GAMON JINI 60 to 65

187 9 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_kina inane *maman juwairiyya and nasreen* kinsan bazan manta dake ba,saboda ina mugun yinki ne,mata a gidan baban juu,ana mugun tare_ 🤝🏻 _wannan  page din duk naki ne ke kadai,kiyi yadda kika ga dama dashi_

6⃣0⃣ to 6⃣5⃣

Dad ne yayi gyaran murya cikin sassayar murya ya para magana.

"Alhamdulillah,Allah ne kadai abin godiya da ya nuna mana wannan rana da muka dade muna addu'ar ganinta"

Sautin kukan umma ne ya qara tashi,sai a lokacin nema abdul yasan cewar da wasu a dakin bayan mommah,dad ne ya kalleta yace

"Zubaida ba kuka zakiyi ba,godiya zakiyiwa Allah da ya hada fuskokinmu tun kapin ya dau ranmu,duk da dai Allah yayiwa hajiya rasuwa tun kapin na baro libya"

Tasowa tayi daga inda take ta zo gabanshi,ta durqusa akan gwiwowinta cikin kuka

"Ka gafartamin,haqiqa naga quncin rayuwa ta sanadin qin bin umarninku da nayi,nayi nadama  kuma daga qarshe nazo bani da wata hanyar da zan para nemanku kasancewar banida abinda zan koma qasarmu dashi"

Tasota yayi daga tsugunnen da take ya zaunar da ita a kusa dashi.

❣❣ASALIN LABARIN❣❣

Zubaida 'ya ce ga alhaji aliyyu wato mahaifin alhaji umar,itace 'ya ta biyar a gidansu,kamar yadda muka sani asalinsu en libya ne.

Zubaida da zainab (mommah) qawayene sosai kasancewarsu cousins,sun shaqu sosai har hakan tasa soyayya ta shiga tsakanin alhji umar da zainab ta sanadin qawancensu.

Mahmoud mahaipin fadeelah asalin dan cikin kano,cikin yakasai,gidansu irin family house dinnan ne na gargajiya,babansu yana da mata uku,maman su shafi'u itace uwar gida,'yayanta shida,biyu maza hudu mata,sai maman mahmoud wacce shi kadai ta haipa,sai maman kabeer wanda shine auta da yayyenshi biyu mata a dakinsu.

Duk cikin gidansu mahmoud ne kadai yake da zuciyar nema,duk da basa karatu a gidan,iyakacin primary suke tsayawa,hakan yasa mahmoud ya para en qananan kasuwancinsa,Allah yasa masa albarka a kasuwancin,har ya bude qaramim shago na siyar da shaddodi da atampopi da dan kayan mayapai hka.

Wani maqocinsu ne alhaji sambo,ganin hankalin mahomoud yasa yake taimaka masa a cikin kasuwancin sa,yasha gwada shi akan dukiyarshi kuma ya tabbatar da yana da amana,hakan yasa ya para janshi a jiki har suke pita qasashen qetare zuwa saro kaya tare.

Cikin haka wata rana pitar tasu takaisu libya,sun saro kayansu sun dawo kuma sunji dadin garin sosai hakan yasa suka maida garin wajen zuwansu,suna yawan zuwa sosai.

A dai dai lokacin da mahmoud kuma arziqi ya qara yawa,don har ya para gini a gandun albasa,a cikin tapiyar da sukeyi ne har wata rana da daddare ya pito shan iska,suka hadu da zubaida da zainab,sun dawo daga gidan su zainab,sbd a gidansu zubaida zasu kwana,sai ya kasance yaji zubaoda ta kwanta masa a rai,kullum haka yake potiwa idan sun dawo daga kasuwa amma bai taba mata magana ba.

A cikin haka watarana ya daure ya mata magana,sun dan para samun matsala don parko bata kula shi ba har sai daga baya suka daidaita,cikin qanqanin lokaci shaquwa mai qarpi ta shiga tsakaninsu,soyayya sukeyi sosai ba tare da kowa ya sani ba sai zainab.

A haka har lokacin tapiyarsu yayi,tayi kukan tapiyarshi don a tunanin ta baxai dawo ba sai daya tabbatar mata da cewar zai dawo sannan hankalinta ya dan kwanta,da ya tapi kuwa tayi kewar shi sosai da sosai,tapiyar da yayi suka dade basu koma libya ba kuma ba waya,hakan ne yasa har ta pidda ran dawowarshi,hakan yasa kullum tana cikin tunani,har wata 'yar ramewa ta para yi.

Shima a nashi bangaren yana ta tunanin kar taga kamar yaudarar ta yayi ya tapi ya barta,lokacin gininshi yayi nisa sosai,kuma wasu abubuwan ne suka tsayar dasu basu koma libya ba,a cikin haka alhaji sambo ya cewa mahmoud sati me xuwa ya shiya zai je libya shi kadai don shi alhaji sambon yana da abubuwa da yawa,murna wajen mahmoud bata misaltuwa,hka ya shirya ya tapi libya.

Ganinshi da xubaida tayi ba qarami farin ciki tayi ba,a lokacin ne suka shirya ta fada a gidansu,saboda asan dashi,don yana son idan ya tapi ya qara dawowa a yi aurensu,haka akayi ta sanar da maminta,tun daga nan bata ga alamun nasara ba,don maminta cewa tayi baxasu bawa wani aurenta ba wanda basu sanshi ba ya tapi da ita qasarsu,damun mamin tayi da magiya da kuka akan ta sanar da umar tunda babansu ya rasu,ita tana sonshi taji zata bishi.

Ita dama maminta sam ba me son 'ya'yanta suyi auren nesa bane,bare ma wanda basu sani ba,magiyar da zubaida ta dinga mata ne yasa ta haqura ta fadawa umar,a wajenshi shima din dai hakan take maganarsu daya da mami,amma zubaida ta kasa haqura da mahmoud,umar yayi dukan yayi mata qulle,bata zuwa ko ina amma dk a banza.

Daga baya ne umar yace mata in ta yadda ta aureshi amma duk abinda ya biyo baya kar ta neme su,saboda so ya rupe mata ido ta yadda da wannan sharadin,amma tana so su daura mata auren da kansu,hakan ne yasa mahmoud bai san yadda sukai da iyayen nata ba,haka aka daura musu aure tana kuka mami na kuka suka taho nigeria,wannan shine dalilin rabuwarta da danginta.

Tunda suka taho dangin mahmoud kwata2 basa nuna mata so ko kadan sai mahaifiyarshi,shi kuwa yana ji da ita sosai,arziqi yapi nada,hakan ne yasa ya siya wasu qananan gidaje da basu kai nashi girma ba amma an musu ginin zamani yasa en uwanshi a ciki,hakan ne yasa basu da nisa da gidajen en uwanshi,duk wata hidimarsu shi yake yi amma duk da haka ba sonshi suke ba kamar yadda ya dauke su duk daya ne.

Suna wata na hudu da aure a lokacin zubaida tana da ciki na wata biyu Allah yayiwa mahmoud rasuwa sanadiyyar gajeruwar rashin lapiya,zubaida tayi kukan rashin mijinta mai sonta kuma gatan ta,don a duniya yanxu bata da gatan daya wuce shi,tabar qasarta tabar iyayenta gashi wanda ta biyo babu shi,tayi baqin ciki sosai,tayi baqi ta rame saboda tunani ga kuma ciki.

Bayan rasuwarahi ne da watanni itama mahaipiyarshi ta rasu,ganin haka yasa en uwanshi suke ganin dukiyarshi ikon su ce,dalilin da yasa kenan har gidan da zubaida take ciki suka karba,suka samar mata wani gidan qasa acikin unguwar take zaune har watan haihuwarta ya kama ta haipi 'yarta kyakykyawa mai kama da mahmoud,komai na ubanta har kalar fatarta.

Cikin halin yau akwai gobe babu haka ta raini 'yarta har ta girma,yayyen babanta sunso suyi mata aure tuntuni amma zubaida ta qiya,don tana son fadeelah tayi karatu ko yaya ne.

A cikin haka har yazo ranar da yace idan bata yadda ta pito da miji ba zai hada ta da wanda yaga dama.

A can libya bayan tapiyar zubaida,gaba daya mami ta kasa kwanciyar hankali na rashin sanin duniyar da 'yarta ta tapi, hakan ne yasa take mata addu'a wane lokaci,amma umar ko a jikinshi don a ganinsa ita ta zabi ta tapi ta bar gida,tun mami tana daukar abin da wasa har yazo ya para affecting lapiyarta,bayan tapiyar zubaida da kusan shekara biyar Allah yayi mata rasuwa,kapin ta rasu ta shaidawa umar cewar ta rataya haqqin neman zubaida a wuyanshi duk inda take,kuma a fadawa zubaida ta yafe mata.

Sanadin umar yasan mahomud dan nigeria ne kuma kano yasa ya para zuwa kano yana komawa lokaci zuwa lokaci ya para dan kasuwancinsa,a zuwan da yake ne har ya mallaki gida a sharada daga baya ya dauko matarshi zainab suka dawo nigeria a lokacin ya kasance yawancin kasuwancinshi yana yinshi ne a nigeria,sai dai yaje libya ya dawo.

Marriam mayshanu👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now