GAMON JINI 40 to 45

183 11 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

4⃣0⃣  To 4⃣5⃣

Shirye shiryen biki akeyi sosai a gidan alh.umar,baqin libya sun para zuwa,dad ne ya bawa mommah kudin da za'a hada lefe,kasancewar abin yazo dab da dab yasa mommah tace idan an gama biki akai mata lefen can abujan.

Abdul ne zaune a daki shi kadai yana rubutu a wani dan qaramin diary,nayi nayi na hango me yake rubutawa amma duk ya kare ko'ina,bayan ya gama rubutun ne ya janyo wata drawer a gepen gadon ya sa diaryn,wayarshi dake hepen shi ce tadau qara,yana dagowa yaga abbanshi ne,miqewa yayi kawai ya pita ya nupi part din dad.

Da sallamarshi ya shiga ya sameshi zaune kan 3 sitter,sai mommah da mummy a gefenshi,gaishesu yayi ya nemi waje a qasa ya zauna.

"Abdul" dad ya kira sunanshi,kanshi ya dago ya kalli dad

"Na'am"

"Meya sameka,baka da lapiya ne??" Ya tambayeshi

"A'ah dad,lapiyata lau" mommah ce take mai kallon tsanaki inda taga ya dan rame kwana biu.

"Tashi ka dauko min waccan ledar"dad ya pada yana nuna mai kan wata kujera,miqewa yayi yaje ya dauko ledar ya ajiye a gaban dad.shaddodi ne a ciki iri daya guda goma,dad yace

"Ka dauki wannan kakai muku dinki kai da mubarakh,sannan ga cheque nan aje a siyo huluna da takalman kayan,abiya kudin dinkin sauran za'a dinko daga libya"

"Mun gode dad,Allah ya saka da alkahiri" ya karbi cheque din ya hada da ledar kayan ya pita yabar dakin.

Yana pita ya koma daki yaga missed calls din mubarakh guda biyu,kiranshi yayi,ringing daya tayi ya daga wayar

"Ya ina ka shiga ne ka bar wayar"

"Naje wajen dad ne,ya bada kaya ai mana dinki"

"Ohk,mungode"

"pls na turo mka kudi a account kaje ka siyo all food stuffs akai gidansu fadeelah"

"Dan aikenka na zama kenan,to baxani ba"

"Pls mana,in bakai ba wa zaimin,pls kaje"

"Toh zanje,amma kasan dai ni ba matsiyaci bane zaka turo min kudi ko??"

"Ooh,naji kai min sendin kudin back,aje a siyo kayan akai musu pls"

"Ohk,yaushe zaka dawo ne??"

"On wednesday in shaa Allah"

"Allah ya kaimu" yace tare da kashe wayar

❣❣❣❣❣❣❣❣

Saleema ce zaune tana tunanin yadda xata bullowa al'amarin abdul,malaminta daya bata wani garin magani akan ta sawa abdul a abinci ko abinsha,ya tabbatar mata da sai abinda tace amma har yanzu bata samu damar bashi ba kasancewar ko ta shiga part din mommah,bata bari ta taya ta aikin girki,kuma ba harkarta yake shiga ba bare tamai girki ta kai mai,gashi ko cin abincin part din mummy bai yi.

Waya ta dauka ta kira wata number,tana ringing daga can a ka daga,magana ta para yi

"Qawata har yanxu pa ba nasara,ban san yadda za'ayi ba,kinsan pa ni so nake a hada ayi bikin nan"

shiru tayi alamar tana sauraren magana  awayar sannan tace

"Shi yasa nake sonki qawata,bakya taba barina da matsala,haka za'ayi sai kin jini" ta kashe wayar ta miqe ta nupi qopar bedroom din mummy.

Tana shiga ta ganta zaune kan gado tana waya,tana ganinta ta katse wayar

"Me yasa ke baki iya sallama ba idan xaki shigarwa mutane daki"

"Yi haquri aunty,magana nazo muyi"

"Ina jinki"

"Aunty akan maganar abdul,me zai hana ki fadawa dad cewar muna soyayya da abdul,ya kamata a hada auren nan"

"Saboda shi mahaukaci ne irinki ko??,kawai zai hada aure ne ba tare da ya tambayeshi ba ko uwarshi,ke shirmenki ya miki yawa,ki rabu dashi mana,manyan mutane nawa kike kulawa kin tsaya son auren wannan yaron"

Kuka ta pashe dashi

"Dan Allah aunty ki taimaka min,idan ba ke ba ba wanda zai iya min wannan abin dan Allah,wlh ina sonshi sosai"

"Tashi ki bani wuri" tace tana nuna mata hanyar qopa,tashi tayi ta pito,tana zuwa qopar dakin ta goge hawayenta tayi wani shu'umin murmushi ta tapi dakin khadija.

"Khadija wai wannan yayan naki ko dan girki bakya mai"

"Idan nayi ma ba lallai yaci ba,indai yaya abdul ne,kuma ni ban ma iya abubuwan da ya pi son ci ba,ya pison abincin mommah"

"Me yapi so??"

"Kayan gargajiyar nan"

"Toh ko zamuyi mai waina ko sinasir da miyar taushe,tunda ni na iya,sai kice ke kikai mai"

"Toh sai kije kiyi don ni kinsan ban iya ba,kuma bana son na iya"

"In anyi zaki kai mai ??"

"Ehh"

Pita tayi daga dakin ta nupi kitchen a take ta hada kayan markaden waina tayi a blender,ta hada kayan miya ta daura miya a dayan gas din,nan da nan ta gama hada markaden wainar dayake kadan tayi ta para suya.

Sai da ta gama tsap sannan ta koma daki ta dauko qullin maganin ta zuba a cikin miyar taushen ta juya sosai sannan ta rupe flask din.

Zuwa tayi ta sanar da khadija ta gama tazo ta dauka,bata kawo komai ba ta tashi tazo su nabeel suka taya ta suka kai mai daki

"Sis yau me na samu ne haka"

"Waina ce nayi maka"

"Wow amma na gode sosae,zo kiji"

Matsowa tayi ya zaro kidi a aljihunshi,da baisan ko nawa bane ya bata,karba tayi tace

"Na gode yaya"

Tana pita ya janyo flask din wainar, ya bude ta miyar ma,ya zuba a plate.miyar taushen tamai kyau a ido

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now