GAMON JINI 99

189 13 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_Jinjina gareki sis *maimuna umar ata* ina miki murnar fara book dinki mai suna  *ni da yaya farouq* Allah ya qara basira ai ta suburbudo mana muna karancewa_  ana mugun tare 🤝🏻

_*Second to the last page*_

9⃣9⃣

❣❣BAYAN WATA 1❣❣

fadeelah ce zaune a daki ita da rukhy suna english lesson,don sunyi hutun makaranta,zuwa yanxu ta fara iya fahimtar turancin,don tana iya ji ta kuma karanta,mayarwar ce ke mata wahala,sanadin haka yasa ta fara fahimtar karatunta,sai gashi ta zama daya daga cikin best students a ajinsu a wannan term din da sukayi exam,dad har ma da abdoul sunji dadin ganin irin result dinta,dad ne yace wa abdul tunda an fara registration na SSCE yaje yai mata registration tayi a wannan shekarar.

abdoul ba qaramin dadi yaji ba don yana ganim hakan na nuni da cewar ya kusa samun cikakken kusanci da matarshi.

Washegari online yai mata registration din waec,neco da jamb,duk abinda akeyi ita bata da labari ma.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Malam shafi'u ne a kwance ranga ranga ba lafiya,a hanyar masallacin asuba ya fadi aka dauko shi,rabin jikinshi gaba daya ya daina aiki,tsawon wata 1 kenan yana kwance komai sai dai ayi masa,sunje asibiti kuma an tabbatar musu da cewar sai dai su kaishi egypt ko india ko za'a dace,sanin cewar basu ajiye ba basu bayar ajiya ba yasa suka dawo dashi gida suka kwantar ana na gargajiya.

Kabeer ne zaune a gefenshi bayan ya gama yi mai wanka ya ce

"Kabeeru na gode da dawainiyar da kake tayi dani,Allah ya saka da alkhairi"ya fada da muryarshi da bataa fita sosai don bakin ya karkace gefe daya

"Haba yaya, kai dan uwa nane ya zama dole na inyi maka ko abinda yafi haka ne"

"Nagode"

Kafin kabeer yace wani abu yayyenshi suka shigo a tare malam hashimu da malam saleh,kallo malam shafi'u yabisu dashi yana tuna yaushe rabonsu da gidansa kusan sati kenan,wa'yanda sukafi kowa kusanci dashi 'yan uwanshi sai kabeer ne yake masa wanka kullum da alwalar sallah da dai sauran abinda baya iyawa,cikin tunanim da yakeyi ne ya tsinkayi muryar su

"Yaya ya jiki"

Hannunshi mai lafiyar ya dan daga musu,basu damu da haka ba kasancewar sun san ba magana yake ba sosai

Daga hka basu qara cewa komai ba,suka miqe,naira dari malam saleh ya dauko a aljihunshi ya miqawa kabeer

"Ga wannan,ko cefane ayi musu"

Kallon kudin yayi ya karba yace musu

"Angode" suka kada kansu suka fita,har yanxu malam shafi'u bai daina kallon su ba,har suka fita hawayene ya fara zirarowa daga idonshi yana tunanin tun bai mutu ba kenan saboda bashi da lafiya sun watsar dashi,in ya mutu kenan a cikinsu ba wanda zai iya kula da iyalinshi da 'ya'yanshi,a take wata nadama ta saukar mai na yadda yayi da iyalin dan uwanshi mahmoud da ya rasu,ya cinye musu gadonsu,ya muzgunawa rayuwarsu gashi nan shi tun bai mutu ba yaga abinda 'yan uwanshi uwa daya uba daya suke mai,sai dan uba da suka raina ne yake kula dashi.

bude baki yayi zaiyi magana kabeer yace

"Yaya ka daina yawan magana sosai,ka bari bakin naka ya dan qarasa budewa"chewing gum ya bude a leda ya samai a bakin ya tauna saboda bakinshi yana dan saisaituwa da taimakon taunar chewing gum din.

Miqewa kabeer yayi ya kirawo wani yaro da baifi shekara 9 ba a gidan,jan hannunshi yayi suka fita,wajen me kayan miya suka tsaya ya siya musu kayan miyan da zasuyi abinci ya bawa yaron ya kai mamanhi sannan ya siya na gidanshi ya tafi,ba nisa zuwa gidanshi don gidan mlm hashimu,da mlm saleh ne sannan na kabeer

❣❣❣❣❣❣❣❣

Mommah ne da mummyn su khadija a zaune a dakin dad suna magana akan zuwa convocation din su abdulmaleek,shawara suka yanke kan cewar mummy da mummy zubaidah zasu tapi abar mommah a gdan saboda yara,waya dad ya dauka yai dialing number mummy zubaidah,umarni yai mata akan taxo part dinshi ta sameshi,cikin mintunan da bazasu wuce 5 ba ta shigo da sallamar ta ta zauna gefe,mummyn khadija ce ta miqe ta fita,ya kasance saura su uku a parlon,gyaran murya dad yayi yace

"Zubaidah in Allah ya kaimu jibi ki shirya zamuje cyprus"

Farin ciki ne ya lullube ta na karar da suke mata akan 'ya'yansu tunda ta dawo gidan,,muryarshi ta qara ji yana cewa

"Magana ta biyu kuma,Allah ya fito mki da miji sbd haka ya kamata kiyi aure" a firgice ta dago ta kalleshi tama kasa cewa komai,gyada kai yayi alamar tabbatar da maganr da yakeyi yaci gaba

"Alhaji balarabe babban amini na ne wanda nasan cewar mutumin kirki ne,ya nuna sha'awar aurenki saboda hka kafin ku tafi ko zuwa gobe zaizo,idan kun daidaita maasha Allah sai shan biki" Ya qarasa maganar cikin zolaya

Kunya ce gaba daya ta rufe ta dajin zancen aurenta,don dama saboda fadeelah ne batai auren ba ta zauna ta jure rashin mutuncin dangin mijinta,kuma tunda yanxu fadeelan na tayi aure,Allah yasa hkan yafi alkhairi.

*Nima nace amyn*

Washegari alhaji balarabe yazo sun zauna kuma sun fahimci junansu,hakan ne yasa alhaji umar yace suna dawowa daga cyprus sai a daura auren,sun amince da hakan,fadeelah ba qaramin farin ciki tayi ba jin cewar ummanta zatayi aure,don ko ba komai tayi rayuwar farin ciki a gidan aure.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Kwanci tashi asarar mai rai,yau su mummy sun dawo daga cyprus,duk gidan a cike yake da farin cikin dawowar abdulmaleek da abdallah,har su mubarakh da hannan ba'a barsu a baya ba,tana nan tana fama da cikinta na wata 4,anci ansha angama komai yadda ya zamo dai dai da satin da su fadeelah zasu fara exams ta waec

Cikin sa'a suke exams din,suna cikin waec jamb dinsu ta fito kuma taci,kullun shi yake kaita ya dauko ta zuwa yanxu soyayya tayi qarfi tsakaninsu,don bashi kadai yake nuna mata yanda yake sonta ba,itama tana qoqartawa ta nuna masa soyayyarta.

Bikin mummy zubaida ne ya tashi,komai a rana daya aka daura aure aka kai amarya gidan mijinta,bata samu matsala da danginshi ba ko matanshi dake gdan,kasancewar gidanshi part din mace daya ne yasa ya ware mata gidanta daban shiyasa ba abinda yake hadasu da ita tana zaune a gidan mijinta cikin kwanciyar hankali,bayan bikin ne su mubarakh suka koma abuja cike da farin ciki

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now