya ne yake nan, kawai dai na gamsu da hujjarsu. sai dai mene yasa za su bawa Kabir ita? hakan shi ne adalci? mafita ce za'a samar ta hakan? me yasa basu bawa Jawad ita ba? wannan ai cin fuska ne, nayi soyayya da ita sannan shima yazo ya aure ta?". a zafafe yake maganar kuma cikin ɗacin rai da zafin kishi. Zulai ta numfasa sannan ta dubi ɗanta cike da tausayawa, murya a matuƙar sanyaye tace,"Amadu da ilminka, dan haka ka tsayar da tunaninka da iliminka a wuri guda ka auna, idan da Allah ya rubuta Maryama matarka ce Amadu ba ƙwayar cutar halitta ba, ko menene babu abunda zai hana fasuwar aurenka da ita...Matar mutum ƙabarinsa, ka ɗauki hakan a matsayin ƙaddararka, sai ka roƙe shi ya sauya maka da mafi alkhairinta, baka san wane tanadi Allah yay maka a gaba ba...ni mahaifiyarka ce, a kullum adu'ata akanku Allah ya haɗaku da abunda yake alkhairi agareku, ya kuma nisanta tsakaninku da abun da yake ba alkhairi bane agareku...damuwa ko ɗaga hankali ba su zasu baka Maryam ba, basu zasu dawo maka da Maryam ba ta ƙarfi da yaji, ka zama mai haƙuri da tawakkali sune suturarka". ji yake kamar yay kuka a wannan lokacin,"to amma Inna saboda rashin dacewa sai a ɗauki yarinyar da ansan nayi soyayya da ita kuma a aurawa Yayana, mene hikimar yin hakan? ba'a tunanin yanda zan dinga feeling a zuciyata idan ina ganinsu tare, me yasa ma Baba zai yarda da hakan, ba sai ya ƙyalesu su maye gurbina da wani can daban ba". "ni dai na faɗa maka Amadu, idan baka ɗauki maganata ba zugar zuciya zata kaika ta baro ka...Umarni ɗaya zan baka shi ne kar naji kar na gani, ka miƙe ka tashi ka tafi wurin ɗaurin auren Yayanka kamar yanda mahaifinka ya umarceka, kar ka taɓa bari huɗubar shaiɗan tayi tasiri a zuciyarka ta ɓata kyakykyawar alaƙar da ke tsakaninka da ɗan'uwanka, jini yafi ruwa kauri dan haka mace karta zama silar rusa tsakaninku, ka gane me nake nufi, idan har ka ƙetare gaskiya da shawarar da na ke faɗa maka kuma, danasani ce zata zo bayan aikata ba dai-dai ba, kuma wata ƙila anan ubangiji ya nuna min ishara ne". sai kawai ta fashe da kuka, kuka irin me ban tausayin nan, tasa hannu ta rufe fuskarta, inda hankalin Ahmad ya ƙara tashi, ya baro kujerarsa yazo ya kamata ya zaunar da ita, cikin muryar kuka taci gaba da cewa,"a baya na yiwa Maryam asirin kan ba zata taɓa aure ba, yarinyar nan baiwar Allah bata tare min komai ba amma ni da ƴaƴana muka sa mata ƙahon zuƙar hassadarmu...a ƙarshe saboda tasirin adu'oin tsarin da takewa kanta da wanda Suwaiba da Akila suka dage kan yi mata shi ya karya asirin, boka ya tabbatar min da karyewar asirin dole sai ya taɓa ƴaƴana uku, kuma bayan na tuba na nemi yafiyarsu ban faɗa da wannan ba balle suce sun yafe min, na ɓoye saboda ina ganin kamar saboda shi ɗaya za su iya cewa basu yafe ba...ban yarda da maganar boka ba sai da akazo ana saka ranar auren Adawiyya sama da sau uku tana rushewa, Jamila ma ya zama a ranar aurenta yaron yace ya fasa, ananne na fara shiga tashin hankali saboda asirin da nayi akan Maryam kenan, asirin tozarci ba wai ya zama sam sam babu mai zuwa yace zai sota ba, a'a zata samu masu sonta kuma har ta kai ga ranar aure amma a ranar ace an fasa, wanda silar wannan baƙin cikin ya iya zama ajalinta da mahaifiyarta...shi yasa da naga hakan akan Adawiyya da Jamila nayi hanzarin komawa wurin boka amma na tarar ya mutu...ashe Amadu kai ne zaka zama na ukunsu". muryarta ta sarƙe inda ta ƙara fashewa da wani kukan. "nayi danasani, nayi nadama, Allah na tuba...tabbas Allah ba ya yafe hakkin bawa akan bawansa, Amadu a wannan gaɓar ba zan iya tozali da bayin Allah nan ba, ka nema min gafarar Maryam dan Allah, ko lamura sa samu su daidaita".
