GAMON JINI 30 to 35

221 9 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

3⃣0⃣ to 3⃣5⃣

Saida mubarakh ya tabbatar abdul yasha maganin ya kwanta sannan shima yay wanka,sam ya manta da cewar zai kira fadeelah sai da ya duba agogo yaga har 10:00 pm tayi,ganin cewar tym din yayi dare ya kirata ne yasa ya ajiye wayar ya kwanta.

Duk abinda mubarakh din keyi akan kunnenshi,don gaba daya tunani yaqi barinshi,sai da ya tabbatar mubarakh yayi bacci ya tashi ya shiga toilet yay alwala yazo ya tayar da sallah,ko da ya idar da sallar ma zama yayi yana addu'o'i domin samun mapita,yana nan har aka kira sallar asuba ya tashi mubarakh suka pita masallaci.

❣❣❣❣❣❣❣❣
BAYAN KWANA BIYU
❣❣❣❣❣❣❣❣

Yau ne ya kama ranar juma'a ranar da su daddy zasuje nemawa mubarakh auren fadeelah,parin cikin mubarakh ba zai misaltu ba inda shi kuwa abdul ba zai iya passara halin da yake ciki ba,duk yadda yayi qoqarin ya hana kanshi tunawa da fadeelah abin yaci tura.

A bangaren fadeelah murnar ta ta tsaya ne akan mubarakh zai rupa mata asiri ya aureta amma ita sam bayan ganin girmanshi da take,bata tunanin akwai son shi a ranta,don ma taga yana da kamala ne da alamun mutanene kirki da amma bazata taba yadda ta auri wanda ummanta bata taba ganinshi kuma ta yadda dashi ba amma sai dai ba yadda ta iya,tata qaddarar kenan kamar yadda ummanta take fada mata kullum.

Alhaji umar ne da abokansa su uku suka pito domin tapiya gidan su fadeelah,abdul ne zai kaisu kasancewar basu san gidan ba,inda mubarakh kuma yana shirin tapiyar da zaiyi abuja gobe.

Sunje gidan kawun fadeelah,an musu tarbar mutunci sai dai acikin ran malam shafi'u bai ji dadin yadda yaga alamun manyan mutane ne suka zo neman auren fadilan ba,ya sanar dasu duk abinda ya kamata su sani akan yarinyar kuma sunyi na'am da bayaninshi sun bada sadaki akan biki nan da sati daya,malam shafi'u ma ya yadda da hakan saboda  ba abinda zai mata na kayan daki"

Haka suka dawo gida,dad ne ya kira mubarakh ya masa bayanin yadda sukai da iyayenta yai godiya ya tashi,har zai pita dad ya qara kiranshi ya dawo ya zauna,tashi yai yaje ya bude wata safe ya dauko keys

"Karbi wannan,muqullan gidanka ne,tunda a abuja zaka zauna,idan kaje gobe sai kaje ka dudduba,zan bada order kayan da za'a saa mka a part dinka sai ka duba ka dawo ko ranar wednesday ne"
Karba yayi

"Na gode yaya,Allah ya qara arziqi"

"Amyn ,Allah yayi albarka"

Ya tashi ya pita.

Yana shiga daki ya dauki wayarshi ya danna wayar fadeelah,daga can bangaren ta daga wayar,cikin sassanyar muryarta tace
"Assalamu alaikum"

"Wa alikissalamu gimbiyata,da fatan kina lapiya"

"Lapiya lau"

"Ya umman mu "

"Tana lapiya"

"Albishirinki"

"Goro"

Dariya yayi sannan yace

"Nan da sati daya zaki zama matata In shaa Allah"

"Massha Allah" tace acikin sanyin murya.

"Bakya farin ciki ne gimbiya"

Shiru tai hakan ne yasa yai mata sallama ya kwanta bacci.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Washegari tun da sape ya shirya domin tapiya abuja,

Abdul ne ya tapi ya kaishi airport ya tapi akan abdul din zai tasaya akan shirye shiryen bikin kapin yaje yai en kwanakinshi  ya dawo.

Kuyi haquri da wannan pls,chaji yayi qasa

Marriam mayshanu 👌🏼

GAMON JINIWhere stories live. Discover now