PART ONE AND TWO

1.1K 61 8
                                    

🪦🪦 *WAYE SANADI?!* 🪦🪦

           *By*
*Ummu Sumayya*
*Wattpad Bintubaby*

*HONESTY WRITER'S*
*ASSOCIATION📚✍🏻*

'''{{THE HOME OF HONESTLY AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION}} '''
https://www.facebook.com/103166235165046/
                   '''🎖️H.W.A🎖️'''

*(NOTE dan Allah karki wuce kitsaya ki karanta)*
_Alhamdulillah for the gift of life, My fans ina mi'ko gaisuwa buhu buhu fatan alkhairi agremu gaba d'aya to gani naxo muku da wani book mai taken *WAYE SANADI?!* ban san yazaku amshe shiba but duk wacce bata bi daga farko ba anbarta abaya, agaskiya ban so yin littafin free ba to ganin abubuwa dayawa dasuke ta faruwa awannan zamanin namu yasa kawai zanyi littafin nan Free kuma bana tunanin maida shi na kud'i dan haka ku gyrara zama dakyau comments vote share like kawai nake bu'kata domin hakanne zai k'ara min kwarin gwiwa, sannan abu nagaba agaskiya wannan labarin tafiya ce mai nisan zango nasan kuma bazaku gaji ba zaku bani had'in kai sannan kai tsaye bazance budurwa karanta min book ba inkin so ki karanta amma karki zarge ni duk abunda yabiyo baya wannan littafi matan aure yadace su karanta domin tabbas zasu k'aro da abubuwa masu muhimmanci sosai y'an mata inai muku warning baruwa na inkin san sha'awar ki na saurin tashi is better ma karki karanta, ba batsa zan rubuta ba amma zanyi amfani da many'an many'an kalmomi aciki wanda insha Allah zanyi k'ok'ari naga basu zo a batsa ba, bance dole saikin karanta min book ba saboda wallahi duk wacce tazage ni narantse da Allah saina zage ta dan haka kowa yaja girman sa baruwa na da kowa ban gayyato kowa ba balle mutun yace na mai dole tom fatan nasara masoya na kai harma da ma'kiya na 🤣 ina gaishe da kowa da kowa😂🥰_

        *DEDICATION*
*All Nigerian soldiers may Allah bless them, ya Allah keep all of them from the enemy ya rahmanir raheem ya maliki yaumiddin ya Allah*

      *SPECIAL GIFT TO*
*Commend all soldiers wife😭 wanda suka rasa mazajen su afilin daga Allah yabamu ha'kuri da juriyar rashi🤲🏻*

*Praise be to Allah, Lord of the world, praise be to Allah who created men and empower him with knowledge, peace and blessing of Allah be upon beloved our prophet his family and his friend, the prophet Muhammad s.a.w Said wisdom is a lost property to the believer where ever it he pound it*

                *NOTE*

*_It is fiction to be like a true life story, I don't do it to curse or abuse somebody, I guess if it comes across your life story am apologizing, I don't do it because of you_*

_*IN THE NAME OF ALLAH THE MOST GRACIOUS AND THE MOST MERCIFUL, I SEEK REFUGE WITH ALLAH FROM SHAITHAN👏🏻*_

بسم الله الرحمن الرحيم

*PAGE ONE AND TWO*

*ZUMA BARRACK*
       *Monday*

Babban barrack ne daya amsa sunan sa barrack kowa kagani acikin barrack d'in harkan gaban sa yake musanmnan matan sojoji masu wanki nayi masu jida ruwa zuwa block nayi masu kai kawo domin uzurin gaban su sunayi daga chan titi ne ashimfid'e Wanda yami'ke sam'bal har zuwa office d'in many'an hafsoshin sojojin, kamar daga sama suka fara jin jiniya natashi gaba d'aya sai hankulan su yatashi suka maida duban su ga motocin dasuke tunkaro inda block blocks suke a irin wannan lokacin indai sukaji jiniya tabbas mazajen su zasu tafi operation ne, motoci goma ne ke guje bisa kwaltan kamar zasu tashi sama manya manyan jeep ne duka armyn green glass d'in su ma duka tinted windows ne hakan yasa baka isa kaga naciki ba saidai shi yaganka,

Ahankali motocin suka fara sauka daga kwaltan suka shiga wani 'karamin layi wanda shima akwai kwalta a shimfid'e many'an block's ne agaba d'aya layin domin daga wani block d'in zuwa wani block d'in da akwai tazara kuma duka two stairs ne da alamu dai 'bangaren many'an sojoji ne duba da yanda tundaga farkon layin har 'karshen sa sojoji ne atsaye da bindigogi kowanne ka kalla fuskan nan babu sau'ki sai zare idanu suke kamar suci babu lol🤣

