FIFTY THREE & FIFTY FOUR

263 33 14
                                    

🌺🌺🌺🌺
*WAYE SANADI!?*🪦🪦

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO📚✍🏽*

    Story & Writing by
     *Oum Sumayya*

All praise be to Allah Lord of the world,  i don't know how can i describe my happiness 😍  thank you! thank you!! thank you!!! All my fans and writer too thank you for the prayer, Baby Bintu heart you all from the bottom of my soul and my mind😍

*Not Editing➰*

*FIFTY THREE & FIFTY FOUR*

Da k'afa yatafi yana ta y'an sak'e sak'e aranshi da fatan kome zai faru yazo cikin sauk'i tafiyar mintuna goma takaishi gidan inda yasame su a palour su Ammi Aunty Saudat da Hajiya Amina suna zaune inda ya hangi Momma a dining section itada Khadija asanyaye yazauna akan rug yana kallon Ammi yace "Ammi antashi lfy ya taro"
Amaimakon ta amsa shi saita tab'e baki takauda kanta gefe tana d'aura k'afa d'aya kan d'aya tana girgiza wa fuskan ta shimfid'e da wani irin munafukin murmushi mai nuni da ba nace ba kowa ya gani!,
Murya arauna ne yamaida akalan kallon shi ga dining section yace "Momma na kintashi lafiya ya gajiyan taro?"
Murmushin takaici tayi itama bata amsa ba tace "Hamza!"
Asanyaye yace "Na'am Mommanah"
"Zo nan"
Jiki amace yak'arisa inda take yaxube akan gwiwar sa kanshi aduk'e,
"Suwaye wad'ancan?"
Ahankali yad'aga kanshi yakalli inda take pointing hannun ta kanshi yaduk'ar yace "matar uncle da Aunty Saudat"
Kai tad'an gyad'a cikin b'acin rai tace "ok menene yafaru atsakanin ka dasu dakuma marar kunyar matar ka!"
Wani irin d'agowa yy yana kallon Momma cike da tsoro dakuma tashin hankali gefen lips d'in shi yad'an cije yanajin kamar yad'aura hannu aka yy ta kuka idanun shi ya lumshe aranshi yana furta "Allahumma ajirnee fii musibat..."
Cikin masifa da hargagi yaji muryan Aunty Saudat na fad'in "watakan mune masifan ko dole kanema tsari damu ai ni wallahi ko amafarki banyi tunanin zakai min irin wannan butulcin ba amma bb komai nasan da Yaya Hamid na raye da banga hakan ba" Tak'arisa mgnr tana fashewa da wani irin kuka tana danna wayarta,
Cikin takaicin ta Momma tasake fad'in "Hamza wai bakaji tambayar danai maka bane kamin shiru?"
Ranshi amugun b'ace yakalli Momma yakauda idanun shi gefe anatse yakwashe dukkanin abunda yafaru yagaya mata sannan yad'aura da fad'in "Aunty Saudat kiyi hak'uri wallahi raina ne yab'aci sbd abunda kikayi bai kamata ba shiyasa amma ina mai sake baki hak'uri"
Tunda yafara mgn Momma take kallon su dan ba haka suka cemata ba cikin takaici tamik'e tahaye sama tabarsu,
Itako Aunty Saudat bahaka taso ba so tayi acimai mutunci dagashi har Haulat d'in amma insun san wata basu san wata ba ai,
Fuska acunkushe tace "shike nan nima ban kyauta ba kaba Haulat d'in hak'uri komai ya wuce"
Murmushi yayi yace "insha Allah zan bata nasan ma bata da ruk'o Allah yakyauta gaba"
Da amin ta amsa,
Mik'ewa yayi da niyyar haurawa sama ya tsinkayi muryan Aunty Saudat na fad'in "Hamza inada magana dakai fa!"
Azabure yajuyo hakanan yaji zuciyar shi tafara bugawa amma yadake yadawo paloun yaxauna ak'asan k'afafun ta yace "gani Aunty Saudat"
Wata uwar harara taxuba ma kanshi kafin takalli Hajiya Amina data kafe su da idanu haka Ammi ma kauda idanun ta tayi tace "Dama ina son Dija tabika can gidan ka tazauna tunda tak'i kwantar da hankalin ta tafidda miji gashi ta k'arisa karatunta saita zauna daku inbabu matsala fa?"
Tunda tafara mgn hankalin shi yayi wani mugun tashi amma Aunty Saudat ta wuce komai agaresa murya asanyaye yace "babu matsala amma kuma wani hanzari ba guduba Aunty Saudat next week zan koma Ilorin kuma tare da Haulat zamu tafi"
Fuska ta tamke tace "No babu matsala kutafi harda Dija tunda bawani abu takemin ba agidan"
D'an jim yayi alamun ranshi bai soba yace "ok ba matsala zan iya tafiya?"
Kanshi tashafa cike da farin ciki tace "eh Allah yamaka albarka"
Da amin ya amsa sannan yamik'e ya haura sama wajen Momma,
Waya yasame ta tanayi saida yayi zaman kusan ten minutes kafun ta kammala takalle shi tace "hope ba wata matsalar kuma?"
Murya sanyaye yace "ehmm"
Hankalin ta na kan wayarta bata lura da yanayin shiba tace "to saiku dage da addu'ah sannan kad'auke ta ku koma can unit d'in ka da zama dan bana son k'ananan maganganu tunda abun yafara da haka ban san ya akai ma suka san lbrn Haulat d'in ba?"
Shiru yayi kawai danshi gaba d'aya kanshi yatoshe jiyake kamar yy ta kurma ihu daga aure za'a had'a shi da wata tazauna mai agida bak'aramin takura zaiyi b..."
"Hamza!"
Mommanah Tafad'a da d'an k'arfi dan tana ta magana taji tsit,
Afirgice yakalle ta yana sosa kanshi yace "Mommanahh"
Murmushi tayi tace "bazaka daina shagwab'a ko? To kan wannan abun kardai kasama kanka damuwa dan itace ta zubar da kimar ta banga laifin kaba hakan daka mata shine daidai amma kadinga tausasa halshen ka akanta domin ta maka halacci"
Baki yad'an kauda zancen yace "Uhm wai kinji Khadii zata bini har Ilorin"
"Kamar ya ban gane ba?" Tafad'a tana kallon shi,
Cike da damuwa ya labarta mata abunda Aunty Saudat d'in tace,
Kai tajinjina tace "ai shikenan tunda ka amince mata menene nagaya min Allah yakyuata gaba"
Gaba d'aya sai yaji kamar anzare mai laka dak'yar yama Momma sallama yafito babu kowa a paloun saida yafita balcony ne yaga Aliyu da Ammi kallo d'aya yamusu yakauda kanshi har yafuta bai juyo ba amma ajikin shi yaji shi suke kallo,  tsaki yaketa ja yanzu taya zai fara sanar da BabyHazlat zaman Dija awajen shi saida yy sallar la'asar sannan yak'arisa gidan.

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora