46

148 16 2
                                    

*SIRRIN ƁOYE*

*(46)*
*8:30am na safiya.*
"ina Nawwara?". Kabir da ke tsaye a bakin entrance na parlon Inna Zulai ya jefa tambayar ga Jamila. "Yaya ba zata wuce part ɗin Yagana ba". sai ya zare hannunsa na dama da ke zube cikin aljihun wandon suite ɗin da ke jikinsa, ya sose gemunsa a san da yake kallon sashin Yagana, ya ɗauki kusan daƙiƙa uku yana kallon sashin kaman baƙonsa, nazari da tunani yake akan ta yanda zai iya shiga part ɗin Yaganan da yake ɗinke da jama'a ƴan taron biki da suka zo, ya ratsa su ya wuce zuwa inda zai sami Nawwara ya kamo hannunta ya fito da ita, yay ɗakinsa da ita ta shirya acan sannan ya ɗauki mota ya fita da ita zuwa inda ya gama tsara zai kai ta a gyarata kaman kowa, abin da ya tsara a jiya kenan da zarar ya dawo. sai dai abinda ya hana faruwar hakan tun a jiya baccin da tayi, lokacin da ya dawo tana bacci bata tashi ba, kuma ko da ya shiga ɗakinta ya taɓa jikinta sai yaji da ɗumi da alama ma akwai zazzaɓi jikin nata, wanda ya lura da hakan tun a lokacin nan da yake waya da ita. idanuwansa sun kalleta tar kuma sun fallasa masa yanayi ne na ƙarfin hali takeyi saboda babu yanda ta iya, matsayin ƴar aiki ta ke a gidan bata da batun cewar zata huta kaman yanda ta ke so, hakanne yasa ya haɗo mata da wannan maganin saboda bacci me nauyi ya ɗauketa, ta yanda duk irin tashin da za'a yi mata ba zata san ma ana yi ba, sannan ya saukar mata duk wata tarin gajiye da ke tare da ita da ma sauran ciwukan da ke jikinta.
kuma abin da zai iya cewa shi ne tun a daren jiyan zuwa yanzu da yake tsaye anan hankalinsa da tunaninsa na kanta, yana kan son sanin a wanne hali ta ke ciki, taci abinci?, ta samu damar yin wanka?, ciwon da ke damunta ya warke?, gajiyar jikinta ta barta?, sannan kuma ya tambayeta me take so?. kwanaki da kwanaki kenan yana jin wani abu na wucewa har zuciyarsa akan yarinyar, ya rasa menene shi, abun da kawai ya sani yana so ya zamana yana kasancewa tare da ita, yana so ta sake da shi ta dinƙa faɗa masa wannan ɓoyayyun sirrikan damuwar da ya lura tana tare da ita tun farkon zuwanta gidan, ya sani ba zai magance mata komai ba, amma zai yi duk mai wuyar da zai yi dan ganin ya rabata da damuwar da mutum zai ke iya tsinta a tare da itan.
sai kawai ya kulle idonsa ya buɗe tare da fuzgar da iska daga bakinsa, shi kansa ya san ya sauya 100%, ba ya da walwala a yanzu, ba ya da sukuni, ba ya iya sakewa da mutane, yanayin fara'arsa ta sauya, kullum zuciyarsa matsewa take, forsure yasan ya canja daga Kabir ɗin shekarun baya da yawa, kuma kullum ƙaryata zuciyarsa da Abdulrrahim ya ke akan cewar Soyayya ce ta maida shi hakan, shi ai ba ragon namiji bane, dan haka mace da soyayyarta basu isa su lugwigwita shi ba, basu isa su sauya shi daga Kabir ɗinsa ba, abu ɗaya ne yanzu dunƙule a zuciyarsa, kuma ya kusa kora shi ya wuce da abinda yake ganin shi ne mafitarsa, nan kusa ba sai an kai ga nisa ba, a gobe ba jibi ba. ya sani aure ya ƙunshi abubuwa guda uku; abota, aminci da yarda, sannan so da ƙauna. tabbas waɗannan su ne ginshiƙin aure, in har da su aure zai yi inganci da ƙarko, to sai dai anya ba zai yi kuskure ba akan abinda ya gama yanke tabbatuwar faruwarsa a gobe?, idan shi akwai waɗannan abubuwa ukun to ita fa?. ya sa ni baya tsoron komai goben kawai yake jira, babban fatansa shi ne Allah ya kai kowa lokacin.
ya kai hannu ya ciro wayarsa da ke ringing a aljihunsa, bai ɗaga ba sai da ta kusa tsinkewa kana ya kai kunnensa yana yin sallama. Akila ta amsa masa yanayinta babu yabo babu fallasa. "are you coming to Abuja?". "no Ummi". "but why?". "just like that". "but you will attend the dinner party ok?". bata jira cewarsa ba ta ƙara cewa,"Kabir i want to you to go to the dinner party please, don't say you will not go". to dama me ta ke tunanin zai hana shi zuwa?, zai je forsure, wata ƙila ma Dinner ɗin ta tashi ata mutane biyu, mutane ɗayan da aka shirya da mutane ɗayan da ba'a shiryawa ba.
Ya rufe murfin idonsa sannan yace da ita,"zamu zo insha'Allah Ummi". "kai da wa?". "mu biyu". Akila na miƙawa maid wasu kaya tace,"are you sure Kabir?". kaman yana gabanta ya gyaɗa ma ta kai,"ehh Ummi indai ba zai wuce nan kano ba zamu zo". Akila ta sauke numfashi daga inda ta ke kafin tace masa,"ananne mana za ai, komai ai a masarautar bichi zamu yi tarukan bikinmu".
bai ce da ita komai ba yay shiru yana sauraron bugun zuciyarsa da ke harbawa da sauri-sauri. ta katse shirun nasa da faɗin,"Kabir jikina sai yake bani kaman zaren wata ƙaddarar zai gifta kafin ɗaurin auren nan". nan ma bai ce komai ba yay shiru. ta ƙara cewa,"na kasa yardarwa kaina ba zaka mallaki Maryam ba. Kabir mai yasa ba zaka fito ka faɗawa su Baba abin da ke ranka ba?". yay wani gajeren murmushi a saman leɓensa sannan yace,"zan iya faɗa musu hakanne kaɗai idan Ahmad yace ya fasa kuma baya son Maryam. amma muddin Ahmad na sonta ba zan taɓa iya buɗewa kowa zuciyata ba yaga abin da ke dangane da Maryam ba. Ummi hatta raina zan iya sadaukar da shi akan ƙannena balle kuma wata aba soyayyar mace. dan Allah ina so ki manta da na so ƴarki, haka kuma ki daina kawo faruwar wani abu a ranki da zai hana auren nan domin ina son farin cikin ɗan'uwana, ni na cire soyayyar Maryam a raina tuni, zan kuma tabbatar miki da hakan wata ƙila a gobe".
Tayi murmushi mai sauti sannan tace,"kai ma kasan ba zan taɓa yarda da batunka na cewan ka daina son Maryam ba, duk wannan fiffizgewar da kake ƙarfin hali kawai kake, dakiya ce irin taka ta jaruman maza, amma yanayin maganarka kaɗai ya isa ya ƙaryata kalamanka, kuma kaman yanda na faɗa maka sam sam bana farin ciki da auren nan kamar yanda kai ma baka farin ciki da shi". "Ummi ya za'ai ki faɗi hakan. taya zanƙi farin ciki da auren ɗan'uwana, gaba ɗayanmu fa alkhairin auren nan muka nema, kullum cewa kike Allah ya bani ita idan har ita ce alkhairina, to tun da kika ga hakan ta kasance Allah ne zai mana sauyi mafi alkhairi tsakanin ni da ita".
yana gama maganar ɗiff yaji ta katse wayar. sai kawai ya girgiza kai, sannan ya fara tafiya sannu a hankali har ya kai ga parlon Yagana, yana shiga hayaniyar mutanen da ke zazzaune a parlon ana ta hira ta shiga kansa, ta ke yaji wani ɗan ƙaramin ciwon kai na neman kama shi, saboda haka ko tsayawa cire takalmansa bai yi ba ya gaidasu a tsaitsaye, da yake duk ƴan'uwana sai suke ta masa tsiyar ƙaninsa zai yi aure ya barshi, shi dai murmushi kawai yay bai ce musu ƙala ba, har wata Yayar Malam ƴar wan Babansu tace da shi,"Allah Kabiru kaji mun faɗa maka tazarar aurenku ba zata wuce wuta guda ba, wannan ai sai ya zama hauka, so kake ka zama tuzuru...ni shi yasa sam ban so wannan karatun nasaran ba, ga shi nan kun ɗauki aƙidarsu kuna amfani da ita, tsakani da Allah a tsarinmu mutanen ƙauye Ƴaƴanka nawa yanzu? kai ko kunya baka ji, Aminu yayi, ga Amadu zai yi amma kai wai Yagana ma ce min take ta karatunka kake bata aure ba, to naci uban bokon". kansa a ƙasa yace da ita,"za'a yi Umma, ai lokaci ne". daga faɗin haka ya wuce kai tsaye zuwa ɗakin Nawwaran, yana zuwa kuma ya tarar bata nan sai ƴan ƙunshin kayanta da jakar kayan a tsakiyar ɗakin, da alama tayi wanki ne tana haɗa kan kayan ko kuma ta fito da su dan zaɓan wanda zata saka. jin bai ji motsinta ba a ɗakin ya fito ya koma bedroom ɗin Yagana. tana ganinsa kuwa ta taso tana faɗin,"ɗan albarka ya akai?". yana kanne idanu yace,"ranki ya daɗe babu komai, ganinki kawai nazo yi". sai ta kaɗa kai kawai tana cewa,"ni kuwa kaga jiya gaba ɗaya banyi bacci me daɗi ba. ramar nan taka na bani tsoro Kabiru, duk yanda akai akwai abin da kasa a ranka yake damunka, dan Allah ka taimaka ka faɗa min, na san ban isa na rabaka da ita ba amma zan maka adu'a Allah ya yaye maka koma menene". ya wadata fuskarsa da murmushi a san da idanuwansa suka hango masa Nawwara ta fito daga toilet ɗin Yagana riƙe da wani yaro, alama kuma ta nuna masa wanka ta yiwa yaron tun da gashi nan naɗe cikin zane, ita kuma hannunta da ƙafarta duka da ruwa, ya shafa fuskar Yagana yana faɗin,"Yagana ki kwantar da hankalinki babu abinda ke damuna, idan ma akwai to komai yazo ƙarshe insha'Allah". ba hakan taso ba sai dai bata da yanda ta iya da shi, bata so ta takura masa sam. "to kaci abinci?". yasa hannu yana shafo bayan wuyansa yayinda idanuwansa ke kan ƙafar Nawwara yana bin yatsun ƙafarta da kallo, yace da Yagana. "ban ci komai ba tukunna. na ɗan fita ne sai yanzu na dawo". cikin dabara kuma sai yace da ita,"waccan yarinyar sam bata son tsafta, ana biki kowa na gyara jikinsa amma ita kalleta wani curkuɗe-curkuɗe". ya ƙarasa maganar yana haɗawa da ƙaramin tsoki.
Yagana ta waiga ta dubi Nawwaran da yake magana akai sannan ta dawo gare shi da cewan,"wallah ba laifinta bane...aiki ne ya mata yawa bata zama, kaga ɗazu ma har ta zauna za'a mata ƙunshin kuma wannan yaron sai yasa kuka, shi kuma uwar tazo ba lafiya shi yasa dole ta tashi". a lokacin ji yay kaman ya haɗa uwar yaron da yaron ya yarfa masu zagi, sannan yaywa Uwar yaron kashedin kar ta ƙara saka masa Mata rainon ɗanta tun da ba ita ta haife shi ba, kuma a cikin kuɗin aikinta babu na raino, ba kuma raino aka ɗaukota yi ba.
lokaci guda ɓacin ransa ya ƙaru yana me cewa da Yagana. "jiya ma bata je makaranta ba yauma haka. ɗazu Principal ɗin nasu ya kirani ai...tazo ta sameni a ɗaki su yi magana da shi". Yagana tace,"to Allah yasa su karɓi uzurinta, ni ban san hakan zai zama da matsala ba da ban hanata zuwa ba". shi dai juyawa kawai yay yana daɗa faɗawa Yagana,"ta taho min da kayan abincina".
Kwata-kwata Nawwara bata lura da shigowarsa ɗakin ba, sai lokacin da furucinsa na,"bata je makaranta ba". ya shiga kunnenta. A lokacin ne ta ɗago kai ta gansa, idonta ya shiga cikin nasa, kuma haka kawai ƙwayar idonta ta haska da wani irin tsoro da fargabar da bata taɓa ji ba, bata san ya dawo ba sai cikin dare da ta farka taga kwalaben madarar waken suya acikin leda har guda uku, da kuma tufa guda shida, da bunch na ayaba, kuma a wannan lokacin yunwa ce ta tasheta, dan haka ta tashi Iya dan neman izininta akan taci, tun da babu damar ta fita yanzu neman abinci, ta san ba zata samu ba dan yanzu abinci baya saura a gidan.
ko da Iyan ta tashi ta faɗa mata ai tsarabar Kabir ce da ya dawo, ta tsorata sosai da irin baccin da tayi dan tun sha biyu na rana ita ce sai 11 da rabi na dare ta farka, baccin da zata ce bata taɓa yinsa ba tun girmanta, sai dai taji daɗin yanayin jikinta sosai, wannan ciwon kan ya ɗauke gaba ɗaya, haka duk inda ke mata ciwo ajikinta ya saki, amma tayi mamakin baccin sosai. kuma murɗawar da cikinta keyi yasa ta aje mamakin a gefe ta shiga cin tufar tana korawa da madarar waken suyan, tana sha tana lumshe ido daɗinsa na ratswa har cikin kanta.
fatanta ɗaya ne a yanzu Allah yasa bai ganta ba, dan a yanda ta tsara sai lokacin dawowa daga makaranta yayi zata je ta gaishe shi, kuma jin yace ta kai masa abinci taji wani abu me kama da tsoro shi kaɗai ya dira a ƙirjinta. kallonsa take har ya ɓace daga bakin ƙofar ɗakin sannan ta ɗauke kanta da sauri ta shiga shafawa Abbas mai ajiki, jikinta sai rawa yake kamar wacce ta yiwa sarki laifi, yanayin fuskarsa take tunawa da yanayin furucinsa, da kuma kalmarsa na cewar zai yi mata exams idan ya dawo, me zai faru idan ransa ya kai ga ɓaci yace ya zare hannunsa daga ɗawainiyar makarantarta?, zata iya ɗaukan wannan ɗanyen hukuncin?, tana ganin kamar ƙwallafa ran da tayi akan karatun bokon zai iya mata illa a duk san da akace yau karatun ya datse mata?, ya zama dole ma taje ta ba shi haƙuri tun kafin zuciyarsa ta gama yanke hukunci.
dan haka da sauri ta ƙarasa shirya Abbas ta saɓe shi ta goya shi, daga yanda take nishi zaka gane goyon yaron yaywa ƙirjinta nauyi, ta fita a ɗakin cikin hanzari tana jijjiga Abbas dan yay bacci. ba ta kai ga tsakiyar parlon ba kiran sunanta da Yagana tayi ya tsayar da ƙafafunta a lokaci guda. "ga kayan abincin Kabiru can na haɗa, ki ɗauka ki kai masa ɗakinsa". "tom Yagana". sai Yagana ta bita da kallo tare da jefa mata tambayar,"lafiyarki kuwa na ganki kamar a firgice?". tayi saurin girgiza kai da cewan,"a'a babu komai Yagana". Yagana ta kaɗa kai kawai ta wuce ta barta, ita kuma ta nufi kitchen ɗin har tana tuntuɓe.
****
*76 Kafe District, Asokoro, Abuja.*
"i will definetly teach her a lesson, ni ba shashashar matan nan bace da zan bar ƙawa ta ƙulla alaƙar gaisawa da mijina ko saurayina. ni kika sani dan haka da ni za ki zumunci, so Aisha Tayo tell your that stupid friend kar ta ƙara kiran Yaya ko da sunan menene ma, in ba haka ba kuma wallah zata ga ɗanyen hauka". Shamsiyya Sani da ke daga kan gadona a kwance ta bushe da dariya tana yunƙurawa zaune.
"wallah ke dai Maryam anyi masifaffiya, wannan wanne irin kishin jaraba ne. ance miki kiransa fa kawai tayi ta tambaye shi ke saboda tana ta kiran wayarki bata samu ba, amma kinzo kin ishi mutane da bambami". naja tsaki na miƙe daga kan kujerar da nake, na kalli Shamsiyya Sani na banka mata uwar harara kafin nasa kai na fice daga bedroom ɗin, ina jinta ta rakoni da dariyar da ta ƙara ƙular da ni, idan na dawo ciki sai munyi faɗa sosai da ita, to matsalar ina son Shamsiyya.
kai tsaye ɗakin Mami na nufa sai huci na ke, su huɗu na samu a ɗakin su na arraging gift ɗin da za'a bada a wurin dinner, baka jin komai sai ƙarar acn da ke hurawa a ɗakin, da alama yanda suke magana a hankali lissafin kayan suke ba kuma sa so ya kubce masu. na nemi bakin gadon Mami na zauna ina aikin ɓata fuska kamar zan fashe. Mami ta waiwayo tana dubana tace,"Auta wa ya taɓan ke?". na ƙara kumbura fuska ina bata amsar,"ba Yaya bane". "to shi kuma Yayan da kansa yau. me ya maki hala?". tambayar tasa na fashe da kuka. Ummi tayi saurin aje kayan da ke hannunta ta iso gare ni. "ke da wa wai? sanin kanki ne bana ƙaunar kukanki". nasa hannu na goge hawayena nace,"to Ummi ki yiwa Yaya magana kar ya ƙara picking call en kowacce shegiyar ƙawata da zata kira shi. kawai yaje ya biyewa wannan banzar Mabrukan sunata waya for morethan 3mints wai da sunan kwatance yake mata. ni nace mata dole sai tazo bikin nawa ne?, ban ma san a gidan uban da ta sami lambarsa ba, dama waccan banzar Shamsiyyar ce ta jajuɓo min ita kuma Allah ita ma kiyi mata magana Ummi". "to yanzu mene abin ɗaga hankali akai. address fa kawai ta tambaye shi ba wani abu ba". sai na ƙara kumbura ina cewa,"bada address ne Ummi for more than 2minutes?, duniyar yake mata kwatance gaba ɗaya ko me?, to ni dai bana son ake jiye min muryan miji, just call him and talk to him in ba haka ba Allah ni mai iya zuwa wurin Daddy ne yanzu nace na fasa auren". Mami tayi guntun tsoki tace da Ummi,"du Allah leave this girl, go and meet Ibrahim outside naji kaman tsayawan motansa". sai na shiga shashsheƙar kuka ina faɗin,"ni nama fasa auren, dan ba zan auri me sauran maganar wata ba". Anty Samiha(cousin ɗin su Mami) ta wurgo min harara da faɗin,"kin tashi kinje kin shirya ko sai na jefo miki wannan plate ɗin...ki wuce kije ki shirya tun kafin azo tafiya kizo kina ɓatawa mutane rai, akanki Maryam ba zan ɗauki faɗan Bella ba kinji na faɗa maki". ina ƙunƙuni nace,"ita wannan Bella ta cika iko, dole ne sai anje inda ta ke sannan za ai bikin, nima ba ga gidanmu ba ta bari ayi a gidan ubana mana. mene haɗina da wani masarautar bichi, kaje ma duk wannan Jawad ɗin ya ɓata maka rai". ina rufe baki Anty Iftihal ta wawuro pillow ta jefo min, nayi saurin miƙewa ina dariya na kaucewa jifan. "ƴar ƙaniya mara kunya, Mahaifiyar tamu kike faɗawa haka saboda kin rainamu ba ki da ta ido a gabanmu". Mami tace,"to ba Kakarta bace, haka za ku yi haƙuri, ni kar a takurawa Ƴata". ina wata dariyar nace,"Allah kam wannan tsohuwan ta isheni, ko da yake kwana nawa ne ma ya rage ma ta Allah na tuba, ta tafi kowa ya huta da mulkinta". Anty Samiha tayo inda nake da plate ɗin hannunta nayi tsalle akan gadon nayi wurin Mami na ruƙunƙumeta. Mami kuma ta kareni ta hanata dukana.
Anty iftihal tace,"Maryam kici gaba, rabon kisa nayi adua ne a ɗaura aurenku ku biyu gobe". na waro ido waje ina cewa,"ni da wa?". tace,"ke da kishiyarki". na taɓe baki nace,"Anty Iftihal ba ki da labarin nayi zarra a zuciyar Yaya ne ko". kuma dan ta ƙunsa min sai ta taso da maganar ɗazu, nayi saurin tashi na bar ɗakin ina faman zumɓure zumɓure na koma ɗakina.
"ke kuma gorilla you know very well bana ƙawance, da ma ke kika naye min, ƙawata ɗaya ce Basma my sister, so dan haka daga yau na yanke ƙawancen dake, ki tarkata komatsanki ki koma gidanku, bikina ko babu ke za'a yi shi ai dama bani na gayyatoki ba, gayyar soɗi kika zo kuma manzon Allah ma ya hanata". abin da nace da Shamsiyya kenan a san da na shiga ɗakin, amma da yake Shamsiyya ƴar iska ce sai ta ci gaba da dariya ƙasa-ƙasa sannan ta sauko akan gadon tazo ta rungumeni tana bani peck a kumatu.
"easy mana my sister, mai da wuƙar kinji". na ƙara ɓata rai fiye da ɗazu dan ma tasan da gaske nake maganata, sai dai abin da ta raɗa min a kunne yasa na ƙyalƙyale da dariya na juyo ina wartar wayar hannunta nayi kan gado. muka haɗe kai muna karanta posting ɗin da ke cikin group en Matan Sirri a whatsapp, Aisha Tayo tazo zata gani muka korata da cewar ita yarinya ce da sauranta tukunna, abin na manya ne bana yara irinsu ba. hakan kuma ya ƙular da Aisha ta bar mana wurin.
wayata ce ta shiga ƙara, sanin mamallakin ringtone ɗin yasa na bar iya shegen da muke ni da Shamsiyya na mai da hankalina kan wayar, na ɗaga da zummar caccake Yaya nayi masa ruwan masifa, amma furucin farko da yay akaina yasa na sauko daga wannan saman mai nisa ta bala'in kishin da na hau, nima na shiga kwantar da murya kaman yanda tasa take, muka shiga zuba zantukan love ɗinmu ni da shi, kuma a wannan lokacin gaba ɗayanmu ji muke kaman muyi fiffike mu tashi zuwa wata sama mai nisa, mu zauna a duniyar da zamu kasance mu biyu ne kacal acikinta.

_thanks for your time and support, keep voting and commenting please, love you all😘😘._

SIRRIN ƁOYE CompleteWhere stories live. Discover now