44

142 20 4
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._

*(44)*
"Maryam za ki aure ni?". tambayar ta ƙara fitowa kamin rufewar idanuwana da buɗesu.
bai nisa ba ya ƙara cewa,"Dan Allah kice min eh, kice musu kin amince, ki faɗawa kowa kin yarda dan Allah. na gama shirya rayuwata da ke Maryam, duk wani plans nawa na gaba na gama tsarasu da ke, wallah ina sonki, kuma so nake na aureki. i cant imagine this life without you Maryam, tun daga ranar da komai ya bayyana kika samu muhalli a zuciyata, i love you, i love you so much". harufan ƙarshen suka fito tare da ɗauke hannuna da yake daga saman ƙirjinsa ya sarƙe yatsunmu wuri guda ya damƙe hannuwanmu sose, ya kafe ni da idanuwansa da haskawar wani abu da ban taɓa gani ba a ƙwayar idon wani mahaluƙi.
ina iya jiyo yanda ƙafafuwana suka shiga rawa a wannan lokacin, da yanda jikina ya ɗauki kyarma gaba ɗaya, naji wucewar wani dunƙulallan abu ta maƙogwarona da ban san mene shi ba, a lokaci guda murfayen idona suka haɗe, wani duhu kuma ya shiga haskawa cikinsu, sannan a hankali kuma kalaman Ya Ahmad su shiga maimaituwa cikin kaina. _"Maryam za ki Aure ni? aurenki nake so nayi, i love, i love you so much."_ maimaituwa kalaman suke kaman a lokacin ne yake faɗa min su, ƙara shiga suke ta cikin kaina da tunanina da wani irin tasirin da ke ratsa ko'ina a jikina. iyaka abinda na sani a lokacin shi ne Al'ameen kawai nake so, kuma ko a halin da nake ciki kalaman Al'ameen ɗin da na Ya Ahmad ke kamanceceniya suka gauraye su na amsakuwa a kunnena.
sannu a hankali sai naji duka kalaman Ya Ahmad ɗin sun gushe daga tunanina, zuciyata kuma ta shiga harbawan da zan iya rantsewa na kusa da ni su na iya jiyo sautin ƙararta. na buɗe rufaffun idanuwana na ɗorasu akan fuskar Ya Ahmad da har yanzu bai ɗauke idonsa akaina ba, fuskarsa cike da fargaba, kallona yake da irin tasirin shigar wani abu ta babban yatsan ƙafata zuwa tsakiyar ƙoƙon kaina.
_"na rasa da me zamu biya waɗannan bayin Allah'n da suka mana halacci a rayuwa, Maryam na rasa da me zan saka masu."_ maganar Ummi ta haska a cikin kaina, a washe garin ranar da ta dawo daga india. idan ban manta ba abin da laɓɓana suka furta mata a lokacin shi ne,"Ummi ai mun biya su, ko su bana tunanin su na ƙara saka ran wani abu daga garemu, mun saka masu da abin da basu taɓa haskowa kansu ba". kuma tun daga lokacin da na buɗe baki na fara maganar kallona ta ke da murmushi a fuskarta, har san da nayi shiru ta ɗora da cewan,"Maryam gidan nan da muka basu gani na ke kaman bamu basu komai ba har yanzu, gani nake dama can sunfi ƙarfinsa, Maryam so nake ace yau sun bijiro min da wata buƙata tasu a wurina da zan iya basu kai tsaye, su nemi abin da nasan ina da shi, abin da nasan bai fi ƙarfina ba...". kuma a lokacin bata ƙarasa faɗin abin da zata ce ba Alhassan ya tari numfashinta da faɗin,"Ummi ko Maryam suka nema za ki iya ba su?". kuma ina iya tunawa da amsar da na ba shi a lokacin na cewan,"ai dama ni tasu ce, har abada tasu ce ni". yace,"ina nufin fa Baba ya nemawa ɗaya daga cikin yaransa aurenki, za ki amince Maryam?". abin da Alhassan ya furta kenan, kuma a lokacin ido kawai nasan na iya binsa da shi, ba tare da laɓɓana sun motsa ba har na furta masa wata kalma. Aure! Aure! a wancan lokacin ban bawa Alhassan amsa bane saboda nasan maganar da yayi ba magana bace mai yiwuwa, sai kuma gashi a yau ɗin kuma a yanzu ba Baba bane da kansa, ɗansa ne da kansa a gabana, yake neman yardata akan aurensa, a gaban Baba da Yagana, haka zalika a gaban Ummina da ke jiran wannan lokacin.
Ya Ahmad! Ya Ahmad dai mutumin da shi ya kaini makaranta, da kuɗinsa na fara karatun boko, to shin dama ni wacece da har zanƙi amsar wannan tayin nasa? na girgiza kaina a hankali zuciyata na faɗa min cewar Maryam ke ba butulu bace. ko da baice min ya fara sona ba tun a ranar da ya san haƙiƙanin alaƙar da ke tsakanimu, zan amincewa aurensa ko da a yanzun nanne yaji ya fara sona, ko da za'a min auren dole da Ya Ahmad bana sonsa ba ya sona tabbas zan zauna da shi, tun da har ya kasance shi ɗin jinin Baba da Yagana ne.
na taɓa cewa Alhassan da Mami duk wani abu da zai sa a binciko asalina to ina gudunsa, zan kuma kaucewa duk wata hanya da zata zama sanadin hakan, dalilin bincikar asalina yasa bana sha'awar yin aure kuma na cire ran yinsa har ƙarshen rayuwata. Abin da Umm ta faɗa min a wannan lokacin shi ne,"Maryam idan har za ki ci gaba da dasa wannan abin a ranki to kuwa kina tare da ɓacin rai har ƙarshen rayuwarki, ki manta da komai tun da komai ɗin nan ya rigada ya wuce, ki fuskanci sabuwar rayuwa da kika shiga a yanzu, kiji daɗinki da kwanciyar hankalin da kika samu...kuma abin da nake so na jadddada maki shi ne Aure ko kina so ko ba kya so Maryam sai kinyi, saboda haka ki tsayar da zuciyarki akan Jawad muddin da gaske kina tsoron duk wani abu da zai tono asalinki, dan shi ne wanda ba zai taɓa goranta maki ba, shi yafi dacewa dake a yanda kike, saboda haka ki yarda ki zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya ke da shi tun da acikin danginki yake...idan ba ki sa ni ba ma ki sa ni Jawad ba tun yanzu ne yake sonki ba, tun ranar da ya fara ɗora idonsa akanki yaji yana so ya aureki, ba tare da ya duba banbancin da ke tsakaninki da shi ba, abu ɗaya ne kawai ya jinkirtar da shi akanki Maryam, karatunki! kuma a yanzu da komai yazo a gaɓar da ya tsara, ya furta miki ya kuma sanar da Mai Martaba dan haka ki yiwa kanki karatun ta natsu ki tsaida zuciyarki da tunaninki akansa, ina ƙara faɗa maki da Jawad kaɗai za ki kasance ki tserar da kanki daga wani ƙalubale na asalinki".
ofcourse i know rayuwar aurena da Jawad ta dace dan shi ne rufuwar asirina, to amma a yanzu da nake tsaye gaban Ya Ahmad bana tunanin ko wannan mutumin da Ummi ta bani labarinsa ne zai zo wurin nan a yanzu ya furta min da bakinsa cewar zai aureni zan amince masa, wannan mutumin da Ummi tace ya so ni tun kamin na zama cikakkiyar mace, ya ɗau shekaru goma yana ƙaunata duk da yasan wace ni, ya ɓoye hakan a ransa da zuciyarsa ba tare da ya furta min ba, ba wai dan son da yake min yana da tangarɗa ba, a'a sai dan saboda tsananin soyayyar da yake min, gudun kar ya buɗe min zuciyarsa rayuwata ta faɗa cikin garari idan na gane wace ni, Ummi ta faɗa min tun kafin na san asalina na fara zubar da hawaye shi yake zubar min da nasa, hawayen da yake yinsu akan abu biyu, tausayina da kuma tsananin ƙaunata. mutumin da yace mata ko daga sama aka jefoni zai aureni, ba zai gujeni ba, ba zai taɓa ƙyamatata ba, illa ma yayi dukkan mai yiwuwar da zai yi ya gusar da duk wani dattin baƙin ciki daga zuciyata, ya tsaya min tsayin daka wajen ganin banyi kuka ba dai-dai da second 1, burinsa shi ne kawai yaga laɓɓana na talewa da murmushin farin ciki da jin daɗi a kullu yaumin, ya mantar da ni ƙalubalen da ke cikin rayuwata, ya faɗa mata ya ƙara nanata mata rashina zai iya yiwa zuciyarsa illa._
_"son Maryam zai min illa idan har na rasata Ummi"._ waɗannan kalaman kullum su yake faɗawa Ummi cikin raunin zuciya. kuma a wannan lokacin da Ummi ke ban labarin mutumin da ban san da shi ba naji ina sonsa, har na iya ce mata tace da shi yazo ga Maryam tasa ce.
sai dai a yanzu ko da shi ɗinne yazo bana jin idanuna zasu iya kallonsa ma ballanta har na miƙa masa zuciyata nace zan aure shi, naji ya so ni tsawon shekaru goma, kuma ya so ni tun ban zama mace ba, ya ƙaunace ni duk da ya san asalina, amma a wajena nafi ganin girman soyayyar da aka fara yi min ita cikin lokaci kaɗan, soyayyar da bata haura watanni biyar ba, soyayyar Ya Ahmad ta fiye min duk wata soyayya bayan ta iyayena.
"Maryam abin da nake so kawai ki faɗa masu shi ne kin amince za ki aureni, ki bar batun kina sona ko ba kya sona ko taya za ki fara sona, zanji da wannan agaba, ni zan koyar da ke soyayyata idan mun kasance a inuwa ɗaya".
maganar Ya Ahmad ɗin ta katse min duk wani tunani nawa, kuma maganar tasa da ta ƙara ɗauke komai da ke cikin kaina, wani dunƙulallan abu ya tokare min a ƙirji. _"Halacci! Halacci Maryam!"._ harafai biyun da suka dira a raina kenan, ban san taya akai ba sai kawai naji saukar hawaye a saman kumatuna, na sauke ganina akan tafin hannun Ya Ahmad da ke tallaɓe da haɓata, kafin naji laɓɓana sun furta,"Ya Ahmad na amince zan aureka". furucin da ya fito a hankali kuma suka shiga raɗau a kunnuwan kowa da ke wajen.
sai kuma naji zuciyata ta matse, irin matsewar da ban taɓa ji ba, har ina jin kaman zata faso allon kirjina ne ta fito ta tarwatse a ƙasan gabana. babu zato naji Ya Ahmad ya ƙara janyoni jikinsa ya kwantar da kaina saman chest ɗinsa yana furta min kalman,"thank you". da alama ya manta da mutanen da ke wajen balle yaji kunyarsu, ko kuma yana ɗaya daga cikin mazan da basa shayin nuna soyayyarsu akan abin da suke so a gaban koma wane.
a wannan lokacin idona na kan Ya Kabir ne da ke kan kujera kusa da Ummina, kansa yana kan wayarsa yana shafawa, farin hannunsa tar acikin hasken fitilun da suke gauraye a parlon, kallon zoben hannunsa nake da ƙyallin haskensa ke hasken ido a duk san da na kalla na yatsana da ya saka min tun kafin Mairo tasan wace ita. a wannan lokacin babu abin da nake so sama da Ya Ahmad ya sakeni na ƙarasa gaban Ya Kabir, na duƙa a gaban ƙafafunsa, na miƙa hannuna na riƙe nashi ko ya samu ya tsaya daga karkarwar da naga yana yi a yanzu, nasa ɗayan hannuna na ɗago da fuskarsa na ƙarewa wannan handsome face ɗin nasa kallo kamin nace da shi ya buɗe idanuwansa da suke a kulle ya faɗa min damuwar mece nake gani a saman fuskarsa da tayi yawa haka. idan da so samu ma na kwantar da kansa a ƙirjina na dinga shafa sumar kansa har zuwa san da zai sauke ajiyar zuciya ya buɗe laɓɓansa yace min Maryam komai ya gushe, babu damuwar, babu ɓacin ran, komai ya tafi, na daina fushi da ke, zan dawo asalin Ya Kabir ɗinki.
ashe abin da ban sa ni ba shi ne, wannan kallon da nake masa har nake ayyana wasu abubuwa shi ne zan iya kira da kallo na ƙarshe, dan tun da Ummi tace,"Masha'Allah, Ahmad na baka auren Maryam". Baba kuma yace,"Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa". Yagana kuma tai guɗa, kunya kuma tasa Ya Ahmad ya sakeni. a wannan sandarewar da nayi ina kallon lokacin da Ya Kabir ya taso kaman a fusace, ya kuma zo ya wuceni kaman wucewar guguwa, na kuma ji san da zafin hucinsa ya sauka ajikina kaman garwashi, na kuma ga dawowarsa parlon bayan fitar da yay ta mintuna 2, ya miƙawa Ya Ahmad key ɗin dana ji ƙararsa ya dawo ya kuma wuceni a zafafe.
daga wannan fitar, kuma wannan ranar ban ƙara ganinsa ba, har muka baro bichi muka koma abuja bayan bikinsu Mami, na taho makaranta, akasa ranar bikinmu naje ethiopia nayi kwanaki duk ban sashi a idona ba haka ma muryarsa. sai dai abin da har zuwa yanzu ban gane ba shi ne me na yiwa Ya Kabir a rayuwa?. da naga kamar banda damuwa da hakan kawai sai nayi wancakali da Ya Kabir daga duniyata, na ƙanƙamo ƙaninsa na riƙe, kuma zazzafar soyayyar da Ya Ahmad ke nuna min ta mantar da ni ma wani abu Ya Kabir da Rayuwarsa, alwashi ɗaya da na san na ɗaukarwa kaina shi ne, ko bayan aurena da ƙaninsa ba zai ga fuskata ba a matsayina na matar ɗan'uwasa, haka ma ba zai sami girmamawan nan ba ta sirikantaka balle ta ƙanwa...domin tuni na riga na gano musabbabin dalilinsa na fita a harkata, na tsanata da ya ɗorawa kansa, ai da hankalina, komai ya sauya ne tun daga ranar da ya san wace ni, ranar da kowa yasan sai da akayi zina aka samar da Maryam, illigitmecy shi ne dalilin tsanata da Kabir yay, kuma banga laifinsa ba dan irinmu abin a ƙyamata ne, sai dai abin da bai sa ni ba shi ne wannan shegiyar da yake ƙyamata a yanzu yana cin arziƙinta ne ta wani ɓangaren, don haka kaf duniyata Kabir na ɗaya daga cikin mutanen da bana ƙauna.
bayanin da naji matar da ke cikin tv na kwararowa su suka yanke min tunanin da nake yi, na baro tunanin bichi da abin da ya faru a cikinta, na dawo qatar da kuma abin da ke wakana yanzu a cikinta, na tattara hankalina gaba ɗaya ina sauraron abin da balarabiyar matar ke cewa a tashar aljazeera cikin harshen larabci, kuma tun a kalamar Genotype ɗin da ta ambata allon ƙirjina ya girgiza sakamakon tunawa da saƙon Daddy.
