JIDDO(Gidan aurena) Part 35

14 2 0
                                    

JIDDO
(Gidan aurena)
   By
MAMAN NABEELA

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

02:15 pm

Juye yake a kan makeken gadonsa daya gaji da haɗuwa,   sam ya kasa baci tunaninta na neman zautar da shi a cikin daren nan wanda sanadinsa yasa ya kasa ko rintsawa duk da irin matuƙar gajiyar da ya yi. Ƙaro hasken fitilar ɗakin ya yi wanda ta ke ɗakin ya gauraye da haske, ko mai na cikin ɗakin white nd silver color ne hatta da capet da bedsheet,kallon agogon da ke kan bed sight  drower ya yi sannan ya tashi zaune yana  zuru kyawawan ƙafafunsa farare tass  kan lallausan capet ɗin dake shimfiɗe tsakiyar ɗakin  sake kallon agogon ya yi a karo na biyu  yana shafa kwantaciyar sumar kansa da take ta zuba shiƙe da ƙamshi yana yamutsata.  Kimanin awaninsa biyu har da rabi chor da kwanciya fa kenan  amma idanunsa samm babu alamun bacci a cikinsu, ɗaya daga cikin wayoyinsa ya jawo ya kamu number Tahir yana danna masa kira.
“Idon ya ɗaga mai zaka ce masa da tsohun daren nan? Ta yiyu ma ya yi bacci zuwa yanzu” wani sashe na zuciyarsa ya tunatar dashi abinda yake shirin yi, katse kiran ya yi yana dafe kansa da ya yi masa nauyi.

Tamkar sukar allura haka yaji mararsa ta tsira masa,   tashi ya yi ya nufi banɗaki yana tafiya tamkar baya son taka ƙasa duk da yanda yaji mararsa na kuma ɗaurewa.
A daddafe ya ɗauro alwala ya fito yana ƙarajin yadda mararsa ke kuma tamkewa Jallabiya fara tass ya zura a jikinsa cike da dauriya ya tada sallah a daddafe ya yi raka'a huɗu saboda yadda mararsa ta kuma riƙewa tana yi masa wani mugun ciwo.

Sosai yake jin jiki don rabonsa da shiga irin wannan halin ya kwana biyu don duk wani abu da zai tada masa da sha'awa ya kan guje masa kuma sosai yake shan magungunan da allurai da likitansa ya ɗorasa akai wanda suke matuƙar taimaka masa duk da yanda likitan ya faɗa masa baza su jima suna yi masa aiki ba saboda zamtuwarsa Mutum mai matuƙar buƙatar iyali, mafita ɗaya kawai ya kuma yin aure saboda kar akai ga lokacin da allura da ƙwayar magani zasu dena yi masa aiki...

Drower da Magungunansa ke ciki ya ƙarasa da ƙyar ya buɗeta, gaba ɗaya ya fito da magunguna da alluran da ke ciki. Allura ya ɗauko ya zuƙa a siringi ya cirata a jikinsa,  sai da ya gama tsiyayata a jikinsa duka sannan ya fitar da ita zuwa lokacin jikinsa har kamar jijiga yake tsabar ciwo.

Bai jima da yin allurar ba jikinsa ya fara fitar da zufa duk da A.C dake ɗakin gurin ƙarfe uku da rabi bacci ya ɗauke shi a gurin mai cike da mafarkai kala-kala.

★★★★★★★★★

JIDDO

Sosai na yi bacci mai cike da mafarkai iri-iri masu sanya farin ciki da tsayawa arai, ko da na tashi farkawa cike da nishaɗi da farin ciki na tashi tamkar wadda aka yiwa albishir da kujerar Makha.

Ko da na shiga banɗaki don gyara jikina sosai mafarkin da na yi da Dadyn Jannat ke dawo min kamar a lokacin na ke yinshi a mafarkin; zaune na ganni ni dashi cikin wani ƙaton lambu da yake cike da shoke-shoke ga wata sassanyar ni'ma dake tashi mai ɗumbin daɗi. Kayan marmari ne shaƙe kan wani babban trey  dake ajiye a gabanmu ya ke ɗauka yana bani  a baki, dai-dai gurin dana gutsira nan yake saitawa shima yana sakawa a bakinsa yana gutsira cike da nishaɗi muke cin kayan itatuwan  yayin da yake tarairayata tamkar ƙwai.
“Monamooo! I love you with all my hert” ya furta min furucin idanunmu cikin na juna yayin da fuskokinmu ke cike da murmushi irin na ƙauna....

Sosai mafarkin ya tsaya min a cikin zuciya da tunanina har na gama gyara  banɗakin na gyara jikina jina nake cikin wani nishaɗi na musamman.

Kasancewar ba sallah zanyi ba yasa na zauna na yi Azkar ɗin safiya sannan na yi tilawar karatun Al-ƙur'ani, na ɗau lokaci ina karatun sannan na yi Addu'o'i na shafa ina mai ruƙon Ubangije Allah ya zaɓa min abinda yake alkairi a rayuwata.
Gadon na gyara tsaf sannan na ɗauko tsintsiya na share ɗakin tas haɗe da goge shi cike da nishaɗi nake komai cire kayan baccin jikina na yi sannan na saka doguwar riga ta atamfa a jikina haɗe da saka ƙaramin hijab ɗin  da na yi sallah dashi   sannan na fito daga ɗakin har sannan Anty Maimuna da alama bata tashi ba  kitchen  na nufa na share shi tas na goge sannan na fara haɗa kayan break fast, ina cikin aikin  Anty Maimuna ta shigo.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now