12

180 24 5
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maki hajarki cikin farashi mai rahusa, ke dai tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._

*12)*
Mun ɗauki tsawon lokaci rungume da junanmu, tun shashsheƙar kukan Kulu na fita har ta daina, ni kuma a nutsuwar dana samu daga wannan jikin nata ne bacci ya soma ɗaukana, sai can kamar kuma tsikarin allura naji ta tureni daga jikinta har ƙeyata ta bugi da bango, ta kauda fuska gefe saboda kar ta haɗa ido dani, lallai acikin ɗabi'un Gwaggona dana Kulu akaina zan iya cewa babu banbanci, dan ko a ɓangaren Gwaggona sau tari ta kan kauda kai daga gareni musamman lokacin da ta san ina buƙatar kulawarta tamkar ba ita ta tsuguna ta haifeni ba, ni kuma hakan na damuna, yana min ciwo, yana kuma sani zubar hawaye, domin banda shaƙuwa irin ta uwa da ƴa da har Gwaggona zata iya jin sirrina, ko kuma na faɗa mata matsalata, Duk sanda na kaiwa Inna Amarya wannan kukan nawa sai tace nayi haƙuri kunya ce tsakanin Ɗan fari, sai dai ni kuma na ɗauki hakan a matsayin cutarwa, dan tabbas ina cutuwa matuƙa, ita Kulu nasan ba dan komai yasa take yakice ni daga jikinta ba sai dan iyaka da Gwaggo tayi mata da ƴaƴanta, amma banda haka tabbas zan iya cewa Kulu zata iya zame min Uwa kamar Inna Amarya.
Ganin yanda na tsareta da idanu yasa ta tashi ta bar min wajen, ta koma gun shimfiɗarta ta kwanta. Nima na tashi na fita dan ɗauro alwala, sai dai me kuma!, ina fita tsakar gida naja na tsaya saboda abunda idanuna suka yi tozali da shi, tsoro ya kamani, jikina ya hau kyarma, nayi dakiyar dana hana kaina gaggawar kurma ihu, na shiga jero adu'oin neman tsari da halittar dana gani a tsaye daga can wurin banɗaki ta juyan baya, hannu a kunne da alama waya ake, dan ina iya jiyo sautin fitar murya ƙasa-ƙasa amma bana jin me ake cewa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da ƙaton zane, hakan yasa ba zaka tantance mace bace ko namiji, kuma a duk iyaka ƙoƙarina na son in gano zanin wane acikin gidan na kasa saboda na manta a ɗakin wa na taɓa ganinsa, sanin zanin waye ba shi ya dameni ba, waye a tsayen shi na damu da na sani, na dai baro su Gwaggona a ɗaki, ƙofar ɗakin Inna Amarya kuma a rufe yake, Inna Zulai kuwa nasan ko karan hauka ne ya cijeta ba zata fito da wannan tsakiyar daren ba, na tabbatarwa da kaina hakan akanta, saboda ita tana da tsoro sosai, ko fitsarin dare bata fitowa sai dai ta tsula abunta a fo wanda ta siya saboda tashin dare, to kar da ace ɓarawo ne ya shigo mana gida?, Na daddage na buɗe bakina na kurma ihun "Ɓarawo". da siririyar muryar da Allah ya bani, har sai da nayi ihun sau biyu tukunna Baba ya buɗe ƙofa ya fito, sai gasu Ya Amadu da Ya Kabiru ma a tare, kowa kuma ya shiga jefo min tambayar ina ɓarawon yake?, ashe tuni ma ya bar wajen, murya na rawa nace da Baba, "a wajen banɗaki na ganshi". Aiko nan mazan gidanmu suka yi wajen, wasu kuma suka fita ƙofar gida ko zasu tarfa shi ta bayan katanga. "ikon Allah, amma me ɓarawo zai shigo yi cikin gidan nan mu da bamu aje komai ba?". Baba yay maganar da Matansa da ke tsatstsaye kowacce acikin taraddadi, Inna Zulai tace, "shi ne abun tambayar ai...kuma ke Mairo kin tabbatar mutum kika gani kuwa ba a ƴan barci kike ba?". "ehh wallahi Innah, ai banma yi ihun ba sai dana tabbatar shi ne ɗin". Baba ya kuma girgiza kai, "Ɓarawo acikin gidan nan, ikon Allah!". Gwaggona ta sauke numfashi bata ce komai ba sai wajen banɗaki da ta ƙurawa ido, dan ita macece irina me yin nazari da zurfin tunani akan abun da ya bata mamaki. "ni nama kasa cewa komai". Inna Amarya ta faɗa wadda ke tsaye daga ƙofar ɗakinta. Na kuma cewa, "Baba kuma fa waya yake yi lokacin dana gansa". Kan kowa yace wani abun sai ga su Ya Kabiru sun shigo kowa na maida numfashi. "Baba babu fa kowa a wajen nan wallahi, babu ma alamar an dira ta baya gaskiya, dan Malam Yakubu da Ƴaƴansa har kan kwana suka bi". Ya Kabiru ke wannan bayanin, Mu'azzam ya ɗora da cewar,"nan ciki ma fa babu wata alama tasa, saboda ko yane da za'a ga alama ta neman wajen ɓuyarsa ko kuma fita". Kowa yay shiru wucewar sakanni kamin Baba yace, "to Allah ya tsare...kowa ya koma yaje ya kwanta". Sadiya da ke tsaye kusa da Inna Amarya tace, "yanda Mairo ke da hargitsewa wallahi ma nasan bai zama lallai ɓarawo ta gani ba, magagin barcinta ne kawai".
"ai da ban gani ba babu yadda za'ai nayi ihu a wannan daren". Daga haka kuma kowa ya juya ya wuce ɗakinsa, tunda muka shiga ɗaki ni dai na kasa bacci saboda tsoro, nayi lamo kwance ƙirjina sai bugawa yake, kuma dana rufe ido sai hoton wancan mutumin yake haskawa cikin idona, hakan yasa na gagara rufe shi na bar shi a buɗe, kuma ko a duhunma hakan take, nayi yunƙurin kunna haske saina tuna Gwaggo bata iya bacci da haske hakan yasa na koma na ƙudundune.
Can naji motsin an buɗe ƙofa an fita, nayi zumbur kuwa na miƙe nabi bayan Kulu da ta fice, ban sanya ƙafata a tsakar gidan ba sai da na tabbatar da ta shige ɗakin Baba, na tafi saɗaf saɗaf na ɓoye a inda ko fitowa akai ba za'a iya ganin ko da inuwata ba. Na jiyo muryar Baba na fita da cewar, "da ina da ikon tsaida hawaye, da na jima da tsaida zubar hawayenki Kulu". Banji me tace masa ba, haka kuma shi ma banji abunda yace mata ba, na kuma rumtse ido tare da ƙara kasa kunne sosai dan kar wata maganar ta kuma wuce kunnena, domin a yau dai na tabbatar da akwai wani sirrin ɓoye da ke tsakanin Kulu da mahaifana.
Sautin muryar Baba ya ɗan ɗaga yaci gaba da cewa da Kulu, "Kulu ina so ki gane rayuwa kowa da irin tasa. kamar yanda labarin rayuwar kowanne bawa dabanne, To haka kowacce rayuwa na cike ne da tarin ƙaddarori masu yawan gaske, haka ma kowacce ƙaddara da fuskar da take zuwarma mutum, kuma kowanne bawa da kika gani yana taka sawu ne akan ƙaddararsa kuma duk inda ta nufa da kai dole sai ka bita baka isa ka guje mata ba domin rubutacciya ce, amma karɓarta ta kowacce irin fuska shi ke nuna ƙarfin imanin mutum. Kuma kowanne bawa da kalar irin tasa ƙaddarar, wani zai tsinceta da kyau wani kuma zata zo masa da muni kuma dole ya karɓa in har ya yarda yayi imanin da Mahallicinsa, Allah ya kan jarabci bawansa ne domin gwada ƙarfin imaninsa ya gani shin zai iya cinye jarabawar, idan har kuma yayi riƙo da wannan ƙaddarar to zaki kalla ko akan wanne Al'amari ne ƙarshensa yazo masa ta yanda bai yi tsammani ba. Saboda haka ki sani Allah da kansa yana faɗa a Alqur'ani cewa "Ahsiban-nasu an yutraku an ya quluu amanna wahum la yuftanun". Mutane su na tsammanin zamu bar su barkatai alhalin sun ce haƙiƙa mu munyi imani?. To kinga kenan tabbas mumini ake jarrabawa, wannan kuma jarrabawar taki ce, ki roƙi ubangiji ya baki ikon cinyeta ba wai ki zama ko da yaushe cikin kuka ba, wannan kukan babu abunda zai yi miki. Suwaiba ta faɗa miki abunda kike tunanin faruwarsa anan gaba muddin tana raye ba zata bari hakan ta faru ba, nima kuma nayi miki wannan alƙawarin, matuƙar ina raye babu mai sanin wannan sirrin naki, na ɗauke ki ne tamkar ƴar cikina...Suwaiba kuma ta ɗaukeki ne matsayin ƴar'uwar da kuka fito ciki guda, Ko wani ya nemi ya tozartaki wallahi sai inda ƙarfin Suwaiba ya ƙare, ba zata bari ba ko da ace hakan zai zama silar rayuwarta ne".
Wucewar sakanni kamin na jiyo muryar Kulu na cewa, "Malam gani nake kaman ƙaddarar zata iya juyawa, ina tunawa da maganar Kakata da take cewa Barewa bata gudu ɗanta yayi rarrafe...haka kuma mahaifina ya taɓa ce mana abunda iyaye suka aikata a ƙuruciyarsu to shi ƴaƴansu suke aikatawa idan sun taso...Malam kayi haƙuri, waɗannan kalamai biyun da nake tunawa su ne suke sakani zubar hawaye su kuma ɗaga hankalina sannan zuciyata ta ƙara yin rauni, ayanzu haka ina mai dana sanin sunan dana raɗa mata, ina gudun karta tashi akan turbar me wannan sunan, Dama ace sunana na raɗa mata da ba zan kasance a fargabar rayuwarta ba a duk inda zata tsinci kanta kuwa, sai dai kuma idan itama ta gamu da irin tawa ƙaddarar". Kukan da ya ci ƙarfinta yasa ta yin shiru, kamin taci gaba da cewa, "wallahi ina jin tamkar na kashe kawunanmu ko dan saboda na huta da ɗanɗanar wannan baƙin cikin rayuwar da nake yi, itama kuma ta huta da fuskantar baƙin ciki anan gaba". Kuka yaci ƙarfinta sosai tana kuma cewa, "gwara ita na kanji tana bina da kyakykyawar adu'a wani lokacin, amma ɗan'uwanta fa?, Allah ɗaya yasan acikin rayuwar da ya ke ciki yanzu, Allah kuma kaɗai yasan irin kalaman da yake jifana da su a kowacce rana ta rayuwarsa, hakkinsa kaɗai ba zai barni samun natsuwa da kwanciyar hankali ba, ita kanta ina shakkar ta san sirrin komai anan gaba domin zuciyarta irinta Kakarta ce, ba zatayi min da sauƙi ba muddin tasan Sirrin Ɓoye...Malam na roƙeka kai da Yaya ku taimaka min da maganin da zamu sha mu mutu, wallahi ba kaina nake tausayi ba, rayuwarta na ke tausayawa...ku bar batun zan koma wajen iyayena domin kuwa zuwa yanzu sun manta da rayuwata...amma ga wannan takardar tana ɗauke da adireshin gidanmu, Bayan raina na aminta akan kuje, idan kunje kun sami mahaifina a raye kuce ina neman gafararsu, ku sanar musu ni da Hussaina mun bar duniyar, amma Hassan yana raye, ina roƙon alfarmar su neme shi su mallaka masa abunda na mallaka gudun kar ya tagayyara a rayuwarsa, idan kuma ya buƙaci mahaifinsa su bashi hoton da yake cikin wannan saƙon yaje yayi yaƙin nemansa"...
Shirunta yayi dai-dai da sandarewar ƙafafuna, shin ta wacce fuska zan fassara Al'amarin Kulu ne wanda yake da matuƙar ɗaure kai?, menene ya faru acikin rayuwarta, jiyo takun motsin fitowa nai saurin barin wajen na koma ɗaki, kuma har ɓarawon bacci ya ɗaukeni Kulu bata dawo ɗakin ba, sai a washe gari dana farka sakamakon hasken rana da ya dallare min idanu wanda ya shigo ta ƙofar taga, nayi zumbur na miƙe na sauka daga gado tunawa da nayi da banyi sallah ba.

*Comment&Share.*

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now