GAMON JINI 75 to 80

198 11 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_wannan page din naki ne *aysha sada machika* a cigaba da suburbudo mana *hasken rayuwata* muna karancewa,Allah ya qaro basira,I luv u loads_ 😘😘

7⃣5⃣ to 8⃣0⃣

Zuwa yamma komai ya kammala a gidan,rukhy sai rawar kan bikin take,ga hannan ga sabuwar sistern ta kuma matar yayanta,anyi musu lalle mai kyau na gani na fada,amma hannan ran nan a hade,don ita bata ga ampanin wannan lallen da akace ayi mata ba ranar da tapi kowacce rana baqin cikinta,haka dai tai tayiwa rukhy mitar lallen ita dai dariya kawai take mata har ta bata haushi.

Fadeelah kuwa duk da bata da sabo har sun dan saba da rukhy saboda surutun da rukhyn take tayi mata,hkan yasa itama tadan saki jikinta ganin tare zasu zauna a gidan da rukhyn.

Umma tunda ta pito daga wanka ta shirya ta pito aka ci gaba da sha'ani da ita,jinta take kamar sabuwar jaririya saboda farin cikin dawowa cikin ahalinta,sai yamma sosai suka pito mommah,mami,da umman driver ya jasu suka tapi super market,kaya suke daukowa komai iri daya guda uku,atampa,laces,mayapai,jakunkuna da takalma,siyayya sukayi mai yawa sosae sannan suka wuce wajen telan mommah ta bashi ya dinka musu biyar kapin gobe da daddare, suka dawo gida.

Bayan sun dawo ne da daddare suka taru su uku suka kira hannan domin sanar da ita abinda ya paru da aurenta amma ko kadan basu fada mata mubarkh ne mijin ba,idan taje ta gani,kukanta taci sosai ta godewa Allah,ta haqura.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Abdul likita yana zuwa ya dubashi da taimakon tambayoyin da yamai ya tabbatar da cewa damuwa ce tamai yawa,abdoul ne ya roqi doctorn akan kar ya fadawa su mommah abinda yake damunshi saboda kada hankalinsu ya tashi,dn hka magungunan daya rubuta ya miqa mai,ya bashi shawarwari sannan ya tapi.

Shigowar mubarakh kenan dakin ya tarar da shi kwance inda ya barshi,cikin zolaya yake tambayarshi

"Ango,har yanxu baka pita ba,bare ma kaje kaga amaryarka??"

Qara qunshe fuska yayi

"Kai me ya hana kaje ka gano min ita??"

"Ni ai na ganta har na gaji ma,kaine dai nake ganin ma sau daya ka taba ganinta"

Kafada abdoul ya daga alamar rashin damuwa da maganar da mubarakh yakeyi

Miqewa yayi daga kan gadon riqe da takaddar da doctor ya bashi,mubarakh ne ya hangi takaddar yace

"Meye a hannunka??"

Hannun ya kalla sannan yace

"Takaddar magani ce,wai mommah ta aiko doctor ya duba ni"

Yana tunanin ya tambayi mubarakh ya labarin budurwarshi da yadda akayi ya pasa aurenta ya auri hannan amma sai yaga tambayar is silly,tunda mubarkh bai fada masa ba da kanshi ya haqura,miqewa yayi ya pita,don yana son ya cirewa kanshi damuwar nan yayi rayuwarshi.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Washegari ya kama ranar asabar da za'ayi wedding diner din bikinsu,kowa farin ciki yakeyi banda hajiya saudat da ko sabgar bikin ma bata shiga ba,haka su mommah da suka kasance iyayen amare da na angwaye suka pito cikin shigar su iri daya su uku sunyi matuqar kyau sosai.

Amare ne suka shirya cikin wani Material royal blue mai qyalli,makeup artist aka kirawo tai musu kwalliya dukkansu sunyi kyau don dama wajen kyau dai sai dai ace maasha Allah,hannan da take komai cikin rashin fahimta bin umarnin mommah kadai take tunda tace mata bata son musu.

Itako fadee dk jikinta ba qwari,saboda yadda auren ya kasance,sun zama ready ne mubarakh ya shigo ya tadda mommah ya shaida mata abdoul pa yaqi shiryawa akan bazaije wata dinner ba.

A tare suka koma ta tarar da shi a kwance da waya yana dannawa,mommah da ta zata jikin nashi ne ma ganinshi da waya yasa ta tsuke fuska ta qaraso cikin dakin

"Aikin me kake da baka tashi ka shirya ba??" Ta tambaye shi

Miqewa yayi tsaye yana sosa kai yace

"Jikin nawa ne ba dadi" kallon shi tayi tace

"Banga alama ba,maza ka shirya yanxu yanxu ka zo ina jiranka" tana kaiwa nan ta juya ta bar dakin.

Ganin ba yadda ya iya yasa ya tashi ya fada toilet,mubarakh da dama ya riga ya gama shirinshi fita yayi a ranshi yana son ganin hannan don tunda aka daura aurensu bai sata a ido ba.

Cikin mintunan da basu wuce talatin ba abdoul ya shirya cikin irin shigar mubarakh,shadda ce fara dinkin abuja style,akai mata aikin kalar royal blue,da hula itama royal blue,sunyi kyaw sosai kamar twins suka pito abduol fuskar nn ba annuri suka shiga part din mommah.

Suna shiga gidan ya kaure da guda abokanan wasa suna ta takonanarsu,mubarakh ne me basu amsa shi kuwa gogan ko takan su bai bi ba ya para baza idon inda zaiga mommah.

Ganin bai ganta ba yasa ya nupi dakinta,abude ya ganshi hakan yasa kawai ya shiga ciki,kan gado ya tadda ita tana hada wasu kaya ya qarso ya zauna kusa da ita,kwantawa yayi ya dora kanshi akan qaparta,baice komai ba haka itama.

Hannunta ta dauka ta dafa kanshi

"Abdul me yake damunka kwana biyu,kullun rashin lapiya,gashi har wata rama kayi"

"Shiru yayi ta cigaba

"Kayi haquri,dk abinda ka gani a duniya ya faru da mutum muqaddari ne daga Allah,yarinyar da aka aura maka er uwarka ce,jinin ka ce,duk da ba'a nemi zabinka ba amma mahaifinka ya tabbatar bazaka taba watsa masa qasa a ido ba,saboda hka yanxu ka girma,matar ka tana cikin gdannan kapin ku tare a naku gidan zuwa wani lokaci"

Shiru yayi maganganunta suna kwantar mai da hankali,ji yake zuciyarshi tana yin sanyi sosai,daurewa yayi yace

"Thanks mommah"

Tashi yayi itama ta tashi suka pito,a wajen suka tarar da mubarakh suna ta hira da en uwa,ita dai barinsu tayi anan ta tapi dakin rukhy ta sami amaren ta fito dasu,kiran su mubarkh tayi suma suka pito farfajiyar gidan inda aka jera motoci ta saka kowa da amaryarshi a mota dai daya da driver ya ja suka fita daga gidan,sauran en biki ne suka ci gaba da tapiya.

Kasancewar abdul baya ta fadeelan ma yasa ko inda take bai kalla ba,suna cikin mota ne kowa yayi shiru ba mai magana,inda ita kuma hannan har yanxu ta kasa fahimtar inda wannan dramar ta nupa ganin tare da mubarakh mommah tasa su a mota,ana nupin shine mijin?? Wata zuciyar ce tace mata a'a bashi bane,haka dai har suka isa wajen tana ta saqe saqen zuci.

Suna isa wajen daidai da zuwan su mami,su rukhy,khadija da qannenta ne suka pito domin shiga da amaren cikin hall din da ake bikin,waqar *wedding day* ce ta _patoranking_ take tashi a wajen sabida shigowarsu,cikin tsari suka shigo dasu kowa ya zauna a mazauninsa,an ci, ansha an bari a wajen,nan na hango su fa'iza getso,su ontop,su salmerh da duk en *kainuwa fans* da kuma *miss marriam novels group* anata murnar ganin su fadeelah _lol_ 😄😄😄

Anyi shagali lapiya an tashi lapiya,a yadda sukazo a haka suka koma gida,hannan aka para yiwa shirin tapiya abuja gobe lahadi tare da mijinta.

Marriam mayshanu  👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now