GAMON JINI 102

189 14 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
(Dashen Allah bana mutum ba,together we stand and succeed)

1⃣0⃣2⃣

A mota ma gaba daya bata da walwala,tafiya kawai take har ta qarasa qofar gidan mummy,horn tayi mai gadi ya leqo ya ganta,sannan ya bude mata gate ta shiga da motar ta,fitowa tayi suka gaisa da mai gadin ta shiga ciki,gidan tsit,bakowa a parlon ta hau qwalla mata kira

"Umma ta ! Umma ta!! Umma ta!!!"

Mummy da take kitchen ta jiyo muryar tilon 'yar tata,wanke hannunta tayi ta fito

"Fadee,sai yanxu kika qaraso ke da kika ce tun dazu kin baro gida,abba ma yana ta jiran qarasowar taki har ya fita"

Qarasawa tayi ta rungume umman tata tana jin kewar ta sosai,kitchen din suka koma gaba daya ta kama mata aikin,suna cikin aikin ne fadee take fada mata halin da malam shafi'u yake ciki,har zuwa kudin da ta basu da kuma ce musu da tayi zasu dawo tare,umma ta tausaya musu sosai musamman kabeer,jinjina kai tayi tace

"Kin kyauta sosae fadee,iyayenki ne kuma naji dadin abinda kikai musu,amma maganar zuwa bazanje ba,ni dama na yafe masa tun tuni,kuma duk abinda kike ganin zakiyi musu na kyautatawa ki tambaye ni zan baki kudi sai kiyi musu"

Fadeelah bata ji dadin abinda umman tata ta fada ba,amma kuma tana da gaskiya don yanxu tana da aure,bata da hadi dasu,a qoqarinta na kare martabar aurenta,amma tasan in tace zataje dubo yayan tsohon mijinta,ai abban ba zai hana ba,marairaice fuska tayi tace

"Haba umma,ya kamata kije ki duba shi ko dan ni,dangina ne,nasan Abba bazai hana ki ba,plss"

"Toh,bara abban ya dawo"

Hira suka ci gaba har suka gama girkin,suna fitowa daga kitchen ta shiga wanka ta canza kaya,tare ta zuba musu abincin,wani irin farin ciki suke ji a ransu ganin yadda rayuwa ta juya musu gaba daya,suna cikin kwanciyar hankali sosai,bayan sun gama cin abincin ne umma tayi wa fadeelah nasiha sosai akan zamantakewar aure,umma ce tace wa fadeelah

"Fadee,tashi kiyi haramar tafiya kada yamma tayi,kinga ke kadai kika zo"

"Toh umma"

Miqewa tayi ta zari mayafinta ta yi rolling kamar yadda tazo dashi,muqullin motar ta dauka,ummanta ta rako ta har bakin mota,suna tsaye aka bude gate wata mota ta shigo,bin motar tayi da kallo,shima yana kallonsu a inda suke tsaye har yayi parking,fitowa yayi yasa wani yadi kalar coffee brown an masa aiki da ratsin milk colour,hularshi ma hka kalarta yake,yasa milk din takalmi,kallo daya tai masa ta dauke kai,yayi mata matuqar kyau da kwarjini,har inda suke ya qaraso,mummy tana ta fara'ar ganinshi da alama ya saba zuwa,kallon mamaki take musu har ya durqusa ya gaishe da mummy,itama fadeelan gaishe shi tayi,ya amsa mata ya shiga ciki,kudi mummy ta bata ta siya kayan abinci ta kai gidan kawunta,godiya tai mata ta shiga mota mummy ta juya,tada motar tayi ta fita,tana fita qofar gidan ta gangara tayi parking,wayarta ta dauko ta kira number shi,a lokacin yana dining din ummanta yana cin abincin da suka dafa,ganin wayarta yasa ya katse sannan ya kirata,daga wayar tayi ta sanar dashi zata biya gidan kawunta,tunda dama gidan ummanta kadai ta tambaye shi daxu,izini ya bata sannan ta kashe wayar.

Shagon data hanga daga inda take ta qarasa ta siya musu buhun shinkafa biyu,taliya da macaroni carton hudu,mai jarka biyu da manja,da duk wasu kayan abinci da zasu buqata,a booth aka loda mata kayan ta biya su kudin ta ja motarta sai gidan malam shafi'u,a lokacin kabeer baya nan,rabin kayan ta sauke anan,ta qarasa gidan kabeer ma ta sauke sauran,anan ta sameshi a gida,kudi ta bada 100k akan ya bawa malam shafi'u rabin kudin shima ya riqe rabi,godiya yayi mata yai ta sa mata albarka sannan ta wuce gida.

tana yin parking ta fito,yana tsaye a bakin part din su abdoul,da farin ciki ta nufi inda yake tsaye,murmushi ya sakar mata

"Gimbiya",yace

Itama murmushin ta mayar masa ta qarasa "yaya mubarakh,don't tell me kaxo for my graduation party"

Gyada mata kai yayi tace "wow! U are very special yaya mubarakh"

"Gimbiya yaushe kikai baki haka"

"Kai yaya mubarakh,ina aunty hannan"

"Tana abuja"

"Ayyah me yasa bata zo ba"

"Jst kidding,tana ciki"

"Wow amma naji dadi sosai"

Tare suka shiga gidan kowa na parlor sun cika gidan,qunshi ake yi wa khadija bayan an gama wa rukhy,hannan kuwa tana zaune him da tsohon ciki,dama mommah tunda taga cikin tace bazata koma abuja ba sai ta haihu,mubarakh bai so ba amma hka ya haqura,inda hannan take ta kalla,qarasawa tayi "aunty hannan an zo lafiya"

"Lafiya lau amarya" kunya taji ta wuce inda su rukhy suke,ana musu lalle don ita ba'ai mata ba tunda zatai exam gobe,sai ta dawo za'ai mata baqi kawai saboda ba tym don ma ta safe ce exam din.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Abdoul da ta baro a gidan mummy bayan ya gama cin abinci ya zauna ya ke ta zuba mata surutu,suna ta hira wacce a gidan su ma bayi yake ba,amma ita yana sakewa da ita sosai,har mantawa yake da cewar surikarsa ce kawai yana daukar ta a qanwar dad dinshi kuma qawar mommah,sai bayan maghrib ya bar gidan,gida ya dawo,bai shiga cikin gidan ba ma ya wuce dakinshi,mubarakh ya tadda a zaune yana kallo,shima zama yayi mubarakh yace

"Daga ina??"

"Gidan mummy naje"

"Ok,tana lafiya??"

"Lafiya lau"

"Da ka fada min da zaka tafi ai da munje tare,kasan tun lokacin bikin ban qara dawowa ba"

"Kana nan kna rainon ciki ina zaka??" Ya fada yana er dariya

"Kar ka damu,yana nan xuwa kanka"

Dariya sukai dukkansu,suna wajen har aka kira sallah,masallaci suka je suka dawo,mubarakh cikin gida ya tafi wajen matarshi shi kuma ya wuce daki,waya ya dauka ya kirata,sun dan taba hira ta ce mai zatai bacci,don gobe da safe ne zata je exam,sallama sukayi ta kwanta bacci

*asuba ta gari*

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now