GAMON JINI 100

272 12 16
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
(Dashen Allah bana mutum ba,together we stand and succeed)

_Masoyan littafin gamon jini naga coments dinku,kuma naji dadi sosai,Allah yabar zumunci,i heart u oll_ 🤝🏻

1⃣0⃣0⃣

Shigowarta kenan gidan ta dawo daga exam,tana shiga daki ta tadda rukhy taci uban kwalliya tayi matuqar kyau,sakin baki tayi tana kallon ta

"Ke kuma ina zaki da wannan tsakar ranar??"

"Gidan mummy zanje wlhy,kuma ba yau zan dawo ba,nayi missing dinta da yawa"

"Amma shine bazaki jirani na dawo nima na shirya mu tafi tare ba"

"Chaab,exam fah kikeyi,don ma dai..."

"Qarasa mana"

"cewa zanyi don ma dai exam din ta masu gata ce,tunda ba karatu kuke ba"

"Wlhy kuwa don wani lokacin ma ko questions din bana karantawa,iya kaci a bani numbers nayi compairing na juye"

Tuntsurewa sukayi da dariya rukhy tace

"Toh Allah ya shirya"

Hade rai fadeelah tayi tace

"Ke wai me kike nufi,kwana zakije kiyi,karatun kuma wa zai min??"

"Ke da kika kusa candy,kuma ma wlhy kin iya,koni yanxu sai in zauna ki koyar dani,kina ganin term daya mukai a class daya amma ni tunda nake bn taba daukar ta 2 ba,ke kuwa a term daya kika baro ta"

Duka ta daka mata,ta fice da sauri tana cewa

"Ko saqon gaisuwa babu wajen mummyn tawa"murmushi fadeelah tayi tace "ki gaisheta,amma pls ki dawo yau"

"Ai wannan ne kuma baki isa ba,ki kira mijinki ya taya ki kwana" toilet kawai ta shige ba tare da ta qara ce mata komai ba,ita kuma wucewa tayi dakin mommah tayi mata sallama ta fita driver ya kaita.

Alwala ta dauro tayi sallar azahar,fitowa tayi ta shiga dakin mommah,tana ganinta ta saki fara'a

"Daughter kin dawo??"

Itama murmushin tayi ta qaraso kusa da ita ta tsugunna ta gaisheta,sai da ta amsa sannan ta tashi ta zauna kan gadon mommah

"Ya exams din"

"Alhadulillah"

"Allah ya bada sa'ah,a ci gaba da dagewa "

"In shaa Allah mommah"

Kinci abinc?" girgiza kai tayi

"Toh tashi kije kici abinci daughter" toh tace ta moqe ta fita,dining ta tafi ta zauna ta zuba abincin taci,sai da ta qoshi sannan ta miqe,daki ta koma,ta dauki wasu keys ta zari hijabi tai waje,part din yaya abdoul naga ta nufa,muqulli tasa ta bude ta shiga,hijabin jikinta ta cire,ta fara mai wankin bandaki,da yake bandakin ba wani girma ne dashi ba nan da nan ta gama,dakin ta fara gyarawa,tana hada mai kayan wanki,sai da ta gama hada ko wane kaya a mazauninshi sannan ta fara shara,tana cikin sharar ne taxo sharo wajen gefen gadon,ta dan zira tsintsiyar ta cikin qarqashin gadon,tsintsiyar ta taho da biro,daukan biron tayi ta bude bed side drawern dake gefenta tasa aciki,har zata rufe taga wani abu da ya dauki hankalinta,bata san ko mene ba,hannu tasa ta dauko sai alokacin ta gane cewar diary ne,ji tai tana son ganin meye a ciki,budewa ta farayi,page din farko taga

GAMON JINIWhere stories live. Discover now