Daga gefen wani gida duka motocin sukai parking d'aya bayan d'aya sojojin suka fara futowa suna nufan wata moto dake tsakiya duka 'kamewa sukai kamar gawar waki wani daga cikin sojojin ne ya bud'e masa kofar jeef d'in gamida saramai sannan shima ya'kame, ahankali yasakko da kafarsa dake cikin black combos na sojoji ya kai kusan minti uku kafin ya fito gaba d'aya, masha Allah ubangiji yayi halittarsa anan matashin saurayi ne wanda bazai wuce 25 years  ba  sanye cikin kakin sojoji wanda sukai masifar amsar jikinsa farine  tas  dogo mai murd'ad'an jiki  yanada 'kira 'karfafan maza da fafad'an 'kirji  kyakyawane  ajin k'arshe gashin kansa  luf luf  akwance kalan na fulani siririn sajen shi ba'ki sidd'ik da alamu yana samun kulawa yanada manyan idanu  musu mutikar haske  da d'aukan hankali  cikin tafiya irinta jaruman sojoji yanufa wani gida da already an bud'e mai gate d'in kasantuwar sauri suke yace ayi parking awaje  babban gida ne da yakasance stairs biyu yanada fad'i sosai sai wata rumfa daga gefe dasuke aje motoci ahankali yakama handle d'in palourn yashiga da sallama abakin shi wata matace dattijiya dasuke kama sosai takalle shi gamida amsan sallmar tana fad'in
"Hope lafiya dai"
Baki yad'an turo yana jan tsaki yace "Momma fisabilillah wai Kwara zan tafi yanzu"
Da murmushi afuskan ta tace "masha Allah hakan yayi Allah yatsare yatai maka"
Baki yad'an tab'e yami'ke yahaura stairs d'in aranshi yace "Nasan sabo da Ester  kikeso nabar arewa amma KO ina can d'in hakan bazai hana inji dad'i naba" da wannan tunanin yad'auki ATM card d'in da duk wani abun bu'katan shi yafito hannun shi ri'ke da brief case yasake ma Momma sallama itakuma tasa mai albarka yafito aka bud'e mai moto driver yaja dake already sun juya motocin haka suka d'auki hanya sai Kwarai.

******

_*MAK'ARFI*_

*SHEHU IDRIS COLLEGE OF EDUCATION*

Sanye suke da fararen kaya harda face mask daya hana ni ganin fuskokin su amma kallo d'aya nai musu nagane suna da kyau ba laifi su biyu ne suna tafiya da alama daga lab suke KO class gaba d'ayan su cikin damuwa suke d'ayar ne takalli y'ar uwar tata tace
"Sister yanzu yazanyi da cikin nan KO ahaka zan koma gida?" Daga yanda take maganar zaka fahimta tana cikin matsanan ciyar damuwa, ahankali d'ayar tadafa ta jikin ta amugun sanyaye tace "Haulat kinyi sakaci why zaki bari har wani abu yashiga tsakanin da namiji alhalin nagaya miki kiyi taka tsantsan iyaka romance ke kinje yajaki da dad'in baki yanzu wa gari ya waya ke KO shi?"
Hawayen da ya silalo afuskar wacce aka kira da Haulat tashare daidai nan suka shigo hostel d'akin su suka nufa suka zauna zugun zugun kafun Haulat cikin kuka sosai tace "Wallahi muddun na koma gida gobe da cikin nan Maama saita kashe ni akullun cewa take tabani amanar kaina naji tsoron Allah amma kash nakasa ri'ke amanar ya Allah save me" tafad'a tana fad'awa jikin d'ayar,
Itama hawaye ne fall fuskar ta tace "Tabbas kinyi kuskuren mallaka ma Aliyu kanki yanzu gashi KO wayar mu ma baya son d'agawa yaci moriyar ganga yayada kauron ta rud'in soyayya yaja miki"
Cikin fushi tad'an d'aga ta tace "Haba Dija *WAYE SANADI!?* cikin nida ke kece fa kikai ta zigani kikace kome yake so nabashi and kuma nabashi saiki zo kina d'aura laifi akaina haba dan Allah"
Baki Dija tad'an tab'e tace "yo mikike so nace miki yanzu bayan saida nagarga d'eki akan karki yarda ki ware mai k'afa balle yad'ura miki ciki ni yanzu ba wannan ba kitashi muje Zariya yanzu musamu private hospital azubar da cikin nan idan bahaka ba nikam ba ruwa nan kinsan da wuri za'a zo d'auka na eheee"
Hawayen fuskan ta tashare cike da nadama tami'ke tashiga toilet,
Da wata shegiyar harara tabita aranta tana raya "banza dak'ik'iya kawai mu tafi naci kud'in ki ba cikin da za'a zubar komai kece kan gaba a school d'in nan tabbas sainai sanadiyyar da aka kore ki daga school d'in har gidan naku" tsaki taja tana sake yin fuskar damuwa aranta kuwa fal farin ciki ne tana ganin burinta yakusa cika.

*****
*KANO*

*AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT*

Agogon dake d'aure atsintsiyar hannun shi yakalla karo na barka tai yana jan tsaki kafun yajingina da motar dake tsaye a gefen ta black benz sanye yake da ash jeams sai farar t-shirt da akai rubutu da ash d'in penti akasa giant  chocolate color ne kyakkyawan gaske domin da gani d'an hutu ne sabida yanda fatar shi take ta glowing yana da siriri hanci da many'an idanu sai d'an k'aramin pinkish mouth d'in shi dayake k'ara mai kyau sosai matashi ne mai jini ajika wanda bazai wuce 22years ba, hannun shi yakai saman gashin kanshi yana shafawa akaro na bar katai yanajin wani ba'kin ciki gani yake kamar inyatafi yayi ban kwana da dukkanin farin cikin sa wayar ya'kara kira awannan karon ma not respond kira yakuma yi sai yaga busy alamun anjefa shi a black list kenan wani iri yakeji kamar yaje mak'arfin amma kuma time d'in tashin shi ajirgi yakusa dan haka dole yajuya jin har anfara kiran su rungume Mom d'in shi yayi yamata peck agoshi sannan yashafa kan wata yarinya wacce bazata haura sixteen years ba murmushi tamai tace "Uncle safe trip Allah yatsare yabaka abunda kaje nema"
Da amin suka amsa shida Mom d'in shi sannan yajuya yana weaving d'in su har yashige cikin jirgin,
Suna tsaye kowa yagama shiga jirgin har k'ofar takulle saida sukaga tashin jirgin sannan suka juya suka shiga motar driver yaja sukai gida..........✍🏻

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONEWhere stories live. Discover now