27

193 24 10
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._

*27)*
"me muka zo yi anan?". Abdurrahim ya tambaya a san da ya waigo ba ya yana duban Kabir, yaji tambayar tasa amma sai dai bai amsa masa ba, dan ya tattara hankalinsa gaba ɗaya zuwa ga fuskar masarautar da ke fuskantarsu, ba komai yake kallo ba illa hoton da ke ajikin ƙatuwar fastar da aka manna daga wajen ginin.
ya san akwai identical twins, amma shi tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin twins ɗin da su kai tsananin kama da juna ba irinsu, kai ko a labari ma bai taɓa ji ba, duk kamannin da suke da su dole akwai ta hanyar da ake gane su, amma su waɗannan kamanninsu ya zarce tunanin mutum ko hasashensa, idan har ba sa ni kayi ba to zaka rantse da Allah mutum ɗaya ne shege editing ya maida shi biyu.
gaba ɗaya ya rasa wacce a ciki zai nuna ya kirata da sunan Kulu, to ko dan ba'a kusa da hoton yake sosai bane yake ganin hakan?. ya ɗauke kallonsa daga barin kallon hoton fastar ya dawo da kallonsa ga hoton Kulu da ke cikin wayarsa, ya jijjiga kai yana mai ƙara jinjinawa sarautar ubangiji, a sannan kuma hoton Mairo ya haska a cikin idonsa, lallai ne maganar hausawa da suka ce sai kasa aka sannan kake ɗauka, in ba haka ba ai akwai tsananin kama a tsakanin Mairo da Kulu, ana sakata a tsakiyar hoton nan zasu tashi a sahun identical twins su koma identical triplet, banbancinta da su ɗan kaɗan ne fuskarta tafi tasu siranta sun kuma fita hasken fata, amma daga wannan ba zai iya kawo wani abu da zai ce ya banbanta kamanninsu ba.
kunna datar wayarsa yayi ya shiga goggle inda ya tafi kan map yana duban ta yanda zai tsarawa shiga gidan ba tare da tambaye tambaye ba har ya isa ga inda Kulu ke so ya isa, wato turakar mahaifiyarta. yana shafa wayar yana dariya ƙasa ƙasa saboda mitar da Abdurrahim keta zabgawa, shirun da yay masa kuma na ƙara hasala shi har da buɗe motar ma ya fice ya tsaya daga waje, Abdurrahim ɗin faɗi yake,"Kabir inda nasan da wannan walaƙancin naka wallahi da ban biyoka ba, kazo ka shanyamu a waje kamar waɗanda aka sassaƙa, ana tambayarka kuma ka share mutane saboda rashin mutunci". bakinsa kuma ya ɗauke da maganar lokacin da idanunsa suka kai masa kan fastar hoton kyawawan ƴan matan su biyu, kana ganinsu kaga larabawan asali, ga shigar da suka yi ta abaya ta ɗaukesu.
ya murza hannayensa yana me leƙo da kai ta glass yay knocking Kabir ya zuge,"Kabir kaga wasu zuƙa-zuƙan ƴan mata anan, la'ila ha'illallahu ka fito malami ka gani mu san yanda za ai". Kabir na jinsa yay masa banza bai tanka shi ba, shi kuma bai fasa surutan da yake ba, har tambayar me taxi ɗin da ya ɗaukosu yake wai ya bashi shawarar da zai shigar da kansa cikin masarautar ko kuma inda zai sami numbar ɗaya daga cikinsu, shi ma Babansa na da kuɗi dan haka Al'amarin aurensu ba zai yi wuya ba, Me taxi ɗin dai murmusawa kawai yay.
Kabir da ya jishi yay tsaki da cewar,"ashe dai bani kaɗai ne mahaukacin ba". "Malam ban sa da kai ba, kai sabgarka nayi tawa". Kabir ya ƙyalƙyale da dariyar da ta ƙular da shi ya ƙara hawa sama da mitarsa.
