THIRTY FIVE AND THIRTY SIX

272 20 6
                                    

🌺🌺🌺🌺
*WAYE SANADI!?*🪦🪦

*By*
*Ummu Sumayya*
*Wattpad #Bintubaby*

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITATTAFAN HAUSA TV_

http://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

_*😭🤲🏼 Kaduna muna bu'katar addu'a ku za'a yanke mana network dan haka zakujini shiru😭 Allah yahad'a fuskokin mu da alkhairi*_

*BINTU KITCHEN AND INCENSE*

*Ina kuke ma'abota son k'awata girke girke da sinadaran girki masu k'amshi da sa dad'in girki uwar gida kai harda amarya kuna ina ku masto kusa ku mallaki Bintu curry powder ingantaccen sinadarin girki mai sa girki k'amshi da dad'i curry powder mu yasamu had'i na musamman daga ingantattun kayan k'amshi masu sanya girki d'and'ano har lau Bintu curry powder basu tsaya anan ba sun kawo muku had'add'en yaji dayaji kayan k'amshi mai k'ara lafiya ajiki dakuma had'in daddawa mai sanya miya k'amshi da sa oga santi muna da kitchen ingredients kamar haka*

Curry powder
Garin citta kanin fari dan lipton
Hadd'd'en yaji mai kayan k'amshi
Had'add'en yaji mai tafarnuwa
Had'add'iyar daddawa mai kayan k'amshi
Duka akan farashi mai sau'ki muna turawa ko ina afad'in arewacin nigeria kayan ki su iso cikin salama uwargida amarya maza ku hanzarta siyan *Bintu kitchen ingredients* sai angwada akan san na kwarai! Zaku iya tuntu'bar mu akan wannan number 07017296839

*abun bai k'are haka ba akwai ingantattun turarukan mu masu sanyin k'amshi masu dad'i munada turaruruka kamar haka*

Humra
Farar humra
Ba'kar humra
Ja humra
Kulacca
Turaren wuta na kaya
Turaren wuta na jiki
Turaren wuta na tsugunno mai matse mace taciki da waje

*Kuna ina amarya uwar gida kai harda y'an mata ma don k'amshi shine mace muna saida d'aya d'aya muna bada sari akan farashi mai sau'ki uwargida amarya karku bari abaku labari zaku iya tuntu'ban mu akan wannan no 07017296839 koda kud'in ka saida rabon ka*

*THIRTY FIVE AND THIRTY SIX*

"Anema yaro yamana sallama da Maama"
D'aya daga cikin dattijan nan ne yace "A'ah Kawun nata fa?"
Kanshi yad'an dafe yace "sorry uncle Ibrahim wallahi gidan shi na baya bara naga Maama tukun saimu wuce can d'in"
Kai kawai yagyad'a yana kallon na kusa dashi suka fara magana atsakanin su,
Wani yaro sojan yakira ya aika bajimawa yadawo yace tace gata nan xuwa,
Tsayin lokaci saiga Mama tafuto sanye da atamfar anko tayi kyau abunta das lokacin datai arba da Hamza wani irin razana tayi saikuma tadake ta'karisa tana k'ak'alo murmushi tad'aura ma face d'in ta amutunce suka gaisa da Uncles d'in shi Hamza ma yad'aura da tashi gaisuwar dan har k'asa yaduk'a shiru ne yabiyo baya kamun Hamza yace "Maama dama wad'annan kawun nai nane sunxo neman min auren Haulat ne shine muka fara zuwa nan tukun ganin gaba d'aya layin acushe"
Wani irin tashin hankali Maama taji yadiran mata kamun ta lalubo abun cewa tahango Kawu yana tafe zaf zaf yana gyara malun malun gamida share zufa alokaci d'aya kallon Kawu take babu ko kiftawa har ya'karisa garesu,
Hamza dayaga tana kallon wani waje yajuya yaga Kawu yasha malun malun d'in farar shadda ga hankie a hannun shi yana ta faman share zufa,
Hannu kawun nan shi suka mi'ka mai suka gaisa amutunce kamun shima Hamza yagaisar dashi Kawu ya amsa yana kallon Maama yace "wajen ki nazo bismillah"
Jiki ba laka tabishi zauren gidan zufan fuskan shi yashare yace "Hafsatu mutanen nan sun mana rashin mutunci innalillahi wa-enna ilaihirraji'un yanzu uban d'an yazo gida yake shaida min wai d'an su yafasa auren Haulat muyi ha'kuri Allah yahad'a kowa da rabon sa"
"Hasbunallahu wa ni'emal wakeem" tafad'a tana dafa bango saka makon wani irin jiri dayake neman kwasan ta wasu zafafan hawaye ne sika zubo mata taduk'a tana fad'in "Allahu akbar Allah yasa hakane mafi alkhairi dama yanzu Hamza yazo yake shaida min sunzo da kawun nan shi neman auren ita Haulat d'in to ban kaiga cemusu komai ba sai na hango ka yanzu kafuta kakira Hamza gefe kuyi maganar fahinta dashi ad'aura auren inyaso sai asaka ranar tarewa daga baya dan nasan Hamza bazai bamu kunya ba koya ka gani?"
Wata wawiyar ajiyar zuciya Kawu yasauke yace "Alhamdulillah wani hanin ga Allah baiwa Allah yasa hakane mafi alkhairi"
Hawayen fuskarta tashare tana fad'in amin ya Allah,
Waje yafuta suka sake gaisawa da kawun nan Hamza kamun yadanja Hamza gefe yamai bayani atsanake babu musu Hamza ya amince da zancen Dad tunda dama da shirin su sukazo haka suka rankaya gidan Kawu inda kawun yama Kawu nan Hamza k'arya dan baiso suzargi wani abu yace yarinyar shi ya aurar yau tunda sunzo adaidai kawai sai ad'aura auren nata duk ahuta take sukai na'am da zancen domin dama sungaji da ganin Hamza ba mata yana yawo daga wannan jaha zuwa wannan jaha,
Babu b'ata lokaci da suka k'arisa gidan Kawu yakaisu d'akin da yake saukan ba'ki yasa aka kawo mai abinci thirty minutes yabasu suka kammala yakoma shida abokin shi da wani abokin marigayi Alhaji Aminu suka taro ad'akin bayan y'an gaishe gaishe aka gabatar da d'aurin aure kamar yanda addini yatsara akan sadaki naira dubu d'ari
Wata ajiyar zuciya Hamza yasaki aranshi yafurta *_Finally she's mine_* wani k'ayataccen murmushi yasaki yad'auko wayar shi yatsara mata text kamar haka
*_Godiya da yabo sun tabbata ga Allah mad'aukakin sarki wanda yahalicci kyakkyawan fure mai matu'kar k'amshi ha'kik'a komai rabo ne yau Haulat tazama na Hamza duk abunda mutun yayi ha'kuri akanshi tabbas zaiga haske akansa kinzama mallakina nazama naki ina fatan kinyi farin ciki dahakan sannan kigane komai nufine na Allah sabida bakya sona kika amince ma auran wani to Allah yatsara ke mallakina ne ina fatan yau kin tabbatar da zance na danace ke tawace ni takice Hazlat ha'kik'a narasa gane WAYE SANADI!? na had'uwa ta da Haulat Mommaa ko Ammi yau gashi na mallaki burin rai da zuciya na ak'arshe nagane Allah ne sa sanadin had'uwa ta da kyakkyawa acikin kyawawa kihuta Baby Hazlat naki Major general hamza Hamid_*
