GAMON JINI 4&5

228 15 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

4⃣ & 5⃣
*M*ubarakh ne ya pito daga motar ya tsaya yana qarewa kyakykyawar fuskarta kallo

lura tayi da kallon da yake mata,hakan yasa ta daga qaparta tabar wajen

Bin tapiyar tata yayi da kallo yana jin wani irin Abu acikin ranshi hade da faduwar gaba,ba wai bai taba ganin mai kyanta ba ne,a'ah shi dai kawai yana jin wani Abu game da yarinyar
Har sai da ta bacewa ganinsa sannan ya koma cikin motar ya ci gaba ta tapiya.

Makarantar ta isa ta shiga ta zauna kasancewar bata da qawaye,don ita bamai son yawan magana bace.

Amma qwaqwalwarta na dauka sosai,hakan ne ya jawo mata farin JINI a wajen dalibai harma da malaman makarantar,baya ga qoqari ma da take dashi akwai nutsuwa a cikin duk lamarinta.

Khadija CE ta qaraso kan seat ta zauna kasancewar seat dinsu daya,fadeelah ta dago ta kalle ta suka gaisa har malami ya shigo aka para darasi.

❣❣❣❣❣❣❣❣

*M*ubarakh ne zaune a office din Abdul kan cushion din dake office din yana tunanin fuskar yarinyar daya gani dazu da safe,shi kanshi yasan ya kamu da Sonta ne DAGA KALLO DAYA
Abinda tunaninshi yake bashi kenan ya kuma tabbata da cewa ya samu matar aure domin daga ganinta akwai nutsuwa a tattare da ita.

Amma ta INA zai sake ganinta,har yasan wace ita??

Shi da yake shirin Barin garin cikin wani satin zuwa abuja.

Wata zuciyar CE ta amsa masa da cewa ya je ya jira ta hanyar da ya ganta,dn ya tabbata ta nan zta wuce ta tapi gida idan an tashi dga makaranta.

"Yesss"

yace da qarpi Wanda ya janyo hankalin Abdul zuwa Inda yake zaune.

"lapiyarka kuwa" Abdul ya tambaya

"Man I think am in luv"

Tabe baki Abdul yayi ya maida kanshi kan computer da yake dannawa domin shi baya cikin wannan shirmen.

Mubarakh ne ya mike tsaye yacewa Abdul

"Man ni zan wuce gida"

Daga kai yayi ya kalle shi

"Kaje ka cigaba da tunanin banzan ko??"

"Kai pa kana da matsala, kai ka zauna a hka in ka isa kar kai auren"

Ya saka kai ya pita daga office din ya hau mota ya tapi.

Dai dai Inda suka hadu da ita ya gangara yai parking duk da baisan lokacin tashin ba,amma yanajin zai iya jira ko awa nawa ne domin ya ganta"
Yana nan a zaune cikin mota har ya para ganin irin uniform dinsu sun para wucewa,nan ya para rarraba ido domin ganin ta Inda zata bullo.

Cikin sa'ah kuwa ya hangeta acikin tapiyarta ta nutsuwa tazo ta wuce ba tare da ta kula dashi ko mortar a wajen ba.

Kunna mortar yayi ya para tapiya har zuwa bakin titin da suka je suka hau motar da zata mayar dasu gida
Motar ya para bi har Inda ta ajiye fadeelah,sannan yai parking ya pito kasancewar lungunan unguwar tasu mota bata shiga,binta ya shiga yi har Inda takai qopar gidansu ta shige sannan ya juya zai tapi.

Tunawa da yayi ko sunanta bai sani bane yasa shi Dan dakatawa ko zaiga yaro,cikin sa'ah kuwa yaga wani yaro ya pito daga gidan da kullin barkono a hannu,yapito yaron yayi da hannu,yaron yazo had gabanshi ya tambayeshi sunan yarinyar gidan ya CE mai sunanta *fadeelah*

Hannunshi yasa a aljihu ya Ciro naira Dari ya bawa yaron ya karba ya juya ya tapi.

Cike da farin cikin ya isa gida kamar Wanda ta Riga tace ta yadda tana sonsa,ya para tunanin anjima da yamma kawai yaje ya sameta a gidansu duk da yana ganin kamar yarinya CE,kuma da ganin gidansu ba wadata amma sai yaji shidai zuciyarshi ta aminta da hkan.

Allah Allah yake lokaci yayi ya pita ko ya samu sauqin bugun da zuciyarsa takeyi da azalzalrsa ya je yaga fuskar babyn tasa.

Marriam_dianah👌🏼

GAMON JINIWhere stories live. Discover now