38

206 24 5
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._

*(38)*
"me yasa ba kya so ya mutu?".
"saboda ina sonsa, dan Allah Mami karya mutu". na faɗa ba tare da sanin ma'anar da furucin nawa zai haifar ba, ina ƙara ƙanƙameta kamar zan karya ƙasusuwan jikinta, sai naji tayi wani murmushi da sautinsa kawai na iya ji, sannan tace da ni,"akwai wasu kalmomin dake bada tarin ma'anoni da yawa...Maryam a shekarunki goma sha bakwai nasan kin san ma'anar So, haka kuma kin san rabeben So...ina so ki faɗa min wanne irin so kikewa Kabir bayan na ƴan'uwan taka?...ba daga fatar bakinki nake son jin amsar ba, ki ba ni ita daga ƙasan zuciyarki".
sai naji na tsaya cak daga motsi na wucewar wasu sakanni, yawun bakina kuma ya ƙafe, abinda Mami ta faɗa daga ƙarshe shi ƙwaƙwalwata ke ƙara biya min, "bayan so na ƴan'uwan taka, wane irin so kikewa Kabir?."_, tabbas tambayar na ɗauke da ma'anar da nake ganin kamar taiwa kaina girma.
to ma wacce amsa zan bawa Mami a yanzu bayan wacce nake da ita ta riga ta faɗeta acikin tambayar da zata min, bayan so na ƴan'uwantaka dama akwai wani so ne da nakewa Ya Kabir wanda ban san da shi ba?, so ɗaya na san ina masa soyayyar Yaya da Ƙanwarsa, irin so na amatu ɗin da zan iya shiga wani hali in har mutuwa ta rabani da shi.
"ehen...". maganar Mami acikin shirun da nai tasa kayan cikina hautsinawa, sai dai a lokacin da zan buɗi baki nai magana a lokacin na godewa Allah da kuma Ya Amadu da maganarsa ta katse zancen na mu.
"Mami likita na magana". "oak Ahmad jeka mana". "no yace ke yake son gani".
Mami ta jayeni daga jikinta sannan ta miƙe ta fita, ni kuma na zauna kan kujerar da ta tashi na tsurawa Ya Kabiru ido wanda motsinsa kawai nake so na gani ko na sami ƴar natsuwa a tare da ruhina. "goge fuskarki". Ya Amadu yace da ni a sanda ya ƙaraso wurin yana tsaye daga gefen gadon, hannunsa kuma daya miƙo min handkerchif ɗinsa ne, na miƙa hannu na amsa sai naji shi da damshin ruwa, na ɗago idona na dube shi naga ya kafeni da ido da irin kallon da ban taɓa ganin ya min shi ba a ƙwayar idonsa.
kallon daya haifar da jin wani abu ajikina, ba shiri na haɗiye guntun yawun dake maƙogorona na haƙura da jin ba'asin dalilin daya sa zan goge fuskana, kuma ban fahimci dalilin hakan ba sai dana ɗora Handky ɗin ina goge fuskar, ashe a bushe ta ke, bushewar ruwan hawayen da nake zubarwa tun tasowarmu daga Qatar har saukarmu ƙasar nan.
"amsar guda ɗaya ce, ƙanwa! daga wannan matsayin so na ƙanwa, daga wannan matsayin karki yarda ki baiwa wani abu me tasiri damar shiga cikin kanki ya sauya tunaninki".
tabbas banda kallonsa nake a sanda yake maganar, zan rantse da Allah ba Ya Amadu ne yay maganar ba, saboda yanda bakinsa yake a gimtse, haka kuma laɓɓansa basu motsa ba, kuma yanda yay maganar kamar bada ni yake ba, dan idonsa sam ba'a kaina yake ba, yana kallon wani wuri na dabanne, sai dai saɓanin tunanin cewar hankalinsa ma ba'a kaina yake ba yasha banban a sanda na kusa zamewa daga kan kujera zan faɗi yay saurin saka ƙafarsa ya riƙe kujerar da kuma hannunsa guda wajen riƙoni.
na rufe idona sai dai kamin na buɗe har ya bar kusa da gadon, sai kawai nabi bayansa da kallo a sanda yake daf da fita daga room ɗin, da tarin wasu abubuwa fal da ban san ma'anarsu ba a cikin kaina. bayan fitarsa na kasa hana hannuna daga riƙo na Ya Kabiru da yake ta sonyi tun ɗazu, ɗumin tafin hannuna da nasa suka haɗe, na lumshe ido tare da jinginar da kaina ga gefen ƙarfen gadon, tunani nake, tunanin da ban san na mene ba, har zuwa sanda idona ya kai kan jakar Mami na ɗauko na zuge zip ɗin na zaro tab ɗinta.
da security ajiki, kuma duk abinda yazo kaina idan nasa sai taƙi buɗewa, haka na tsurawa hoton Ummi dake kan screen ɗin wayar tata ido ina kallo, tunanin saka sunana a password ɗin yazo kaina duk da banda tabbacin zata iya sakawar, dan gani nake Mami tafi son Alhassan akaina, ni kawai dai na amsa sunan ƴane a wurinta, amma banda wani matsayi a zuciyarta, amma kuma ko dana saka har sunan Alhassan ɗin bai buɗe ba, hakan kuma yasa ni mamaki, sai dai mamakin daya haska cikin ƙwayar idona da cikin kaina a yanzu yafi na lokacin dana saka sunan Alhassan yaƙi buɗewa, _Maryam._ ina rubuta sunana wayar ta buɗe, kuma da buɗewarta hoton jarirai biyu ya bayyana akan wallpeper, hoton dana tabbatar da mune time ɗin da muna jarirai, dan haka ban san lokacin da na kai hannu ina shafa hoton ba tare da haɗewar saukar murmushi a fuskata. ƙaunar Mamina, Soyayyar Mamina, Bigen mahaifiyata, wannan Mahaifiyar, Uwa, Uwata da ta ɗauki cikina tsawon wata tara tana rainonsa, ta kuma haifeni bayan mawuyaciyar naƙudar da Allah kaɗai yasan adadin azabar dake cikinta, wadda ita kaɗai ce zata ƙaunace ni, ƙauna ta haƙiƙa a duk yanda nake, da duk yanda na kasance.

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now