FIFTY ONE AND FIFTY TWO

277 22 10
                                    

🌺🌺🌺🌺
*WAYE SANADI!?*🪦🪦

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO📚✍🏼*

*_My fans ina cikin damuwa ina cikin wani yanayi dan Allah ina barar addu'a agareku duk wanda yakaranta wannan page d'in yamin addu'a Allah yashiga tsakanina da mak'iya na😭😭 Allah kar yabasu ikon cin nasara akaina yau ina rubutu ina kuka😭😭 kumin addu'a dan girman Allah🙏🏼👏🏼Allah_*

*FIFTY ONE AND FIFTY TWO*

"Don't torch me!"
Wani irin tsayawa yayi cak yana kallon ta cike da mamakin ta da mamakin kukan data keyi dak'yar ya lalubo haraffan dazai furta dan tabashi tsoro gaba d'aya yace "ban gane inda kika dosa ba me hakan yake nufi? and kukan me ma kikeyi duk kinbi kinb'ata kwaliyyar ki! Kinn san nawa nabiya akan make up d'in nan kuwa?"
Wani irin banzan kallo ta watsa mai zuciyar ta na dad'a zafi jin wai baima san kukan datake yiba wani zazzafan hawaye ne yasake ziraro mata takauda kanta gefe zuciyar ta na tuk'uk'in bak'in ciki tafara takawa ahankali saboda hill d'in k'afar ta ga rigar ta mata yawa ta gefen shi take shirin bi ta wuce yawani fisgota ya had'a da jikin shi yana watsa mata wani irin kallo mai cike da mamakin sauyin ta yace "Baby Hazlat gaya min menene yake faruwa?"
Idanun ta aruntse still hawaye na futa jin k'amshin turaren Dija ajikin shi k'ok'arin k'wacewa take yasake rik'eta dakyau cikin sansanyar murya yace
"Am ask you again what's wrong with you?"
Shiru tamai,
Ganin alamun bazata tanka bane yasa yaji jikin shi yayi mugun sanyi yasake cewa "shike nan am sorry duk da ban san abunda nayi ba am sorry once again My Zuma"
Yak'arisa maganar yana d'an shafa fuskarta kamun kuma yakalli hannun shi 10:42 kanshi yad'an dafe yace "uhm let's go kinga munyi african time muje na goge miki fuskar ki"
Yak'arisa maganar yana d'aukanta cak,
Idanu kawai ta runtse tanajin yanda yake taka step d'in har suka k'arasa d'akin sa da k'afa yatura k'ofar agaban mirror ya zaunar da ita yazaro tissue yafara goge kwaliyyar data lalalce still fuskar ta ahad'e dan tak'i bud'e idanun ta,
Saida yakammala goge fuskar gabaki d'aya kamun yamik'ar da ita yad'an d'age mata rigarta saboda bayana yanajan k'asa murya araunane yace "Baby Hazlat dan Allah karkiyi abunda zai janyo attention d'in mutane kanmu kinga ana ganin darajata da k'imana kisaki fuskar ki please!" Yak'arisa maganar yana wani langab'ar dakanshi gunun ban tausayi,
Kallon shi kawai tayi takauda kanta kamun tafara tafiya shikuma yabiyo bayanta,
Dija na zaune tana waya da Mom d'in ta tana kuka tana labarta mata abunda yafaru fitowar sune yasa tawani katse kiran batasan ma ta mik'e ba, kallon Hamza dake rik'ema Haulat da riga take baki sake harsuka k'araso inda take Hamza yad'an kad'a mata yatsa afuskarta tayi firgigi ganin su gabanta saita k'irk'iro murmushin yak'e tawayance tana goge hawayen fuskarta kamun takashs wayan ta tajuya ga Haulat dataga tamafi kyau ba makd up d'in tace "Aunty Amarya gaskiya kinyi kyau sosai"
Wani banzan kallo Haulat ta watsa mata sama da k'asa kamun tasaki murmushin gefen baki tace "ina godiya"
Yak'e tasake yi tana satan kallon Hamza dake answering call kafun tayi magana yajuyo gareta yace "Yawwa Khadii zamu futa komai yazama ready mu ake jira kid'aga mata riga"
Wani irin kallon shi take kamar wata gaula kamin tace "kamar ya ban fahimce kaba"
Saida yamik'a ma Haulat d'an tulun basket d'in ta sannan yace "kamar yanda kikaga na mata yanzu dazamu fito dan Allah d'aga muje jiranmu akeyi nashanya mutane arana"
Tana y'an k'unk'unai tad'aga ma Haulat d'in riga tanajin itafa kam ta muzanta,
Hannunta Hamza yakama suka fara tafiya atare suna zuwa k'ofaa taga anbud'e kamar amsan da zuwan su, da mamaki take kallon yanda sojoji suke tsaye daki daki hannun hagu da dama daga can bayansu ga mata nan kowacce taci kwalliya na kece raini sunyi anko cikin wata atamafa dukkanin su wasu sanye da hijab wasu gyale kowacce tana tsaye da abu anyi raping da alamun gift e kallon ta tamaida ga Hamza yawani sakin mata murmushi maida mai martani tayi kafun tayi wani tunani taji k'aran ganga da busan algaita natashi sojojin gaban su kuma duk suka k'ame can kuma sai wajen yayi tsit wani soja yace
"Sword party attention"
Gaba d'aya suka sake daidaita, sojan yasake cewa
"To the Bride and groom..... cross sword"
Gaaba d'aya sai sukayi crossing sword d'in,  masu algaita da ganguna suka ci gaba da bugawa,
Hannun ta Hamza yasake damk'ewa suka fara tafiya ahankali Dija na biye dasu tana ta guna guni, suka shiga tsakiyan sword d'in har saida suka futa zuwa inda matan nan suke sannan suka joyo ga sojojin sara musu Hamza yayi gamida k'amewa suma duk sara mai sukayi suka k'ame kafun kuma one by one sufara zuwa inda suke suna bashi hannu suna mai congrat, tight friends d'in shine suka janye shi,
Haulat ko wad'annan matayen ne suka dinga bata side hug suna mata congrat ana bata gift Dija na taya ta karb'a dan hannun ta ma yacika,
Wata babbar mace ne takariso tana sanye da atamafa army green da ratsin kakin sojoji ajikin atamafar dan gaba d'aya wajen duk itace ajikin su saida ta rungume Haulat kamun tace "My name is Nana Firdausi but you can call me Jannat general's wife Happy marriage life Mrs Hamza congratulations"
Cikin farin cikin yanda matar ta mata bayanin kanta tace "thank you Aunty Jannat"
Murmushi Jannat tayi tasake cewa "so....on behalf of the Nigerian army office's wive association.... I want welcome you officially to the association....known we stand by our men and our children when they come while are men stand for our country.... We want to give you this as a token of our love" tak'arisa maganar tana amsan atamfa wacce ba d'in kakkiya ba ahannun wata soja mace tamik'e ma Haulat,
Saida Haulat tarage tsawo sannan ta amsa atamfar sannan tace "Thank you soo much Aunty Jannat"
D'ago ta tayi tad'an rungume ta tace "don't worry they are together"
Godiya tasake mata sannan tad'an daga kanta can tahangi Hamza nata faman dariya acikin friends d'in shi da mamaki takafe shi da idanu ashe dai yana dariya dama,
Ganin anfara watse wane yasa Aunty Jannat ta taimaka musu suka kwashe gift d'in zuwa cikin gidan sannan tad'an zauna tana yima Haulat d'in tambayoyi Dija ko na gefe sai kumbura fuska take tana danna waya tana jiran Hamza yazo danshi zai maidata gida,
Hamza kuwa yana tare sa abokan shi guda biyu Nura da Nazir baida kamar su dan tare sukai passing out kuma tare suke aiki amma suna k'asan shi tsokanar su yake sunk'i aure d'ad'i yabar su shikam nan da nine months zai zama Daddy,
Nura ne yad'an b'ata fuska yace "no problem i will marry your first born"
Wani wawan naushi yakaimai yana fad'in "Shege d'an iska wallahi yarinya na bazata auri tsoho ba"
Nazir ne ya kwashe da dariya yace "Partner nidai friend d'in matar ka tamin kamin hanya nayi wuf da ita kaga wannan sai yazama mai yimana cefane"
Wani duka Nura yakai mai yana fad'in "Buddy wallahi kaima kace wani abufa but nidai ina jira first born d'in ka my sirirki"
Yafad'a yana kallon Hamza,
Dariya yayi yakalli Nazir yace "are you serious she's my cousin sis bana son yaudara fa!"
"Masha Allah that's Yayan mu dagaske nake indai na mata sai zancen maganar aure fa"
"Lallai Buddy bada wasa kake ba Allah yatabbatar" yafad'a suna tafawa suka nufa gidan Hamza Dasauri Nura yabi bayan su yana fad'in "Buddy ina kan baka nafa first born nake so tom"
Kai kawai Hamza yagyad'a aranshi yana mamakin Nura dan tunda suke tare bai tab'a ganin ance gabudurwar Nura ba Nazir nema acikin su mai kwashe kwashe,
Da haka suka shiga gidan suka tadda su suna zaune saidai kafun su zauna saiga Mom d'in Dija da matar Yayan Baban Hamza sai wata wacce Haulat bata san kowa cece ba,
Tunda Haulat taji sallaman su zuciyar ta ke wani irin dukan tara tara ganin yanda suke k'are ma palourn kallo kowacce cike da yatsina,
Aunty Jannat ne tamik'e tana fad'in "amarya bara naje na d'aura lunch sai gani na biyu ko?"
Tsaban yanda takeji takasa amsata sai kai data d'aga tana yak'e,
Saida suka gama kalle kallen su sannan suka zauna akan many'an royal cushion d'in,
Daidai Haulat ta gama gaishe da friends d'in Hamza suna tsokanata da "Ya amarci hope abokin su bai mata rawan kai"
yak'e tayi kawai tamik'e tanufa kitchen dan kawo musu ruwa ta tsinkayi muryan matar yayan baban Hamza na fad'in,
"Wani rawar kai zaiyi abunda sauran wasu k'artai ne yasamu ai sai hak'uri"
Cak ta tsaya jikin ta na wani irin mugun tsuma zuciyar ta kamar zata fasa k'irjin ta tafito tadafe ta wad'ansu zafafan hawaye na zubo mata aranta tace "tafaru ta k'are!",
Hamza ko wani irin had'e fuskar shi yayi cikin zafin rai yace " Aunty Saudat which cain of nonsense is that are you in your on sense? "
Wata uwar harara tazuba mai kamun tafara tafa hannu tana fad'in "innalollahi wa'enna ilaihirraji'un Hamza yanzu nikake cema mahaukaciya akan wannan matar naka dan nafad'i gaskiyata koko k'arya nake ita d'in ba sauran k'artai bane tazo ta musa min mana intana da gaskiya kake bud'e baki kake cemin banda hankali lallai duniya yau da Alhaji na raye dayaga abun al'ajabi d'an dana raina ne yake cemin mara hankali akan mace yiiiiii"
Tafashe da wani irin kuka matar kanin Baban Hamza tawani kwand'e baki tace "sai hak'uri kin san ba haka aka barshi banza ba daga shi har uwar tasa,  kidaina ma asarar hawayen ki kitashi mubar mai gidan sa kafun yakaiga dukan mu akan wannan kodadd'iyar mara tarbiya karuwa!"
Mikewa Mom d'in Dija tayi tana sharan kwallah tace "Muje Hajiya Amina komai yamin nina kawo kaina daga fad'in gaskiya ba komai wannan shine tukwicin da zai saka min dashi"
Ganin sun nifa k'ofa ne yasa Dija tarufa musu baya tana maganganu k'asa k'asa,
Suko su Nazir gaba d'aya y'an kallo suka koma babu wanda ya iya magana yayin da Hamza ranshi yayi mummunan b'aci akan tozarcin da akaima Haulat agaban abokan shi makusan ta jab'ar yazauna akan kujera yana dafe kanshi dak'yar yafurta "Innalollahi wa'enna ilaihirraji'un Allahumma ajirneee fii musiiibatee" yafesar da wani irin zazzafar iska yana lumshe idanun shi,
Nura ne yad'an dafashi murya asanyaye yace "don't worry friend everything will be alright karka damu da abunda mutane zasu fad'i tunda kana son matarka kaci gaba da addu'ah Allah yakauda fitina kaji!"
Kanshi yagyad'a kawai dan baiso wani yasan matar shi ba virgin bace,
Nazir ne yace "Buddy don't mind yourself about what that old woman say ana ganin mace agidan karuwai ma a aurota azauna da ita balle kai nasan kawai k'ilan basa son tane yasa suke mata sharri kayi hak'uri kaji!"
Dak'yar yafurta "thanks!"
Gaba d'aya suka mik'e sukace zasu wuce bai iya yamusu rakiya ba kawai yasake musu godiya,
Haulat kuwa da gudu tak'arisa d'akin ta tafashe dawani irin kukan bak'in ciki nadama da dana sani shin yazata dawo da hannun agoga baya ita kuma kaddarar ta kenan Aliyu da Dija sun cuceta kuka take sosai kamar ranta zai futa tana magan ganu na nadama tanajin inama ta mutu ta huta aure kwana 15 kwana d'aya gidan miji amma k'aluben dake cikin sa sun shallake tunanin ta,
Saida tayi kuka ma'ishinta kamun ta lallashi kanta dak'yar tasamu taje tad'auro alwala azahar ta gabatar tajima tana kuka akan sallayar tana rok'on Allah mafita zamewa tayi ta kwanta bayan tashafa addu'ar still hawaye na zuba a idanun ta ahaka barci yakwashe ta,
Hamza ko saida yaje yayi sallar la'asar sannan yasake nufowa gidan still zuciyar shi ba dad'i a compound suka had'u da driver yakawo lunch amsa yayi yashiga ciki akan dining ya aje basket d'in sannan yanufa room d'inta akwance yaganta dasauri yak'arisa yana kai hannu saman fuskarta wani irin hucin zafi yafara mai sallama dasauri yad'agota gaba d'aya,  tabud'e idanu tana kallon shi sai kuma ta lumshe su hawaye suka ziraro saman fuskar ta,
Rungume ta yayi yana cire hijab d'in ta yaji jikinta rau tausayi tabashi yashafa wuyanta yamik'eda ita suka nufa d'akin shi kan gado ya kwantar da ita batare dayace mata uffan ba yajuya yajanyo drawer magani yad'auko palour yanufa bajimawa sai gashi da ruwa,
Jingina ta yayi da fuskar gadon yab'allo maganin yakalleta yad'an b'ata fuska yace "bana buk'atar sake ganin hawaye afuskarki nine nace ina sonki ahaka kuma zan zauna dake so no need kidinga min asarar hawayen ki, ki adana akwai inda yadace kimin kinji"
Sosai yabata tausayi har taji tana kunyar kallon shi, shin wannan wani irin sone Hamza ke mata?,
Murmushi mai sauti yayi yasa mata maganin abakib ta gamida samata cup d'in ruwa saida ya tabbatar ta had'iye maganin sannan yace "Baki san wani kalan so Hamza yake miki ba ko Haulat?"
Zaro idanu tayi kena  afili tayi magana ya ilahi,
Murmushi yasake yi yace "wannan shine so na gaskiya wanda zan iya ce miki yayi k'aranci awannan zamanin Haulat ina sonki badan kyan fuskar kiba badan kyawun surar kiba badan komai ba nikaina nakasa fahimtar ya akai na fad'a soyayyar ki ina son ki da dukkanin zuciyata abu d'aya nake so agareki kuma nasan insha Allah bazaki kasa yim...."
Kirane yashigo wayarsa d'an jim yayi saikuma yad'an saci kallonta yaga shi take kallo d'aga kiran yayi amma kafun yayi magana ya tsinkayi muryan Momma cikin fusata tana fad'in "duk abunda kake kabari kazo yanzu matuk'ar nice na haife ka!"
Tana fad'in haka ta katse kiran da idanu yabi wayar xuciyar shi na sake tafarfasa tabbas abunda Aunty tamai bata kyautaba kuma shiima yasan bai kyauta ba mik'ewa yayi yad'auki key a side drawer yana k'ak'alo murmushi yace "Baby Hazlat mezan taho miki dashi inzan dawo?"
Hawayen dasuka kawo a idanun ta take k'ok'arin maidawa dan taji abunda Momma tafad'a dak'yar tace "kaje kawai Allah yadawo min dakai lafiya"
Kiss yamanna mata agoshin ta yace "thanks"
Daga nan yasa kai yafuta da d'an sassarfa hakk'un fushin Momma ba dad'i kafun tayi ne aiki amma kuma intayi fushi babu dad'i.....✍🏼

*Me kuke ganin zai faro😟 hakk'un labarin Haulat wani lokacin inna tuna nikaina ina hawaye domin ta fuskanci k'alu bale iri iri arayuwar ta labarine mai nisan zango inaga munyi rabi yanzu dan haka kubini sannu sannu kuji yanda tata kaddarar take kasancewa bayan auren ta*

#Bintubaby

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon