FIFTY NINE & SIXTY

338 36 8
                                    

🌺🌺🌺🌺
*WAYE SANADI!?🪦🪦*

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO...📚✍🏽*

        *Story & Written by*
              Oum Sumayya
               #Babybintuu

*Masha Allah laa k'uwata illah billah Alhamdulillah ala kulli halin ina mik'o gaisuwa ga d'umbi masoya, na fili dana b'oye😍 azahirin gaskiya rayuwa bata yiwuwa saida masoyi sannan nasara bata yiwuwa saida k'alubale domin rayuwa babu k'alubake to babu nasara masoyan Babynintu na wattpad dana WhatsApp dana facebook ina sanar daku nan ne k'arshen WAYE SANADI!? part one saimun had'u a part two wanda zanfara sakin sa a ranar laraba idan me kowa me komai yakaimu darai da lafiya har kullun bazan gaji da sanar daku cewar WAYE SANADI!? free book ne, amma akwai GAMIN GAMBIZA danake rubutawa yanzu haka amma shi na kud'i ne idan kina so chat me 07017296839 idan kin shirya dan krmu b'ata ma juna lokaci,  Allah yabamu nasara yakare mu daga dukkanin mak'iyan mu baki d'aya🙏🏼*

      *FIFTY NINE & SIXTY*


Fuskan ta yafara taping arud'e yana fad'in "Khadija! Khadija!! Khadija!!! Meye yasame ki innalillahi wa'inna ilaihirraj'un"
Wani irin lumshe idanuwa tayi tana bud'esu tana sauke numfashi wasu hawaye suka zubo mata gaba d'aya har lokacin jikinta kyarma yake,
The rest  of Haulat kuwa kallon ikon Allah kawai takeyi tana jinjina makircin Dija ranta amugun b'ace  take kallon su,
Shiko Hamza d'agowa yayi yakalli Haulat yace "Baby meyasame ta kina kallo bazaki taimaka mata ba" yak'arisa maganar yana d'aukan Dija cak yana mata masauki akan kujera amma saita rik'e shi tana shashshekan kuka tace "karka matsa tace saita kashe ni tunda nazo mata gida da k'afana zan gudu nidai karka matsa am scared wallahi" tayi maganar afirgice dan tana tsoron Haulat tagaya mai abunda tagani,
Cikin rashin fahimta yajuyo zaiyi magana Dija tayi karaf tace "nidai Yayanah ka kyaleta nabarta da Allah duk abunda tamin basai kamata fad'a be yauma dan kagani ne da bazan gaya maka ba duka na tayi dan nace tare zamu ci abinci shine take ta dukana aciki nikuma saboda kai nayafe mata amma zanbar gidan nan gobe tunda bani da ikon zama a gidan yayanahhhhhhh" tak'arisa maganar tana wani shan majina  tana matso kwallar k'arya,
Juyowa yayi inda Haulat take tana nan kamar andasa ta tsoron Allah ne yakamata ganin sharri da makirci tsagwaro lallai duniya,  cikin takaici tabud'e baki zatai magana yad'aga mata hannu alamun baya son jidaga gareta batare daya tanka taba yad'aga waya yakira Dr yace yazo yana son ganin shi,
Dasauri Dija tatashi tace "no am owk dama dukan da tamin aciki ne sai ture ni da tayi shine na tsorata dan da bakazo ba ban san mummunan fad'uwan dazanyi ba amma basai Dr yazo ba cikin ma yadaina min zafi"
Tayi maganar tana share k'wallah kamar gaske,
Tausayin tane yakamashi murya atausashe yace "sorry sweet sis bara yazo yaduba cikin kar wani abu yasame ki dan bazan tab'a yafe ma kaina ba am sorry once again" yayi maganar yana share mata hawayen fuskarta,
Wani irin sansanyan farin ciki ne yake shiganta tana sake narkewa shikuma yalalace yana rarrashinta da rok'on alfarmar karta gayama Aunty,  aranta tace"this is my tune Haulat saikin gane shayi ruwa ne" amma afili sai tace "aiba komai yawuce ni nayafe mata wannan d'in ma" tafad'a tana lumshe idanu kamar tatashi tayi ta rawa takeji tsaban happy.