sai kawai idanunsa suka bi bayan mahaifiyarsa da kallo a sanda ta miƙe har san da ta bar ɗakin, wani ɓari na zuciyarsa na ƙara faɗa masa ba lallai sai bawa ya aikata wani laifi ba sannan ubangiji ke jarabtarsa, sau da yawa ana shirya faruwar abubuwa amma ubangiji kan juya lamarin, wanda kai bawa baka isa ka tuhumi ubangiji akan hakan ba.
yaja numfashi ya sauke, Allah ya sani yana son Maryam, amma a yanzu dole yay haƙuri da rashinta, dole ya koyi wannan haƙurin da ya gani a tare da Kabir, wanda ya jima da fahimtar cewar yana son Maryam, sai dai bai san dalilin da ya hana shi furtawa ba...kuma dalilin ganin wannan kwantaccen son a tare da Kabir ɗin, da ita kanta Maryam ɗin da bata tantance irin son da take yiwa Kabir ɗin ba, dole tasa shi hanzarin furta mata nasa son tun kafin Yayan nasa yay masa shigar sauri, saboda a lokacin ya naji kamar ba zai iya zuba ido wani ya mallaketa ba, shi yasa tun a asibiti a amsar da ta bawa mahaifiyarta lokacin data tambayeta me yasa take son Kabir ɗin yay saurin sauya ma ta tunani, dan karma wannan nazarin da yaga tanayi yay tasiri akanta, kuma shi yasa bai yi sanya ba a lokacin da ta amince masa wajen koyar da ita zazzafar soyayyarsa, ta yanda za tayi saurin mantawa da Kabir da tunaninsa, ta kuma yi mugun sabon da ba zata iya rabuwa da shi ba, duk da yasan ta amince ne ba dan tana so ba a lokacin, sai dan babu yanda za tayi, abunda kawai zuciyarsa ta faɗa masa shi ne, zai aureta ko da bata son nasa, idan yaso bayan anyi auren zaiji da wannan, shi yasan yanda zai yi ya koyar da ita sonsa, dalilin da ya sa ma kenan tana furta ta amince bai yi wata-wata ba ya zube gwiwoyinsa a ƙasa ya nemi alfarmar Baba akan asa masu ranar aure nan kusa, yasan a hakanne kaɗai zai gama da ita da dukkan wani lissafinta, shi dai ya san yana son Kabir, amma ba zai iya sadaukarwa da Kabir ke yi ba akansa.
ya miƙe jiki babu ƙwari, ya miƙa hannu ya ɗauki babbar rigarsa ya saka, sannan ya dubi su Habib muryarsa a sanyaye yace da su,"ku tashi mu tafi". ya faɗi hakan yana mai tafiya zuwa hanyar fita, tafiyar yake kamar mara laka ajikinsa, Allah kaɗai yasan me yake ji a ƙasan zuciyarsa, abubuwan da suka wakana ajiya ne kawai ke haska masa a idanuwansa, dinner ɗin jiya, da kuma yanda suka gama tsara yanda rayuwar aurensu zata kasance.
a lokacin da suka ƙarasa bakin mota yasa handky ya goge tarin ƙwallar da ya kasa riƙeta, sannan ya shiga motar Mubaraq yaja su.
yana jiyo muryar Yagana a lokacin da ta taho zuwa sashensa tana faɗin,"to Allah na tuba mene na ɗaga hankali tun da ga dalili an bayar, ai da basu bada wani dalilin nasu me ƙarfi ba ni kaina Amadu sai nace an maka rashin adalci, kuma sai inda ƙarfina ya ƙare dan wallah ko ba Kabir suka bawa ba sai na ƙwato maka matarka balle kuma sun wullata hannun wanda nasan na isa da shi...haƙuri kawai za kai Allah baka wadda ta fita, ubangiji ai da zuciya yake amfani zai kalla kyawun zuciyarka ba zai barka kai kuka ba".

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now