GAMON JINI 70 to 75

204 14 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

7⃣0⃣ to 7⃣5⃣

Su mommah ne suka shiga tare da fadeelah da ummanta,gidan a cike yake sosai da mutane don har baqin mommah sun para zuwa,hannan da har yanxu tana daki tana sana'ar kuka,dakin da take mommah ta nupa tana riqe da hannun fadeelah,tana shiga ta tadda ita a zaune akan gado ta hada kai gwiwa tana ta kuka,ganin haka yasa mommah qarasowa da dan saurin ta

"Subhanallahi,kuka hannan?? Bakiji maganata ba kenan,tashi maza ki yi wanka,yanzu zan turo mai lalle tazo tayi miki"

Kanta ta dago ta bude baki zatai magana mommah tace

"Tashi kaawai,bana son musu"

Miqewa tayi ta sauko,sai da mommah taga ta shiga toilet sanan ta juyo ta kalli fadeelah

"Zauna anan kapin ta pito azo a muku lallen"

"Toh" tace

Mommah ta pito daga dakin, wajen zubaida taje taja ta suka shiga dakin dake kusa dana su hannan

"'Yar uwa kiyi wanka ga kaya nan a cupboard ki dauki wanda yayi miki ki saka,bari naje in dawo"

Pita tayi daga ta nupi inda mami take ta rada mata magana a kunne dayake tana cikin mutane,tashi mami tayi tabi bayan mommah suka koma dakinta,suna shiga mami tace

"Me ya paru,lapiya dai??"

"Lapiya lau,abin farin ciki dai,kun kawo mana hannan kenan bazata koma libya ba don yaya ya mata aure"

Zaro ido mami tayi cikin mamakin jin maganar da mommah take tace

"Aure kuma?? Garin yaya??"

"Hmm,na manta dayan albishir din,anga zubaida pa"

Da sauri tace "A ina??"

"Ashe itace maman fadeelar da mubarakh zai aura,sai a wajen daurin aure suka gane,shine suka juya daurin auren aka daura da abdulrahman,shi kuma mubarakh aka aura masa hannan"

Guda mami ta saka cikin farin ciki tace

"Auta ta buri ya cika ta zama matar mubarakh"

"Ai yanxu ma daga wajenta nke,ta shiga wanka,amma ban fada mata an yi abin ba"

"Toh shikenan,yanxu ina zubaida??"

"Itama tana wanka"

"Toh tashi muje,ai shagali ya zama biyu,mun samu sabon ango"

"Da kuma sabuwar amarya ba" mommah ta fada suka miqe suka fita

Rukhy ce ta qaraso wajen

"Mommah mai lallen tazo"

Mommah tace "to kuje dakin ki,akwai baquwa kice a musu mai kyau na amare ita da hannan"

"Mommah wace ita??"

"Amaryar yayanki ce abdoul"

Zaro ido tayi ta qara  cewa

"Ko dai yaa mubarakh??"

"Nace miki matar abdul ce,mubarkh hannan aka aura mai,but dont tell her kiyi shiru da bakinki"

Zata qara magana mommah tai saurin cewa

"Tapi bana son surutu kije ki kaita,lokaci na qurewa"

Juyawa tayi ta tapi dakin da gudu ta shiga dakin cikin murna.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Kapin kice me maganar auren ta yada ko ina na gidan,har part din mummy (hajiya saudat) salima gigicewa tayi dajin zancen auren abdul,ta kalii mummy ta fara maganganu cikin bacin rai

"Ai laipin kine,nace ki fadawa mijinki muna soyayya da abdul,da yanxu bai aura masa wacce ko saninshi ma batai ba,dama na gane,yadda bakya son uwarshi haka bakya son na aureshi,to yanxu bana buqatar taimakon ki,kuma ki jira sai na auri abdul"

Tana gama maganar ta dauki gyalenta fuuu ta pice tabar gidan zuciyarta na quna,dadin da taji ma da akace ba yanxu matarshi zata tare ba,tana da damar da zata raba su kapin ma ta tare din tunda ance duk basu san juna ba,tana cikin wannan tunanin ne ta hau kan titi bata sani ba,mota ce ta taho da gudun gaske yana ta mata horn amma inaa,qarar ihun da ta kwalla ne ya janyo hankalin mutanen kan titin zuwa inda take

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ce kawai take fitowa daga bakin mutanen,don yadda jini yake zuba ta hancinta da bakinta,da wahala idan tana da rai,qarasawa mutanen sukai bayan wanda ya kade ta tuni ya cika wandonshi da iska,dubata sukai suka tabbatar da tana numfashi.

Daya daga cikinsu ne ya dauko mota a ka sata suka kaita asibiti don suna ganinta da khadija sosai,haakan yasa bayan sun kaita asibiti suka aika a fada a gidan,amma kapin su mummy suzo tuni rai yayi halinsa sai dai muce Allah ya jiqanta.

❣❣❣❣❣❣❣❣

A can gidansu fadeelah kuwa,duk baqin umma idan suka zo ce musu ake an tapi kai amarya da yake nesa ne,sai dai su gaggaisa suci abinci su tapi.

Dad ya kira kabeer akan maganar fadeelah,kabeer ce masa yayi ai yanxu tana qarqashin ikon mijinta ne ba su ba,dad yaji dadi sosai da maganar,saboda haka ma ko su mallam shafi'u basu san cewar fadeelan ba yanxu xata tare ba tunda tana gidan iyayen mijinta.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Abdul ne kwance a daki zazzabi mai zapi ya rufe shi,abubuwa sunwa kanshi yawa,ga son fadeelah ga auren da akayi mai,da yake mubarkh tun daxu daya pita bai dawo ba.

Mommah ce ta aiko rukhy tazo ta kirawo su,tun da suka fita a part din dad bata ga sun shigo ba,dawowa rukhy tayi ta fada mata abin da ta gani a dakin,kasancewar tasan dama bashi da lapiya kwana biyu,kwata kwata bata kawo cewar hadda damuwar auren da akayi mai ba,waya ta dauka ta kira doctor tunda anyi anyi tun daxu aje asibiti ya qi.

Mubarakh ta qara kira ta shaida mai a bar wedding dinner da za suyi xuwa gobe saboda a shirya amare,tunda abin yazo duk na gida ne da kuma zubaida itama tayi dinkunan biki

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now