Cikin xafin zuciya da takaici takoma d'aki tanajin kamar tafashe da kuka kenan ya yarda da zancen Dija kenan "hasbunallahu wani'imal wakeem" tafad'a tana k'ok'arin daidaita zuciyar ta tagumi tazuba yanzu yazatayi kenan hawayen takaicine yazubo mata takwanta akan bed d'in tana lumshe idanun ta hawaye nabin gefen idanun ta lips d'in ta tawani taune tana k'ok'arin had'iye abunda takeji aranta tanajin shi yashigo d'akin murya acunkushe yace "Haulat"
Dasauri tabud'e idanun ta tana kallon shi dan baya kiran sunan ta saida wani babban abu saikum tatashi zaune ganin yanda yawani d'aure face kamar be tab'a dariya ba tsorone yakamata taduk'ar da kanta muryan shi ta tsinkaya yana fad'in "biyo ni" yana fad'in hakan yajuya yafuta
Jikinta yayi mugun sanyi tamik'e tabi bayan shi a dining tasame su su biyun wata iriyar harara taga yana zuba mata daya tilsta mata duk'ar dakanta zuciyar ta na mugun bugawa tak'arisa dining d'in tazauna batare data kalle suba dan kuka yake shirin b'alle mata,
Hamza ne yajanyo plate yazuba mata abinci yasa mata stew d'in data sauya kala daga ja zuwa bak'a yace "eat"
Kallon abincin tayi saikuma takalle shi tana mik'ewa murya na rawa tace "bazanci ba"
Wani kallo ya watsa mata yace "bazaki ciba? Ohhhh nice to hear than but why?"
Hawayen idanun ta tagoge da mamakin Hamza daya sauya yanzu yanzu tace "naga Khadija nazuba wani abu kuma ban yarda da abund ta zuba aciki ba"
Murmushin takaici yayi yana fad'in "Dakyau dama tafad'a min takama ki kina zuba magani acikin abinci shine tace zata gayamin kika shiga dukanta daman kullun haka kike mata kince saikin rabani da kowa  Haulat wani irin soyayya ne bana nuna miki da har saikin mallake ni kin rabani da yan uwana mena rage ki dashi? Kigaya min inji in akwai inda na rage ki dahar saikin je kin saida imanin ki bayan kin rigada kin sameni kin mallake ni amma kike wahalar dakanki why why zakimin haka Haulat nazab'e ki sama dakowa da komai meyasa zakimin hakan?"
Yak'arisa maganar cikin k'unar zuciya da takaici yawani buga table d'in har Dija dake record ta tsorata kamun yacigaba da fad'in "daga yau sai yau bana son ki k'ara yimin girki agidan nan nayafe kidafa iya wanda zakici" yana kaiwa nan yajuya yashige d'aki batare daya koda waigota ba.
Tunda yafara magana jikinta yake b'ari hawaye suna ts zirya saman kuncinta kallon Dija dake danna waya tayi tahad'iye wani mololon bak'in ciki tajuya zata wuce Dija tad'an kama hannun ta afusace ta warce tana juyowa tace "stay out with me munafuka mai bak'ar zuciya da farar fuska"
Dariya Dija tafashe dashi tace "uhm masu miji wanka kam yabi jiki yau ayi oyoyon mugani mana hahahaha Baby kinyi kyaufa amma saidai kash wanda akaimawa d'in yau ko kashi saiyafi burgesa akan kwalliyar yau saidai arungumi filo ba Baby hahahaha daga bazai sake had'a jiki da ragowan wasuba nanda lokaci k'ank'ani zan amshi zaren gidan domin dani yadace bake ballagaza sauran wasuba"
Afusace tajuyo tafalla mata mari tasake tabata ta d'ayan side d'in kafun ta wartsake tace "kinci nasara yau amma kwana d'ari da casa'in da tara ta b'arawo rana d'aya tamai kaya kirubuta ki ajiye nida Hamza mutu karaba takalmin kaza komai karfan baka da kissa da kisisinar ki dole kigani da mijina kik'yale inba hakaba bak'in ciki sai yakaiki lahira" tana kaiwa nan amaganar ta tajuya zata shige d'aki,
Azuciye Dija tayo kanta tana wani huci tashak'ota tabaya aiko Haulat tawani kama hannun ta tana juyowa takaimata naushi afuskarta take Dija tasaki wani ihu tana sakin Haulat d'in ta tab'a hancin ta saiga jini,
Cikin tsananin b'acin rai Haulat tace "kiyi me dalili jaka kawai" tana kaiwa nan amaganar ta tajuya saiga Hamza yafito daga shi sai tewol da alama wanka yakeyi dan jikin shi harda kumfa,
Tsaki Haulat taja zata wuce yawani fincikota yana zare mata idanu yace "k" yana d'aga hannun shi zai mareta
Kallon ido cikin ido tamai saikuma tashige jikin shi atsorace tana k'ok'arin kwance tewol d'in shi yarik'e hannun ta yana k'ok'arin tureta tasake rik'eshi gam tana goga fuskanta ak'irjin shi,
Gaba d'aya sai yaji tsigar jikin shi tawani mik'e idanu yalumshe ranshi amugun b'ace duk yanda yaso cireta ajikin shi tak'i domin ta firgita dukanta zaiyi d'aukan ta yayi yashiga d'akin toilet yashiga da ita murya acunkushe yace "free me"
D'an matsawa tayi tana sake b'ata rai itama ganin yajuya zai futa tasan wajen Dija zaije aiko tawani janyo tewol d'in yafad'i azuciye yajuyo gareta tasake shigewa jikin shi tana sakin wani irin kuka tana shafa kirjin shi zuwa nipple d'in shi tana goggo gashin kanta akirjin shi,
Idanu yalumshe yana furta "Haulat why why kindaki yarinya kin hanani futa mekiso danine gayamin please"
Cikin kuka da takaici tace "tom saika futa ahaka nidai ban yardaba"
Tureta yayi da k'arfi aiko tafad'a cikin jacuzzi dake cike da ruwan wankan daya fara kuka tafashe dashi cike da takaici da bakin ciki,
Futa yayi abayin yanajan tsaki short naker yadauka yasa sanan yazura jallabiya yafuta tana wajen tana kuka hanci jini na futa tana waya dasauri ya amshi wayar yana zare mata idanu muyan Aunty Saudat yaji tana fad'in...........✍🏽



*kun canza nima na canza kugyara nima nagyara more comments more typing🚶🏽‍♀️🥺*

Ayi sharing da comments aganni so soon🚶🏽‍♀️

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONEWhere stories live. Discover now