_"yallaɓai akwai tsaro sosai a wannan masarautar, in dai ba kana da alaƙa da ita ba to ƙofar wajen ma baka zuwa dan hakan zai iya jefa aka a haɗari...yanzu ma ko da munje daga tsallaken titi zamu tsaya saboda ba'a parking a wajejen"._
maganar mai taxi ɗin da ya ɗaukosu daga airpot ta haska masa acikin ka, ehh tabbas kamar yanda ya faɗa akwai tsaro me tsauri ma kuwa...ba ya jin akwai ta yanda zai yi ya sami shiga cikinta, saboda haka zai haƙura ne kawai ya koma, tunda in har ba shiga ɗin yay ba, ba zai sami abinda yazo nema ba, kuma idanma zai sami bayanin da ya ke so ɗin daga wajen wani to dole sai wanda yake mazaunin cikin masarautar ne.
ya buɗe murfin motar ya fito ya jingina da jikin motar, hannayensa harɗe a ƙirjinsa yake kallon masarautar da tunaninka mabanbanta acikin kansa. fitowar wata farar mota ƙirar BMW daga cikin masarautar ya ɗauki hankalinsa, bin motar yake da ido har san da ta hau kan titi idonsa ya sauka akan lambar motar da ke ɗauke da rubutun sunan *Al-Hassan Bin Samin Al-Thalis* da manyan baƙi, ta ke anan maganar Kulu ta gifta a cikin kansa. _"ina ji ajikina Al-Hassan yana tare da ahalina, duk da cewar mahaifinsa ya ƙwace shi daga hannuna, amma na san ba zai iya ɗaukar nauyin riƙe shi ba, so dole ne ma cikin biyun ɗaya, ko ya salwantar da rayuwarsa ko kuma idan da sauran wannan ɗison imanin da na fara saninsa da shi a zuciyarsa to zai miƙa shi gidanmu, zuciyata na cikin zullumin son sanin a wane irin hali Al-Hassan ke ciki, wallahi bana iya bacci saboda tunaninsa, ka taimaka min Kabir"._ bai san ata yanda zai kwatanta yanda yaji ba da ganin wannan motar, suna kawai ya gani ba shi da tabbacin wanda ke cikin motar, dan haka dole ma yay binciken wanda ya wuce acikin motar.
"Driver kabi min bayan waccen motar". abin da yace da me taxi kenan, suka shigo ciki shi da Abdurrahim. Driver faɗi yake,"Yallaɓai ina fatan dai silar hakan ba zai sa na shiga wata matsala ba, domin na lura kai ɗin kamar ma'aikaciɓ bincike ne". "kar ka damu babu wata matsala da zata gifta, ni ɗin ba ma'aikaci ba ne akwai abin da na ke nema dai...ka ƙara speed dan Allah kar su ɓace mana". me motar ya ƙara gudu yana bin bayan motar da irin dabarar da ba za'a gane bin ta yake ba.
motar bata tsaya ba sai a wani ƙaton building da ke ɗauke da rubutun Qatar Charity. su kuma tasu motar ta tsaya daga baya, Kabir ya rufe ido yana roƙon Allah akan Allah yasa kar motar tasu ta shiga cikin gidan marayun ba tare da ya ga Al-Hassan ɗin da zuciyarsa ke zullumi ba, ga shi shi ba irin shigar da zata nuna shi ɗin me tsananin buƙatar taimako bane balle yayi amfani da damar hakan a dabarar da ke cikin kansa, yasa yatsunsa cikin sumar kansa ya yamutsa gashinsa yana cije leɓensa na ƙasa. kamar ance buɗe idonka, yana buɗewa yaga motar na bakin gate bata kai ga shiga ciki ba, sai kuma biyu daga cikin security ɗin da ke tsaron wajen su ka zo suka buɗe murfin motar na ɓarin dama da hagun.
Kabir ya buɗe motar ya fito ya tsaya daga gefe kamar wanda hankalinsa ba'a wurinsu yake ba, ta gefen idonsa yake kallon matar da ta fito daga cikin motar sanye da baƙar abaya, fara ƙal da ita wadda zai iya kira da potocopy ɗin Mairo ta yanda take takun tafiyarta, fuskarta cike da annuri idanunta kuma na ɗauke da gilashin da zai baka tabbacin medical ne. yes! ba shi da haufin cewa wannan ita ce mahaifiyar su Kulu dan ga kamanni nan sun bayyana, ya leƙa cikin motar yana tambayar me taxi, "dan Allah wace ita ɗin?". ya ba shi amsa da,"Yallaɓai wannan ita ce Sarauniya Asma matar Mai Martaba". maida dubansa gareta da zai yi sai yaga wani ɗan saurayi tsaye a kusa da ita tana mishi bayani yana kaɗa kai alamar yana sauraronta, shi ma fari ne ƙal kyakykyawa, dogo, siriri, gefen idonsa akwai abar da ake kira da tusar jaki, akwai kama ta jini sosai a tsakaninsu, bai yi tambayar da zai sake yiwa me taxi ɗin ba ya sami amsarta daga Umm da sautin muryartata ya sauka a kunnensa tana faɗin,"Al-Hassan". ta kira sunan ɗan saurayin da ya juya zai shiga cikin gidan marayun. anan Kabir ya sami damar ƙare masa kallo, sam basa ma kama da Kulu bama zaka ce ɗanta bane indai ba ka lura da kama ta jini ba, kawai dai a surar jikinsa ne suka yi yanayi da Mairo da idan ka gansu tare zaka iya cewa Yaya da Ƙanwa ne.
yay wani sanyayyan murmushi na nuna jin daɗi, sannan ya lalubo wayarsa daga aljihu ya danna kiran lambar Kulu amma sai dai yana ta kiran bata shiga ba, sai can kuma ta shiga a bugun farko kuwa muryarta ta shiga kunnensa.
"Salamu Alaikum Kabir".
sai ya lumshe idonsa ya jingina daga jikin motar, ƙarshen aikinsa yazo, haka kuma ƙarshen komai yazo.
ya amsa sallamartata,"wa alaiki salamu da Aaliyah, barkanki da wannan lokaci". bata yi mamaki ba domin tasan dole ayanzu zai san asalin sunanta in har yay binciken da tasa shi, saboda haka ta amsa masa da,"wane tarihi ka samu ga me da wannan sunan?". har yanzu wannan murmushin na jin daɗi bai bar fuskarsa ba yace,"duk wani bayani ki bari ba yanzu ba sai zuwa anjima...yanzu dai babban albishir zan miki".
cike da zumuɗi me ɗauke da fargaba tace, "Allah yasa albishir ɗin da zai yaye min wani kaso na cikin damuwata ne, ina sauraronka ɗan halak". Ya shafi goshinsa yana cewa,"gani a kusa da Umm da Al-Hassan". sunayen da ya ambata suka daki zuciyarta bugunta ya sauya,"Kabir ka san waɗannan sunayen a bakina, saboda haka karka yi wasa da ni dan wanzar min da farincikin da ba zai ɗore ba". "wallahi da gaske nake miki, tsakanina da Al-Hassan ma bamu da tazara, gashi nan ya girma ya zama saurayi kamar yanda Maryam ɗita ta zama budurwa". a ɗan shiru da ta yi zai iya rantsewa hawayen farin ciki take, kuma bakinta yaƙi rufuwa saboda farincikin da ya lulluɓeta, ya katse wannan shirun nata da tambayar,"amma ko kusa ko alama babu kamanninki a tare da shi, banda kamanni ta jini da kuma kasancewarsa tare da Umm da zan rantse nace ba shi ne Al-Hassan ɗinki ba". ta bashi a amsa da,"ai shi kamar mahaifinsa yayi tun a ranar farko da ya zo duniya...Kabir ina so na dawo cikin ahalina sai dai ban san ya zanyi ba, ubansu ya zama silar tarwatsewar duk wani farinciki nawa". ya sauke numfashi yana faɗin,"karki damu in Allah yarda komai zai warware acikin sauƙi".
ta amsa da,"Allah ya yarda". sannan ta kuma ce masa,"to baka sami labarin Hussainar ba?". yace da ita, "yanzu tunda na gama da nan da zarar na sauka a Ethiopia wurinta zan fara sauka, ita ma zan gano miki ita da lafiyarta, karki damu". ta sauke numfashi sannan tace,"to baka ce min komai ga me da Abi ba". "nace miki sai na tattara dukkan bayanan komai sannan zan sanar miki, nan Qatar dai na gama da ita, Hussainarki ce kawai tayi saura acan ethiopian ma". kamar tana gabansa a lokacin ta gyaɗa masa kai,"to shikenan na gode Kabir". ta tari numfashinsa akan maganar da zai yi da faɗin,"ina ɗaga wayarka kenan Malam ya aiki su Hussaina, sai dai idan ta dawo zuwa anjima zan kiraka".a sannan wani annuri na fuskarsa ya ƙaru yace da ita,"tom sai na jiki...amma nan da 3hours dai ina jirgi". daga haka kuma suka yi sallama.
ya koma mota drivern yaja su zuwa airport, a duniyar tunaninsa ta yau gaba ɗaya cike take da tausayin Kulu, in banda ƙaddara me tsanani me zai baro Kulu daga cikin daularsu ta koma rayuwar ɗan akurkin gidansu.

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now