_"Dukkan ɗan Adam Allah Ya halicce shi ne tare da wasu ƙwayoyin halitta waɗanda su ke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake, ƴaƴa su na samunsu ne daga irin nau'in wanda iyaye suke da shi, idan iyayen suka zama da nau'i mai kyau, za su haifar da ƴaƴa lafiyayyu, idan aka samu akasi kuma za su haifi ƴaƴa masu rauni da matsalar Amosanin jini wadda ake cewa cutar sicler...Masana sun raba genotype zuwa kaso uku da suke cewa: homozygous dominant, homozygous recessive, da kuma hetrozygous. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, wanda daga gwajin ake samun Genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda 3 kamar haka,  AA, AS, SS...AA su ne masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa Carrier, akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukunsu ne SS masu ɗauke da amosanin jini wato Sicler saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura...Abu mai muhimmancin da ya kamata a lura kafin aure idan an duba genotype ɗin su ne kamar haka: Rukunin farko wato na mijin, Na biyun kuma na matar, sakamakon kuwa irin ƴaƴan da za'a samu su ne: (1). AA +AA = AA, AA, AA, AA, za'a samar da ƴaƴa masu cikakkiyar lafiya. (2). AA + AS = AA, AS, AA, AS, shi ma aure ne mai kyau kuma babu matsala a lafiyar ƴaƴan da za'a haifa amma bai kai na AA+AA ba. (3). AA + SS = AS, AS, AS, AS, shi ma wannan auren ana iya yinsa duk da akwai ƴar matsala kaɗan akan ƴaƴan da za'a haifa zasu zama AS ne duka ma'ana carriers. (4). AS + AS = AA, AS, AS, SS, akwai matsala domin za'a samu ɗa ko ƴa mai cutar sikila. (5). AS + SS = AS, SS, SS, SS, a wannan gaɓar akwai matsala sose domin kusan kaso 80 na ƴaƴa zasu zama masu cutar sicler ne. (6). SS + SS = SS, SS, SS, SS, inda matsala mai muni ta ke, domin dukkan ƴaƴan da iyayen sicler ne, zasu ƙare ne cikin tsanani da wahala na rashin lafiya...Idan aka lura da waɗannan matakan duka, ba shakka za'a kawo raguwa ko ƙarshen cutar amosanin jini wato sicler da ta ke galabaitar da waɗanda suke ɗauke da ita, kuma ta wannan hanyar kaɗai ake iya maganceta kamar yanda ta nan ta ke samuwa.  Allah ƙara mana lafiya ya kuma bawa marasa lafiyanmu lafiya"._
gama bayanin matar yay daidai da shigowar kira cikin wayata, nayi saurin ɗauka hannuna na rawa bisa rashin sanin dalilin hakan ganin cewar Bro Almustapha ke kirana. na kara wayar a kunnena ina jin wani irin faɗuwar gaba matsananciya, na rumtse idanuwana na kasa yin sallamar da ta kamaceni nayi.
"Littile". ban amsa kiran sunan nasa ba sai da na haɗiye wani abu ta maƙoshina da ya wuce da ƙyar sannan nace. "na'am Bross". "kina jina ba, ki buɗe wannan box ɗin da na baki ranar dana zo, akwai wani blue envelop da sunan asibitin da muka je da ke, ki ɓare shi ki duba min menene genotype ɗinki, gaba ɗaya na manta ban duba ba a ranar, kiyi da sauri". na miƙe ƙafafuna na rakani da ƙyar har zuwa bakin dressing mirrow, na tsuguna na buɗe drower na ɗauko box ɗin da ya bani ajiya ranar da zai wuce london, na buɗe kamar yanda yace na shiga karanto masa cewar, "Bross AA ne". sai yace da ni,"oak". kamin ya katse nayi saurin cewa da shi,"Bross ka tambayi Ya Ahmad nasa, ina kiran wayansa ban samu ba kuma Dad yace na kira shi nace yana jiran result ɗinsa". da alama daga inda yake lemu ya kurɓa kamin ya ban amsa da cewan,"no ai nasan ma yana wajena tun wancan ranar da Mami tace na amso". cike da fargaba nace,"Bross shi mene nasa?". nayi tambayar da rawar murya. "result ɗinku is the same, shi ma AA ne". kan na ƙara cewa wani abu ya katse kiran. katse kiran da ya sa na jefar da wayata na faɗa kan gado ina kanƙame pillow dan murna.
zuciyata faɗa min take a yanzu ba wata fargaba, babu wani ƙalubale, babu wata damuwa, komai ya kau, aurenmu zai tabbata, Maryam da Ahmad za su tabbata ma'aurata, Maryam da Ahmad zasu kasance a matsayin abu guda, wannan tazarar da ke tsakaninmu zata haɗe a wani dare ta tabbatar damu matsayin mata da miji.

*Vote,Comment and Share plss🙏.*

SIRRIN ƁOYE CompleteOù les histoires vivent. Découvrez maintenant