PART ELEVEN AND TWELVE

288 26 3
                                    

*WAYE SANADI?!* 🪦🪦

           *By*
*Ummu Sumayya*
*Wattpad #Bintubaby*

*PAGE ELEVEN AND TWELVE*

Jiki na kakkarwa Aunty Salma taxube tana damk'e bakinta dan gani take tana yin kuka zasu harbe ta hannun Haulat tafara ja amma Haulat tafisge tana watsa ma sojojin wani d'an iskan kallo duk dacewa ita kanta ta tsorata dasu amma saita dake tana kallonsu cikin hasken farin wata da wutan hasken sola dasuka haska layin dan magrib ta wuce duhu yarufa,
Gaba d'ayan su shakkar ta sukeji domin basu ta'ba had'uwa da yariny'a mai tsayayya kamar wannan ba gashi Oga yahana atab'a ta, wanine yayi k'arfin halin cewa cikin hausar shi dabata futa dan ba musulmi bane "heeee shegen yarinya wuce muje Oga na kiranka"
Cikin dakiya da k'arfafa zuciyar ta tana addu'a Allah yarabata dasu lafiya dan tasan suna iya d'aukan ta sumata fyad'e dan sojoji basu da imani tsayuwarta tagyara cikin tsaurin idanu tace "Bani bace shegiya uwarka ce shegiya and gidan ubanwa zanje dakake min tsawa bakajin abunda nacema d'an uwan kaba d'azun ko? To wallahi ka kiyaye inba hakaba akan ka zan huce fushin tafiyar k'asan dakuka samu zamuyi yanzu"
Cikin b'acin rai wani yad'aga hannu yasharara mata mari dan gani yake rainin hankalin ta yayi yawa taya za'ai tadinga zagin hukuma sukasa d'aukan mataki akanta kafun ta wartsake tasake jin wani kyakkyawan marin saman d'ayan kuncin nata yau saidai akore shi awajen aiki amma bazai tsaya yarinyar da ahaihuwar kaji sun haifeta ba tai ta raina musu wayau ba gaba d'aya jikin shi kakkarwa yake yana jiran kota kwana daga gareta,
Dawani irin sauri suka ri'ke shi da tsoron abunda zai biyo baya,
Wani irin kafe shi tayi da idanu idanun ta babu k'wallah KO d'aya duk dacewar marin yagigita ta har jida ganin ta suka d'auke na wucin gadi wani irin kau kau takeji a kunnunwan nata kamar anbuga abu mai k'ara acikisa idanun ta sun mugun kad'awa muryan Aunty Salma taji tana fad'in
"Officer kuwa Allah kuwa annabi Muhammad s.a.w kuyi ha'kuri wallahi tanada tab'in hankali shiyasa kuyi ha'kuri kubarmu muwuce"
Wanine yace "madam so sorry to say Oga ne yace mukaita kuma wallahi bazamu tsallake umarnin saba dan haka kijata mutafi wajen sa kawai kwabashi ha'kuri inya ha'kura muba ruwan mu"
Jikinta yana wani irin kyarma tami'ke tafara jan Haulat daba musu tabita kuma har lokacin idanun ta na kan wanda yamareta da tunanin hukuncin dazatai mai ahaka suka k'arisa gaban Oga Hamza dake cikin moto k'afafun shi na waje saida kana iya hango fuskar shi sabida waya dake dannawa tuni mutane sun cika wajen duk da d'ar d'ar d'in dawasu keyi amma masu taurin kunnen suna daga nesa suna hangen abunda ke faruwa yayinda wani yaro yatafi dagudu yagayo ma Mama dake ta zuba idanun dawowar su KO sallah takasa yi ranta duk ajagule akid'ime tabiyo yaron tana salati da sallalamin meye yahad'a su fad'a da sojoji.
Wanine yadaka musu tsawa yace suyi kneel down Salma daketa hawaye ba bakin kuka taduk'a amma Haulat da zuciyar ta ke suya da tafarfasa tayi kunnen uwar shegu jira take Ogan nasu yafito tarama marin da akai mata akan shi inyaso duk abunda zai faru saidai yafaru 🙆🏽‍♀️😳🤣
(K'ut gaskiya Haulat jaruma ce General Hamza zaki mara aradu babu ruwa na🏃🏽‍♀️)
Ganin bazata duk'a bane yasa sojan yashareta yakoma yana jinjina taurin kunne da tsaurin idanun yarinyar danshi tunda yashiga soja bai ta'ba had'u wa da tantirya irin wannan ba,
Tsayin mintuna kusan talatin sannan yafito daga motan yana k'are mata kallo afakaice fuskar nan kamar anyi gobara idanun shi sanye cikin glass ba'ki daya b'oye ainihin yanayin da idanun shi yake ahankali yarufe motar yatsaya yana k'are ma sojojin dasuka k'ame kamar ba numfashi ajikinsu kallo baki yad'an tab'e yakalli Haulat da take kallon fuskar shi babu KO kiftawa  a idanun ta yahango tsoro da fargaba akwance tsayuwa yagayara yana kallon ta dakyau kamun calmly yace "My sister kneel down"
Cikin rashin kunya tace "bazanyi ba inkuma zaka iya sani nayi dole to sani naga"
Glass d'in yad'an cire yana kallon yanda pinkish lips d'inta ke motsawa aranshi yaraya "any'a mutun ce kuwa? Bai ta'ba had'uwa da wanda yakalle fuskar shi yamai rashin kunya ba sai yau ko sojoji tsoron tun karan shi suke saboda tsaban kamewar sa" Amma bari yad'an koya mata hankali gab dasu ya'karisa cikin takun k'asaita da izzar jinin soja dake yawo ajikin shi daga yanayin tafiyar shi zaka gane jarumi ne mai bama maza wuta duk da ta tsorata amma saita dake takauda fuskarta tana addu'a acikin ranta kusa da ita ya'karisa yana k'are mata kallo saikuma yajuya yace "Captain Mk"
Cikin sauri wani yace "yes sir" yana k'araso wa gaban shi kafun yayi magana yaga tad'aga hannu cikin mamaki yatsaya kawai yaga tanufo fuskar shi dasauri yarik'e hannun dawani mugun k'arfi yana kallon ta fuska ad'aure lallai wannan tantiriyar mara kunya ce shizata mara wani irin murd'a hannun yayi yana kallon ta fuska ad'aure yace "are you mad" yafad'a yana sake murd'a hannun cikin mugunta yana kallon idanun ta dasuka tara k'wallah amma ta'ki yin ihu shi so yake yaji tana ihu tana ro'kon shi amma ina,
Duk abunda yafaru a idanun Mama cikin tashin hankali tashiga gidan Yayan babansu dake kusa ne Allah yataimake ta yanacin abinci alamun bai san wainar da ake toyawa ba tun da kusa da gidan shine tana kuka tashaida mai gasu Haulat can ahannun sojoji batasan mesukayi ba cikin sauri yami'ke yana fad'in "Subhanallah Allah yakyauta gaba muje KO" yafad'a yana saka takalmin shi suka futa cikin azama yatun kari sojojin yana xuwa ya'karisa inda su Haulat ke tsaye idanun ta na tsiyayar hawaye kanta aduk'e kuma har lokacin bai sakin mata hannu ba sai murd'a shi yake idanun shi akanta fuskar shi ad'aure kamar besan wani abu waishi dariya ba, da azama ya'karisa garesu kasantuwar shi na tsohon soja yasa baiyi shakkar isa garesu ba yana isa yamarairace cikin ladabi yace "Officer ayi ha'kuri dan Allah yarane basu san komai ba kawa darajar iyayen ka ka k'yale su kaga mata ne ba maza ba sunada rauni"
Ranshi amatuk'ar b'ace yakalle mutumin saikuma yaga yamai kwarjini har yakasa cewa komai wata zazzafar iska yafurzar yana sakin hannun nata sabida arayuwar shi yana mutunta tsoho koyaya ne ahankali yajuya batare dayace komai ba yanufa mota dasauri wani soja yaje yabud'e mai yashiga sauran ma suka shiga motocin su suka tayar suka bar layin da wani irin space ajiyar zuciya yasauke yana tura hannun shi cikin sumar kanshi yalumshe idanu fuskar tane tafara mai gizo muryan ta namai amo _"Bazanyi ba inkuma zaka iya sani nayi dole to sani naga"_ wani irin murmushi yasaki yace _"That's my new catch saina koya miki hankali"_ yafad'a ahankali gefen titi yak'ura ma idanu kamar me irga motoci dahaka suka isa janguza barracks saida yatabbatar kowa yaci abinci yayi sallah sannan yatara su akausashe yace "how's betting her?" Gaba d'aya sai suka fara zare idanu cikin tsawa yace "we don't here what an saying I say how's betting her?" Dasauri wani yace "sir" idanu yad'an kad'a yace "oh you're betrayed me sergeant Mubarak"
Kai yaduk'ar jikin shi na kyarma,
Cikin b'acin rai yabada umarnin aje akulle shi a guard room juyawa yayi yana basu umarnin suje suci gaba da aikin su sama ya haura cikin sassarfa kwanciya yayi yana shafa fuskar shi Mommaa yakira yashaida mata yaje gidan Ammi sun d'an jima suna waya kafun su katse kwanciya yayi idanun shi akan pop d'in bedroom d'in gaba d'aya tunanin ta ya addabe shi ya hana shi sa'kat dazarar ya rufe idanu ita yake gani kwanciyar shi yagyara yana tuhumar kanshi akan meyasa yarik'e mata hannu lumshe lumsassun idanun shi yayi yana furta "ya Allah!" Saikuma yasake k'ank'ame pillow jin yanayin shi yafara sauyawa da'kyar yasamu barci yakwashe shi mai cike da mafarki akan yarinyar da ko sunan ta bai sani ba.
Me keke napep dake gefe yasaki ajiyar zuciya yak'arasa wajen  Haulat daketa kuka Salma na k'ok'arin janta sutafi Mama dake bayan su tuni tai gaba sannu yamata da Allah kyauta Salma ne ta amsa shima tamai sannu da jajanta ma juna sannan yatada napep d'in shi dake wangare agefe yatayar da ita yabasu kayan su dasuka zube saboda ledan ta yage yajuya yabar layin.
Harsuka isa gida Haulat kuka take saboda zugin da hannun yake mata dan har ya kumbura suntum sai shining yake Mama ne tad'auko tabarma tashimfad'a atsakar gida kawu yazauna yana kallon yanda Haulat ke yarfe d'ayan hannun tana kuka sosai dan harda ihu take sabida azaban datake ji ahannun
Kai Kawu yagirgiza yace "Salamatu menene yahad'a ku da babban soja mai mu'kamin janar?"
Hawayen fuskar ta tasharce tana kallon Haulat daketa kuka tana yarfe hannu idanun ta taduk'ar tabasu labarin dukkanin abunda yafaru, kai Kawu yagyad'a yana fad'in "Asha asha Allah yakyauta gaba amma Haulat ina miki kallon natsatstsiya shine kika tsaya fad'a da maza atiti kowa yana kallon ki kina mace yanzu kinsan fassarar da za'ai miki alayin nan kuwa kuma menene ribar ki nayin hakan?"
Shiru tamai tana kuka har lokacin still tana yarfa hannu dan ita kad'ai tasan azabar datakeji,
Mama kam jitake kamar tarufe ta da duka tsaban takaici tami'ke tashige d'aki cikin ba'kin ciki dama tabari sun mata d'an banzan duka gobe tasake tsokanar su,
Cikin tausayi Kawu yace "Haulat zo muga hannun!"
Dasauri ta'karisa garesa,
Hannun yakama yana karanta wasu addu'oeh wani irin razanannen ihu tasaki saiga fitsari ya kucce mata tsaban azabar datake ji wacce bata ta'ba jin makamancin taba tafara k'ok'arin kwace hannun amma yadam'ke shi dakyau dasauri yama Salma nuni data ri'ke ta aiko tazo takama d'ayan hannun shikuma yaci gaba da gyara hannun yana mata addu'a yana shafawa tsayin lokaci yakira Mama dake d'aki har lokacin yace takawo mai k'yalle yad'aure hannun ba musu tajuya tad'auko tsohon zaninta tayaga aka nad'e ma Haulat hannu wacce gaba d'aya zufa yagama jik'a ta tadaina kukan sai ajiyar zuciya take ta saukewa,
Kallon Mama yayi yace "dan Allah ki kula da ita da hannun nan dasafe zan kawo mata shafi karaya ne tasamu ahannun"
Baki Mama tata'be d'onainai tace "to shikenan Allah yasaka da alkhairi"
Da amin ya amsa yami'ke yamusu saida safe yatafi,
Ajiyar zuciya Salma tasaki tami'ke tayo al-wala tayi sallolin dake kanta sannan tazauna tanuna ma Mama kayan da kud'in da aka basu amsa tayi ta k'irga kud'in da fara'ar ta tace "kai masha Allah, Allah yasa nema rabone kaga iyayen arziki irin arziki" ta'karisa maganar tana kalmashe kud'in taci gaba dacewa "wannan gobe zan shiga kasuwa nasai miki kula da sauran tsince tsince na kitchen naira dubu sittin ne inkuma da abunda zakiyi dasu to kigaya min"
Murmushi Salma tayi cikin kunya ta girgiza kai alamun ba'a abunda zatayi dasu,
Haulat kuwa duk da halin datake ciki saitaji wani iri wata kan itace tsinanniya ba'a maganan sai mata  kayan kitchen k'wafa tayi tami'ke tad'auki buta taje bayi ta tsaftace jikinta tashiga d'aki da'kyar ta iya canza kaya ta kwanta akan katifa tana lumshe idanun ta duk da yinwar dake sasik'arta hakan baisa tami'ke taje taci abinci ba tin tanajin firan su sama sama har barcin wahala ya kwashe ta.
Ammi na gida labarin abunda yafaru yazo kunnen ta nanfa tasake fusata tadinga zazzaga masifa Humaida na ziga ta nan tafito backyard tazauna akan kujera zaman jiran Aliyu yadawo sai wajajen tara yashigo aiko ta tsaya agaban shi tace tabashi nan da gobe yajanye maganar auren Haulat inba hakaba ba ta tsine mai duk yanda yaso magana hanashi tayi hakan yasa yashiga side d'in shi cikin tashin hankali da tunanin neman mafita aranar barci duk satar shi haka ya'kyale shi asubhar fari yakira Haulat yagaya mata halin da ake ciki aiko ta kwantsama mai wani uban ihu mai firgitar wa dasauri yakashe wayar shi, shikan shi yanacikin matsanan ciyar damuwa da neman mafita dan akan mace bazai ta'ba b'ata wa da mahaifiyar shiba macen ma wacce yasanta tun awaje baima san iya wad'anda sukan
san ta ba bayan shi dan mata ba amana daga sun san dad'in namiji shikenan.
Washe gari daya tashi saida yayi wanka yashirya yafuto dan zuwa wajen dayaje cos gaba d'aya jikin shi asanyaye yake bashi da wani kuzari tunanin yarinyar yahana shi sakat abu kad'an yayi murmushi yalumshe idanu yana shafa kai gaba d'aya sai yawani zama silent danko magana awunin baiyi ba saidai nuni da idanu suna tashi wajen aiki 5:43 yace sunufa gwamja gaba d'aya escort d'in suka kalla junan su da mamakin mezasu koma yi cikin bin umarni suka shiga motoci sukai cikin kano dan cika umarnin Ogan nasu,
Suna shiga farkon layin yatura ma driven dake jan motan farko text message kamar haka _*Ka parker anan kaje ka binciko mana gidan su yarinyar nan!*_
Lokacin da text message d'in yasami driven sosai yayi mamaki saikuma yayi murmushi dama tunda yaji Oga nacewa karsu ta'ba ta yasan dawata jik'akk'a! Futa yayi yatambaya aiko baisha wahalaba aka kwatanta mishi gidan dan wani mai faci yatambaya kuma ajiyan yaganshi yasan bazai rasa sanin taba cikin mota yashiga yatada suka k'arisa k'ofar gidan duka motocin sukai parking dasauri sojojin suka futo suka tsaya abakin motan dajiran kota kwana,
Gaba d'aya sai yaji wani iri baima san mezaice yazo yi wajen taba kanshi yad'an shafa da sajen fuskar shi yafesar da iska yana tunain abin yi text yatura ma captain Mk yace susamu yaro akira Maman yarinyar,
Ba musu aka samu yaro aka aika gidan ba jimawa yafito yace tace gatanan zuwa sallaman yaron sukai suka tsaya jiran tsammani...........✍🏼

*Idan kuka matse hannu nima na matse kuga typing kad'an baruwana yasin more comments more typing innaga comments dayawa anijma kuga new update🤣🚶🏽‍♀️💃🏽*

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt