GAMON JINI 🔚🔚🔚

338 22 1
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
(together we stand and succeed)

1⃣0⃣5⃣

Washegari da rana tana zaune ita kadai abdoul ya fita,wayarta ta janyo tana danne danne,cikin contacts dinta taci karo da number *baba kabiru* kamar yadda tayi saving ranar da suka hadu,dialling number tayi,taji ta fara ringing,sai can taji an daga wayar,da sallamarshi ya daga wayar,amsawa tayi jin cewar bai gane mai magana yasa tace

"Baba fadeelah ce"

"Toh toh toh fadeelah ya kuke"

"Lafiya lau baba,ya mai jikin"

"Mai jiki gamu dai a asibiti,jiki yaqi dadi"

"Toh a gaishe shi da jikin,muna nan zamu zo da mummy in shaa Allah"

"Toh fadeelah,Allah ya kaimu"

"amyn"

tace ta kashe wayar,jingina kanta tayi jikin kujerar,number mummynta ta kira don jin yadda sukai da abbah akan maganar zuwansu duba kawu,tace mata ya barta,ce mata tayi idan abdul ya barta ko yau sai suje,mummy tace sai dai gobe,don yau zataje gidan mommah ganin jaririya,a kan haka suka tsaya ta kashe wayar.

Bai dawo ba sai bayan sallar la'asar,ta idar da sallah taji knocking dinshi,tashi tayi taje ta bude mai gidan,tana budewa yayi hugging dinta,ya rada mata a kunne

"I miss u baby" kafin tace wani abu ya dauke ta tundaga qofar gidan har parlonsu,tana dariya ya direta kan kujera,zama shima yayi suka fara hira,a cikin hirar ne ta tambayeshi zuwa wajen kawunta gobe,har wayar da sukayi da baba kabiru daxun ta bashi labari,cewa yayi Allah ya kaimu goben sai suje tare,taji dadi sosai da ya barta kuma yace zaije.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Tun da safe da ta tashi,gyaran gidanta tayi ta yi musu abinci suka ci,suna fitowa taga sabuwar mota dal,juyawa tayi ta kalleshi yai mata murmushi,tace

"Wannan fah??"

"Mota che" ya fada a taqaice,gaba yayi ta bishi a baya,kamar yadda ya saba shi ya bude mata qofa amma yau ta bangaren driver,har tayi can side din yace

"Baby nan xaki shiga fah"

Juyowa tayi ta qara mai kallon mamaki,tace

"Wa zai ja motar wai??"

"Ke mana" murmushi tayi ta dawo kusa dashi ta shiga,hannu ta miqo mai ya dora mata muqullin motar akai,tada motar tayi suka fita,suna tafe suna hira,ce masa tayi

"Wai yaushe aka siyo wannan motar"

"Jiya"

"Amma tayi kyau kuma tana da laushi"

"Kinji dadinta kenan"

"Sosaima kuwa"

"Ohk,dama taki ce ai"

Zaro ido tayi ta kalleshi "like seriously"

Gyada mata kai yayi "yeah like seriously"

"Wow,am out of words,just dunno frm where to start..."

       Katseta yayi da cewa "kin manta kenan"

"No dear,i must to,thank you so much"

"It'x my pleasure,and u deserve much more than this"

GAMON JINIWhere stories live. Discover now