GAMON JINI 1

760 27 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty dan lawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
1⃣

*T*afiya takeyi ahankali cikin nutsuwa tamkar wacce take yanga,amma Sam ba yanga take ba kawai dai tana tapiya me da yanayin nutsuwarta

Wani layi naga ta shiga Wanda shi zai sadata da gdansu,ba dadewa da shiga layin ta nufi kofar gdansu Wanda yake rukunin gidajen marasa wadata duk da cewa ginin qasa ne amma an samu damar yi masa plaster da siminti,sallama tayi ta shiga gdan inda ta Tarar da ummanta tana fama itacen girki

"sannu da aiki umma"

"Yauwa 'yar albarka kin barosu lapiya"

"lapiya qalau umma suna gaisheki"

dakinta ta nufa Wanda yake kusa Dana ummanta duk da cewa dakin NATA suna ya Tara don tare suke kwana a dakin umman tata.

Hijabin ta ajiye a dakin ta pito tsakar gida domin daura alwalar la'asar,har ta gama alwalar tata ta koma daki don tayar da sallah ta tsinkayi muryar ummanta

"ki idar da sallar ki fito kici abinci"

toh tace kapin nn ta Tayar da sallah,ta Dade a zaune akan sallayar bayan idar da sallar tana kaiwa Allah kukanta tare da addu'ar neman rahamar Allah ga mahaifinta.

Lokaci daya kuma ta fada duniyar tunanin qiyayyar da en uwan mahaipinta suke musu,ita dai tunda ta tashi take ganin cin kashin da suke zuwa har cikin gida suyi musu bayan Duk cikin en uwan mahaifin NATA babu Wanda ya taba tallafa musu ko da kwayar shinkafa ce
"fadilah"
muryar ummanta ta katse mata tunan"na'am umma"tace tare da mikewa domin fita wajen ummanta ta.

❣❣❣❣❣❣❣❣

*Y*arinya CE wacce bazata wuce shekara 15 zuwa 16 ba yanayin fatarta bamai haske bane,irin kalar nn CE da ake cewa wankan tarwada,BATA cikin gajeru amma bata fiya tsayi ba

Ita kadai ta taso ta ganta a cikin gidansu sai mahaipiyarta,btasan mahaifinta ba kasancewar tun cikin ta yana wata biyu ya rasu.

kasancewar suna kusa da en uwan mahaifinta yasa ta sansu sosai duk da cewar babu jituwa a tsakaninsu.

Bata San komai dan game da dangin mahaifiyar taba,wani lokacin yana gwada tambayar ta amma bata samun nasarar samun koda wani Abu ne daga labarin nasu har dai ta fuskanci maganar tana Dan daga wa mahaifiyar tata hankali

Dalilin dayasa ta daina tambayarta kenan amma abin yana damun zuciyarta na son sanin menene dalilin dayasa mahaifiyar tata BATA son zancen ahalin NATA.

❣❣❣❣❣❣❣
*S*allama suka jiyo a qofar gida Wanda yasa fadilah tashi zuwa daki dauko hijabinta ta fito don ganin Wanda yake sallama,wanda ta gani tsaye qofar gdan nasu ne ya Sanya annurin fuskarta daukewa don tasan duk abinda zai kawo shi ba alkhairi bane.

"yau da wuri aka dawo daga yawon kenan"
Sunkuyar da kanta tayi qasa domin Indai irin wadannan maganganun ne sun saba dasu daga wajen en uwan mahaifin nata

"Yi min magana da matsiyaciyar uwarki"
Jiki a sabule ta juya ta koma cikin gida,yanayin da ummanta ta ganta ne yasa ta tambayarta

"Lapiya??

"Waye a wajen??

Da kyar ta iya bude bakin ta tace mata

" abban su rashida ne"

maza dauko min hijabi na a daki.

Fitowa tayi cikin soron gidan inda ta hango shi ta can qofar gidan

"Sannu da zuwa,qaraso saga ciki mana"

Cikin soron gidan ya shigo tana gaisheshi ma yai banza da ita

"Zuwa nayi akan maganar wannan yarinyar da kika barta tana gantali a gari da sunan zuwa makaranta,na gaji da maganar mutanen gari akan na bar 'yar Dan uwana sakaka a gari,saboda haka ko ta fito da miji in mata aure ko kuma na aura mata Wanda na ga dama"

Daga haka ya juya ya fice daga gidan,tashi tayi itama daga Inda take a tsugunne ta koma cikin gida,kallon fadila tayi a Inda take tsaye data tabbatar taji duk abinda wan mahaifin nata yace.

Muje zuwa.

GAMON JINIWhere stories live. Discover now