sander mata yayi yalumshe idanun shi yanajin yanda maro'ki ke maimaita d'aurin auren acikin speaker da sunan shi rad'au Dana Haulat abakin su,
Awaje kuwa tuni kawun nan Hamza sun bud'e bakin aljihu sunata rabon kud'i maro'ka nasake wasa d'an su gamida sama aure albarka y'an jarida da y'an gidan TV dasuka zo domin haska d'aurin auren d'an Alhaji Bilyaminu motors sukaita mamakin ya haka tafaru d'aurin aure yajuya akan wani shin menene yafaru abokan Ahmad kuwa sai kiran shi suke awaya ransu amatuk'ar b'ace yayinda Sulaiman yanufa can gidan domin jin ya akai aka haihu aragaya duk dacewa dama yasan Hamza nason Haulat amma dayaga zata auri Ahmad yad'auka sun rabu ne,
Cikin farin ciki Hamza keta gaisawa da mutane duk da bai sansu ba yayinda gidan TV keta haska al'amarin wani d'an jarida ya'kariso wajen Hamza dashi da masu d'auka live TV yana fad'in "Ranka shidad'e ya akai d'aurin aure yakoma kanka alhalin da d'an Alhaji Bilyaminu motors za'a d'aura?"
Wani k'ayataccen murmushi yasaki yana shafa suman dake tsakiyar kanshi irin na sojoji dasuke bari yace "Ha'kik'a komai nufine na Allah dama haka Allah yatsara Haulat mata tace batun wanda kuke magana akanshi kuwa ban san dalilin shi nakin auran Haulat ba dan dama shiga hanci da k'udundune yamin nina fara son Haulat sainazo nayi tafiya ban dawo dawuri ba shine yaso yayi wuf da ita Allah yace batashi bace tawa ce"
Kai d'an jaridan yajin jina yasake cewa "Shin wani irin farin ciki kake ciki ayau daka samu muradin ranka"
Murmushi yasakeyi while hannun shi nacikin kanshi kamun yacire yasaka acikin rigarshi yace "Gaskiya dukkanin abunda zanyi ayau minus ne dan bazai ta'ba kwatanta irin farin cikin danake ciki ba ayau saidai nace Alhamdulillah"
Yana kaiwa nan azancen sa yasa kai yafara tafiya sojojin shi suka take mai baya already ankawo motocin su nan dan haka suka shiga sai gidan su Haulat.
Ab'angaren Aliyu kuwa sai safe suka zo gaisar da Ammi inda ta amsa fuska akimshe kamun tace "kuzauna ina son magana daku"
Ba musu duk suka zauna jikin su asanyaye barinma Aliyu dayasan maganar shice fuska ba walwala takalle shi tace "kanace saika auri Haulat akaro na biyu KO harke dabaki san ciwon kankiba kina son kisa kanki amaganan KO tokujini dakyau dagake harshi d'in zan sallamaku kaje ka aura Haulat amma zakaga abunda zai faru indai nina d'au nauyin cikin ka tsawon wata tara nashayar dakai watannin ashirin da hud'u zaka ga abunda zai faru dakai muddun baka bar maganar Haulat ba kacire ta arayuwar kaba!" Tana kaiwa nan tatashi tashige d'aki tabarsu nan bayan wasu y'an sakwanni tafito KO kallon inda suke batayi ba,
Gaba d'aya kan Aliyu yagama cud'ewa da'kyar ya ara jarumta yami'ke yafuta yama Humaida sallama yanufa wajen aiki cike da damuwa yanzu yahak'ura zaima Haulat fatan alkhairi asabuwar rayuwar dazata fara shikuma yarungumi Humaida amatsayin sakayyar abunda yadinga yima y'ay'an mutane,
Ammi direct gidan Alhaji Bilyaminu motors tanufa da'kyar da sid'in goshi aka barta tashiga gidan aranta tace daular duniya lallai Hausi to karyan Ku auren nan sai ya lalace agoben bayan sun gaisa da hajiyar su Ahmad ne tafara bata bayani inda tace aje har can mak'arfi shehu idris d'in ayi bincike,
