FORTY THREE AND FORTY FOUR

324 23 11
                                    

🌺🌺🌺🌺
*WAYE SANADI!?*🪦🪦

             *By*
*Ummu Sumayya*
*Wattpad #Bintubaby*

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITATTAFAN HAUSA TV_

http://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*Muhimmiyar sanarwa gareku masu bibiyar WAYE SANADI!?*

_*Dafari dazan fara rubuta wannan littafi bance paid book bane kuma bance zaikoma paid ba dan kyauta nayi niyyar yinsa har sanarwa nasa ashafin farko but ba zato ba tsammani tun satin daya gaba ta aketa kirana akan anason ayi payment na waye sanadi yayinda nashare batun kwatsam shekaran jiya aka kirani akan cewar ana fa saida min littafi inda har screen shot akaimin awani group abunda yamatu'kar d'aure min kai yaban mamaki😭 duk wanda ke saida min littafi bada sanina ba Allah ya isa ban yafe ba ga wad'anda suke siye kuma kafun kutura kud'in ku yakamata ku tuntu'beni firstly numbers dina guda biyu ne nake WhatsApp dasu mtn da airtel 07017296839 da kuma 07042682333 idan har kukaga sa'bani wad'annan numbers d'in bani bace kam y'an dan fara ne dan haka akiyaye Allah yakyauta gaba WAYE SANADI FREE BOOK ne kuma bazan ta'ba sanja ra'ayi akan hakan ba yanzu aka fara wasan dan yanzu ne muka shiga cikin labarin ka'en da na'en sai agayara zama adinga sambada min comments acigaba da share fisabilillah Ummu Sumayya heart you all💃🏼😍*

*FORTY THREE AND FORTY FOUR*

Suna shigowada akwatuna suna jerawa saida suka jera shida shida waje biyu dozin d'aya kenan guda sha biyu, kallo d'aya tamusu taduk'ar da kanta zuciyar ta na wani irin bugawa kamar amafarki taji muryan Aunty Salma na sallama kafun kuma tarangad'a gud'a dan sunjima da zuwa dama sun tsaya ne awajen Mommaa sunci abinci sannan tace suje suga kaya, dawani irin sauri tad'ago kawai sai ganin su tayi Inna Hauwa'u Ina Halima Halisa Aunty Jidda da wani irin gudu tami'ke ta'karisa bakin k'ofar tanufa Salma zata rungume ta Jidda tace "ke baki da hankali ne bakiga abunda take d'auke dashiba ne eye"
Ina Haulat bataji taba saida ta k'ank'ame ta tana fashewa da wani irin kuka,
Murmushi kawai Aunty Salma take tana d'an bubbuga bayanta kafun cikin rad'a tace "Wai meye haka bakiyi farin cikin ganin mu bane mu koma"
Dasauri ta girgiza kanta tana calming kanta tace "nayi mana yaxakice haka"
Hannun ta takama suka k'arisa cikin d'akin inda Inna Halima su harsun k'arisa wajen kayan sunata dadd'a gawa yayinda Aunty jiddake bubbud'e akwatin sunayi suna shewa gasu Ammi agefe domin Mommaa cewa tayi su tsaya idan sun gama dubawa abunda bai musu ba KO babu sufad'a musu sai anemo hakan kuwa ya mugun ba'kanta ran Ammi hartana dana sanin zuwa,
Zama sukayi gefen gado Aunty Salma tace "please and please kidaina kuka if not wallahi juyawa zamuyi"
Murmushi tayi tana goge hawayen ta tace "ya Mamana take ina nan inata missing d'in ta wallahi itama nasan tayi missing d'ina ko?"
Dariya Salma tayi kafun tace "da sauran ki y'an mata kam bari naga kayan nan kafun nan nabaki amsar tambayar ki" tafad'a tana k'arisawa wajen akwatunan dakowa ke son barka da Allah sanya alkairi cikin auren yayin da Ammi keta tsine ma auran cikin ranta,
Saida suka gama sannan sukace komai yayi tukwici Aunty Salma tabasu naira dubu hamsin awula'kance Ammi ta amsa tace "saikace baku yaba ba"
Aunty Salma ne tamata wani irin kallo kafun tace "yaba kyauta tukwici shine nabaki ai dabamu yaba ba sisi munbar badawa"
Wata mata ce awad'anda suka shigo tace "ai dubu Hamsun dai ba laifi Allah sanya alkairi yakawo zuri'a dayyiba"
Da amin duk suka amsa banda Ammi data wani futa fuuu sauran biyun sukai musu sallama suka futa,
Baki Haulat ta tab'e aranta tace aniyar ki tabiki insha Allah na miki fintinkau nikam.
Bayan anyi sallar magrib ne suna zaune sunata fira cike da nishad'i Haulat na kwance jikin Inna Hauwa advice suke ta k'ara mata akan zantakewar aure knocking akayi suka bada izinin shigowa maid ce da wata had'add'iyar mata tad'an rusuna tana kallon Haulat tace "Madam Mommaa ne ta toru ni tace ashirya ki akwai mother's day da za'ai k'arfe 8:00 kuma tace duk sauran ba'kin su shirya"
Ta'karisa maganar tana kallon su,
Da to suka amsa tami'ke tafita tabar mai yin make up azaune,
Mik'ewa Haulat tayi tafad'a toilet da sauri tayi wanka dan shaf tamanta don Mommaa tasanar mata da mother's day d'in tana fitowa ta zauna akan kujerar mirro aka fara tsantsara mata make up kusan thirty minutes suka d'auka dan su Aunty Salma ma sun riga da sun tafi su biyu kawai suka rage ad'akin bayan tagama mata make up d'in ne tace "kai masha Allah gaskiya kinyi kyau" tafad'a tana ciro wani ubansu boyel daya gaji da had'uwa tabata tashirya cikin sauri d'aurin d'an kwali tamata daya sake fito da kwalliyar ta wani irin murmushi tasaki ganin yanda tayi d'as abunta, ita kanta artie's d'in tayaba k'yan datayi hutuna tafara mata da wayarta tana ta kod'a ta itadai tayi tsit batai magana ba sai murmushin da take tayi sallama tamata tafuta tabarta ad'akin,
Tsayawa tayi agaban mirron tana ta jujjuyawa kamar amafarki tahango shi acikin mirro sanye da wando da kad'an yawuce gwiwarsa sai riga ta shan iska dan tana hango k'irjin shi da gashin daya kwanta luf luf ba'ki sid'ik kallon ta yake kamar ranar yafara ganin ta dasauri taduk'ar dakai tana addu'a cikin ranta,
Takalmin shi yaxo d'auka dan baiyi tunanin tana ciki ba sabida yasan da mother's day d'in tun idanun shi suka sauka akanta gaba d'aya tsigar jikin shi tawani mi'ke yarrrrr idanu yalumshe kawai yana ganin yanda take d'an jujjuyawa kamar da gayya bud'esu yayi tas yacigaba da kallon ta ganin taganshine yasa ya'karisa d'akin har bakin mirror still idanun shi na yawo asassan jikin ta k'amshin dake tashi ajikin ta yanema zauta shi yana zuwa bayanta yarungume ta tabaya yawani saki ajiyar zuciya yana shinshina wuyanta hannun shi saman cikin ta yana dad'a mannata ajikin shi shinshina ta yake kamar maye while idanun shi alumshe murya can k'asan makoshi yace "you're looking good my wife" yafad'a yana sakin wani irin nishi kamar wanda yayi tseren gudu,
Tunda taji hannun shi a waist d'in ta tafara daburcewa dan gaba d'aya itama kant ga'ba take magun gunan da aka bata ba'karamin tsumata sukayiba sake jingina tayi ajikin shi idanun ta arufe unexpected taji yawani juyo da ita bud'e idanun ta tayi tana kallon lumsassun idanun shi dasuke arufe bud'e idanun yayi karaf idanun suka sar'ke dana juna d'an rankofowa yayi yace "open your mouth"
Ba musu tawani bud'e mai bakin yawani tura halshen shi tacafke tana wani irin tsotsan shi kamar tasamu sweet me shegen dad'i shima nata yakama yana tsotsa still idanun su asark'e while hannun shi nakan ass d'inta yana shafawa wani irin narkemai take k'ara yi gaba d'aya tama mance mezatayi ganin tsayuwa na neman gagarar tane yasa yawani d'agata yad'aura kan mirron sukaci gaba da kissing juna kamar zasu cinye junan su yana k'ok'arin zuge zif d'in rigar tane yaji gyaran murya abayan su dasauri yad'an saketa yana juyowa Mommaa yagani kanshi yad'an fara sosawa zaiyi magana ta b'alla mai wata uwar harara tace "futa"
Baki yasake bud'ewa zaiyi magana tace "I said out" suf suf yafuta yana sosa kai dan yaji kunya sosai kafad'a yad'aga yana d'an murmushi tuna ba haram ya aikata ba.
Haulat kuwa gaba d'aya jitake inama k'asa ta tsage tashige komai ya kwance mata futan Mommaa kawai taji dasauri tajuya jikin mirro taga gaba d'aya janbakin fuskar ta babushi ga d'aurin dankwalin duk ya sukurkuce knocking taji dasauri tajuya dan tasan ba Mommaa bane izini tabada mai make up ne tadawo batare data mata magana ba tace tazauna zama tayi tad'an gyaggyara ta sannan takamo hannun ta suka sauko,
Harabar gidan tacika soaai k'amshi ne me dad'i da cool music ke tashi kawai awajen wata katafariyar runfa da tasha decorations suka nufa zaunar da ita tayi sannan tajuya,
Du'kar dakai kawai Haulat tayi tanajin Mommaa ta amsa microphone tana mata maraba da zuwa,
Sosai mother's day d'in ya'kayatar yanda yakamata anci ansha anraba souvenir mai hoton amarya da angonta dasukai cas kamar kasace su, wanda ita Haulat tarasa inda aka samu hoton nata ma k'arfe tara daidai suka tashi inda masu tafiya gida suka tafi wad'anda zasu kwana nan suka shiga cikin gidan kowa na yaba k'yan matar Hamza,
Bayan takoma d'akin da take zaune tunda tazo gidan tasamu Aunty Salma dasu Inna Hauwa'u anata fira toilet tashiga tayi wanka sannan tafito tazauna cikin su tana shafa humra dasata yazamar mata jiki, tana jin yanda suke k'oda akwatinan ta da yaba ma surukarta shiru tayi tanajin su wayar tane tad'an kawo haske alamun kira dan tana silent ne d'an satan kallon su tayi saita mi'ke tashiga toilet har kiran yakatse wani kiran ne yasake shigowa kamar bazata d'aga ba saikuma tad'aga kafun tayi magana taji muryan shi in a low voice yace "Baby kije wajen Mommaa tabaki coffee ki kawo min dakanki dan Allah"
D'an shiru tayi saikuma tace "to" tana katse kiran da tunanin dawani idanu zata kalla Mommaa dan tun abun d'azun basu had'u ido da ido ba kuma ita yanzu ma tsoron shi takeji kam da'kyar tafuta tabar toilet d'in takoma taci gaba da firar ta hankalin ta duk yana garesa har suka kwanta saida ta tabbatar barcin su yayi nisa sannan tami'ke tsam tad'aura vail kan kayan barcin ta tafuta kitchen tasauka babu kowa sai fright dake ta aiki kettle takunna tad'auko mug da spoon d'an dube dube tafara na neman coffee powder.
Shiko Hamza tunda yakwanta ciwon ciki dana mara suka sakoshi gaba daddafe yayi sallar isha'eh yakoma yakwanta yana ri'ke marar shi datai mai mugun tauri tana mai ciwo juyi kawai yake zufa duk taji'ka shi duk da sanyin air condition d'in dake tashi kuwa wayar shi yalalubo da'kyar yakira Haulat dan yasan sun tashi awajen taron dan bayajin hayaniyar su gidan yayi tsit da alamun kowa ya kawwami shiru yanata zuba idanu bai gantaba sai ranshi yadinga suya ga ciwo na damun shi alhalin yanada mata amma shida mara mata kusan d'aya ajiyar zuciya yadinga saukewa ajjajere kamar amafarki yaji anbud'e k'ofa d'agowa yayi da'kyar kallo d'aya yamata yad'an d'auke kanshi yana share zufar fuskan shi da hannu,
Asanyaye ta'karaso cikin room d'in ta aje mai mug d'in coffee d'in kan side drawer  tace "gashi"
Banza yamata cike da takaici saida tasake maimaita maganar ta sannan yace "kije da abunki bana so"
Marairaicewa tayi tace "dan Allah kayi ha'kuri kaga akwai mutane ad'akin ne shiyasa"
Wani kallo ya watsa mata yace "mutane har sun fini Haulat anya kina sona kuwa kodai yaudarar kaina nake?"
Jikin tane yayi wani mugun sanyi taduk'a kan k'afafun ta tace "kayi ha'kuri"
Kallon ta yayi sama da k'asa yana sake kimshe fuska yace "hmm kije kawai tunda mutane sunfi miki aljannar ki"
"Dan girman Allah kayi ha'kuri ban sakewa" tafad'a tana calming kanta dan sosai zuciyar ta takarye k'iris takejira tafashe da kuka,
Kauda kanshi yayi cike da takaici kafun yami'ke yafad'a toilet wanka yayi da ruwa mai d'an zafi zafi sabida yanayin dayake ciki tewol kawai yad'auro a k'ugun shi inda yabarta nan yasame ta batare daya damu da itaba yacire tewol d'in yana goge jikin shi dashi kafun yawice tagaban ta yad'auki boxer da singlet yasaka yahaye gado batare daya kalli coffee d'in ba wayarsa yad'auka yana dannawa amma kuma hankalin shi na wajen ta ji yake kamar yaje ya lalashe ta amma yarabu da ita so yake kawai tagane baya son abunda take mai sabida inyazama halinta wuya zaisha.
Gaba d'aya saitaji ta muzanta amma kuma tana tsoron tafiya duk abunda yake kanta a'kasa yake ganin datayi yakwanta ne yasa tagoge hawayen daya silalo mata tami'ke tafuta ad'akin tana toshe bakin ta a corridor tatsaya taci kukanta kamun tanufa d'aki da Aunty Salma sukai clash tafito daga toilet babu wanda yatanka ma wani suka kwanta,
Washe gari takama yinin biki tun da safe bayan tayi wanka me make up tamata kwalliya na kece raini aka shirya ta cikin wani ubansu lace aka feshe ta da turaruka different design Mommaa ne tafuta da ita tana nuna ma many'an k'awayen ta kowa sai yabata yake yayinda mai video coverage yake ta d'aukan su gaba d'aya yau fuskan Haulat ba walwala sai d'an abunda ba'a rasaba amma duk dahaka tayi kyau na musamman after like twenty minutes akasake samata wani shadda aka gyara mata make up,
haka akaita canza mata kayan har yamma Mommaa dakanta tasake had'a mata ruwa mai cike da turaruka da Hajiya Falmata tabata tace taje tayi, akunyace tashiga bayin tajima acikin jacuzzi dan k'amshin ruwan ba'karamin dad'i yake mata ba gefe d'aya kuma tunanin Hamza ya addabe ta lumshe idanu tayi data tuna nanda wasu awoyi suna tare kamar yanda akasanar da ita ana tashi solder parade direct gidan shi za'a kaita ajiyar zuciya tasauke kamun tafara cud'a kanta tanajin yau wankan na musamman ne dan zata bashi mamaki sosai zata cire tsoro ta rungumi mijinta tafaranta mai rai,
Bayan tafuto daga bayin ne tayi sallar isha'eh akasake yimata light make up wasu kaya tabata tafuta tace tashirya, kulle k'ofar tayi sannan tabud'e ledar wani irin zaro idanu tayi ganin kakin sojoji harda takalmi d'an jujjuyawa tayi tana d'aga su d'aya bayan d'aya harda halp vest da short naker murmushi tasaki kafun tafara shiryawa sosai kayan suka amshe ta takalmin tad'aura tsaf sannan tatsaya tana kallon kanta ita kanta tasan tayi ba k'arya kamar soja, shiru taji gidan yayi alamun duk antafi wajen dinner parade d'in kenan, zama tayi  abakin bed saiga text d'in Hamza yace tasame shi awaje kallon kanta tayi saikuma tad'aura hulan asaman gashinta dayake d'aure ahankali tabud'e k'ofar zuciyar ta nawani irin bugawa tana fitowa tafara jin magana k'asa k'asa harta fara tafiya tad'an dakata jin ance "Haulat d'in me ita d'in banza ita d'in wofi aikamar kin auri hamza kin gama kima daina kuka da gashi har uwar sa zasu gane kuransu ki kwantar da hankalin ki komai zai zo asannu"
D'akin datakejin magana takalla zuciyar ta na wani irin lugude ta'karisa wajen dan bata fahimta komai ba amaganan maganar wata taji tanacewa "yo banda ke gaula ce Dija ina kince tare kukayi karatu kuma kinsan irin lalatar datayi da tsohon saurayin ta har aka kore ta sanadin zubar da cikin shefe aida tini kin FASA kwan awajen hamza tunda ita Mommaa ta'ki response d'in maganar balle taba abun muhimman ci auren ki da hamza kuwa kamar anyi angama kidaina kuka kinji"
Gaba d'aya jikinta yad'auki kyarma lokacin data hangi Dija azaune tana sharar kwallar ga wad'anda Mommaa tagabatar mata dasu d'aya amatsayin k'anwar Baban hamza marigayi d'aya matar Yayan sa wacce kuma taga sunfi kama da Hamza kenan Dija causing sister Hamza ne ya ilahil alameen wani irin jiri ne yake shirin kada ita tad'anyi baya zata fad'i taji tafad'a jikin wani d'ago idanu tayi idanun su suka sark'e zuciyar ta tabuga dawani irin k'arfi "Aliyu" tafad'a cikin ranta wani irin murmushi yasakin mata yana k'ok'arin ta'ba fuskan ta tawani fisge jikin ta daga garesa ta hankad'a shi yayi taga taga zai fad'i sai yajingina da banko yana watsa mata wani irin shu'umin kallo, tajuya da xummar tafiya gaba d'aya kwakwalwarta ta hargitse bayyanar wad'annan mutane biyun arayuwar ta ba'karamin tashin hankali bane shin meke shirin faruwa da itane d'agowar da zatayi sukai ido hud'u da Hamza gaba d'aya saita gigice ganin yanayin sa murya na makyarkyata tace...............✍🏽

*Allow me to enjoy my self👯🏻‍♀️ yazata kaya kenan nidai bance komai ba kam koya zata kasance ga Dija ga Aliyu ga kuma Hamza rikita rikita kenan Haulat kinga taskur rayuwa kam🙆🏽‍♀️🤦🏽‍♀️ ruwan comments da vote kawai zaisa kujini soon insha Allah if not sainan da talata KO laraba👩🏽‍🦯💃🏼*

#Follow me
#Vote
#Comments
#and share it fisabilillah🙏🏽

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon