GAMON JINI 90 to 95

224 12 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

9⃣0⃣ to 9⃣5⃣

Shiru sukayi ba mai mgn a cikinsu,kowa da abinda yake saqawa a ransa,ganin shirun yayi yawa ya daure yace

"A school ajinki nawa??"

"S S 2"

"Kina son komawa skul??"

Abinda taji yace ne yasa ta dago kanta don murna tana kallonshi,sai a lokacin ta tuna da wa take magana a hankali tace

"Ehh"

"Good,klas dinku daya da rukhy,ki tambayeta idan skul dinsu ta miki sai akai ki can"

"Tayi ma"

"Olryt,ki shirya gobe da safe sai muje"

"Toh,na gode"

"Ai ba sai kin gode ba,haqqina ne"

Miqewa yayi yace"pls ki dafa min tea,ki tambayi rukhy irin wanda nake so,sai ki kawo min"

Haka kawai ta tsinci kanta da rashin yi mishi musu tace "toh"

Ya fita ranshi fes,ko ba komai yau yaji muryarta,qarasawa yayi daki ya dauki wayarsa yai dialling *lil sis* rukhy ce ta daga wayar tana dakin umman fadeelah tana mata gyaran kaya

"Hello,yaya"

"Sis pls ki zo mana"

"Ina wa mummy(da yake yanxu mummy suke ce mata) aiki,bara na gama"

"Ohk,then gama sai kizo"Ya kashe wayar,jin maganar da rukhy tayi a waya yasa umma tace

"Ki tashi kije kiran yayan naki,ai an kusa gamawa"

"A'ah mummy ki bari in gama duka,ai yanxu xan gama"

Farin ciki umman takeji a ranta na ganin irin yadda rayuwa ta canja musu lokaci daya,'ya'yan dan uwanta suka maida ita kamar mahaifiyarsu,hira suka ci gaba dayi har ta gama gyaran kayan ta miqe tace

"Mummy bari inje wajen yaya abdul naji kiran da yake min"

"Toh ruqayya,Allah yai miki albarka"

"Amyn mummy" ta fada ta fita daga dakin,wajen abdul ta tapi tayi knocking qofar,kasancewar yasan ya kirata kawai yace mata ta shigo,shiga dakin tayi ta zauna sannan yace

"Har kin gama taya mummy aikin??"

"Ehh na gama,ka dawo daga wajen matar taka"

"Ehh,dama skul ce,gobe da safe kada kibi motan driver,ki jira zamuje skul din akai fadeelah"

"Wow yaya,amma naji dadi,Allah ya kaimu"

"Amma ya kike ganin zamanta a school din a matsayinta na matar aure??"

"Yaya zan kula da ita sosai,kar ka damu"

"Ok,u can go"

Miqewa tayi shima ya miqe suka fita a tare,suna shiga tayi daki, shi kuma ya tafi dakin mommah,tana zaune tana waya da mamin hannan ya shigo,zama yayi sai da ta gama wayar sannan ta juyo ta kalleshi

GAMON JINIWhere stories live. Discover now