Hajiya Amina batai k'asa agwiwaba takira Alhaji Bilyaminu tashaida mai komai take yabaro kasuwa yazo yasamu Ammi tasake gaya mai komai yace tazauna akwai wanda yasani amakarantar dan shine shugaban makarantar yanzu bayanin Haulat yamai take yace yarik'e waya after one hour yakira Alhaji Bilyaminu yatabbatar mai da gaskiyar maganar yamai godiya suka yanke waya Alhaji Bilyaminu yaba Ammi kyautar naira dubu hamsin Hajiya Amina kuma tabata kyautan Super da hijab suka mata godiya sosai akan taimakon su datayi tanusar dasu,
Haka tadawo gida cikin farin ciki tana ta zagin Hausi da Haulat tana irga kud'in ta tatura k'asan pillow cikin farin ciki. Wannan ne abunda yafaru.
Ana d'aura aure Kawu yanufa gidan Mama yadank'a mata sadakin Haulat naira dubu d'ari yashaida mata aure yad'auro take Mama tafashe da kukan farin ciki tana dariya alokaci d'aya tabbas wani baya auren matar wani wata bata auren mijin wata hamdala tayi tanufa cikin gidan tana rangada gud'a take Inna Hauwa'u da Inna Halima suka fara gud'a suma suna fad'in ina Haulat d'in take?
Haulat na d'aki su tun safe take kuka kamar me sabida yanda zuciyar ta keta bugawa ga wani zazzafan zazza'bi daya rufeta dole Salma tafuta tasiyo mata magani tasha tace takwanta tasamu rest inta tashi tayi wanka tayi kwalliya tunda ba'a kawo lefe ba sai d'inkin dasuka d'inka anko kala uku itada Salma da Maman ta,
Cikin ikon Allah barci yakwashe ta acikin barcin tayi mafarkin Hamza yadawo gareta yana murmushi yami'ka mata fure da hannun shi zata kama kenan gud'a yasauka acikin kunnen ta tatashi zaune tana mutsike idanun ta zuciyar ta nakarye wa yanzu shikenan tazama mallakin Ahmad wasu hawaye ne suka zubo mata daidai nan Inna Hauwa tashigo d'akin tana sake rangad'a gud'a turus taja ta tsaya saikuma takalli Salma dake gyara mayafi taci kwalliya da wani dakakken lace ga k'aramin cikin ta da yafito d'an kwas dashi sosai tayi kyau b'ata fuska Inna Hauwa tayi tana fad'in "mezan gani amarya ba kwalliya ke kina ta zuba k'amshi kamar kece amaryar?"
Baki ta tura tace "tun safe take fama da zazza'bi saida naje nasiyo mata magani ina tunanin zazza'bin yasauka bara nadawo nakai mata ruwan tayi wankan"
Ta'karisa zancen tana shirin futa Inna Halima tace "to daddawa sarkin miji basai tajira ki kindawo ba yanzu zatai wankan ta, ke Haulat tashi futo kiyi wanka aiba labari amarya ba kwalliya" tafad'a tana barin d'akin,
Ajiyar zuciya Haulat tasauke dan zazza'bin yasauka sai kasala kamar me data rufeta gaba d'aya kamar anzare mata laka ajikin ta wani sabon sanyin ne takeji nashigan ta kanta a'kasa tanajin Inna Hauwa nata tsokanar ta data zama ta zama tazama d'auko riga tazama d'auko buta tazama d'auko wando,
Ajiyar zuciya tasauke tana lumshe idanun ta tuna ranar auren Aunty Salma haka tadinga mata wannan wa'kar Inna Halima ne tadawo takama ta har bakin bayi takaita tace inbazata iya wankan ba tamata kanta a'kasa tace zata iya tana shiga bayin taji jiniya yacika unguwar wani irin bugawa zuciyar ta tayi tafara zare idanu kamar tafuto daga bayin wannan shine ake kira ga k'oshi ga kwanan yinwa........✍🏼

_*Kuyi share dan darajar Allah da manzon sa🤲🏼*_

*🤲🏼😭Innalillahi wa-enna ilaihirraji'un*

*WAYE SANADI!?*
*CARBIN K'WAI paid*
*RANAR MASOYA paid*
(Valentine day)

Dan Allah masoya na masu bibiyan litattafaina ina mai baku ha'kuri abisa abunda yake shirin faruwa damu definitely gobe laraba za'a katse mana network😭 kuma basu fad'a date line daza'a amaida ba dan haka ina mai baku ha'kuri dajina shiru dazakuyi musamman wad'anda suka siya CARBIN K'WAI da RANAR MASOYA insha Allah dazarar ansaki zakuji ina alfahari daku masoya na k'ashin bayan nasarata Allah yakare mu yatsare mana imanin mu🤲🏼😭 Allah yatasare mu da aikin danasani ya hayyu ya qayyum ka kawo mana d'auki

Sa'ko daga
*Ummu Sumayya*
Bintubaby

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONEWhere stories live. Discover now