JIDDO (Gidan aurena) Part 13

5 0 0
                                    


            *JIDDO*
    *GIDAN AURE NA*
               *BY*
  *MAMAN NABEELA*

*Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y

*HAƊAKA PALACE GROUP*

*Page* 1️⃣3️⃣

“Aikinku yana kyau nasarah zatai ta bibiyar rayuwarku, ɗaukaka da shahara zasu zamu a tare daku hhhhhhhh” sautin ya fito daga muryar haɗe da kecewa da mahaukaciyar dariya.

Ƙasa suka ƙarayi da kawonansu tamakar zasu lashi ƙasa kafin daga baya ɗaya bayan ɗaya suka fara tashi suna zuwa gaban wata ƙatuwar jar kujera da amun muryar nan mara daɗi ke fitowa.

Kamar kiftar ido wata mumunar halitta ta bayyana a gurin,  wadda na gaza gane mutumne ko aljan mace kuma ko namiji sanye da jan ƙyale wanda yake iya kwan-kwasonta. Jikinta zane yake da danƙara-danƙaran zanen ƙaton kan dabbar da yake kowane bango dake gurin.

Ɗaya bayan ɗaya kowane ya fara gabatar da aikin da aka bashi har aka zo kan wani jibgegen  Mutum. “Shugaba ayi min afuwa a kuma bani dama wannan ɗin be samu ba, a kuma bani zaɓi ko jinin waye zan kawo” Mutumin ya yi maganar yana daɗa ƙasa da kansa.

Wata mummunar dariya ce ta fara tashi kafin daga bisani aka fara maganar cikin kaushin murya.
“Tabbas jinin Mahaifiyarka muke buƙata guguwa idan har ka kuma ƙin bin Umarni Jinin zuri'arku gaba ɗaya zai zamu fansa ga fada.  BARBUSHE da kansa zai bisu ɗaya bayan ɗaya ya shanye musu jini hhhhhhhhh”

“An gama shugaba” mutumin yayi maganar yana yin baya na kusa dashi ne ya taso baƙi wulik wanda shima  ƙato ne sai uban maiƙo yake ya zube yana baje ƙyalen dake hannunshi wanda yake ɗauke da zanen kan dabbar da yazamu tambarin ƙongiyarsu,  caɓa-caɓa yake da jini aman wani farin abu ya fara yi kamar madara yana gama amayoshi gaba ɗaya kyallen ya haɗu ya dunƙule guri daya yana wata girgiza take jini ya fara fitowa ta jikinsa yana sauka kan wata ƙwarya.
“Aikinka yana kyau Tantiri, ƙongiyar B. B. G (Black Blood Group) tana jin-jina maka, sai da hakan bazai sa ta yafewa wadda ta tarwatsa mana zoben sihiri ba, tabbas zata girbi abinda ta aikataaaaa! Hhhhhh”
Amun muryar ya kuma fitowa, haɗe da dariya kafin kuma daga baya halittar ta ɓace ɓat.......

************

Dukansu ba wanda hankalinsa be tashi da ganin  abinda ke faruwa da Jaririn ba duk inda ake tuninin tashin hankali toh hankalinsu ya kai  ƙololuwar tashi.
Tamkar ƙiftarwar anobar dake tafiya da jinin jiki,   take jikinsa yayi wani irin haske kamar ba'a taɓɓa halitar jini a jikinsa ba.

Gaba ɗaya tashin hankalin da suke ciki yasa sun rasa me zasu fara yiwa ɗan talikin dan ceton rayuwarsa.

Mitunan da basu gaza biyar ba Jariri Hussain yace ga garinku nan.

Jiddo tun da ya fara Jijigar na nemi hankalina na rasa bansan sanda Ummansu Harisu ta karɓi Hussain daga hannuna ba,  na zama tamkar butun-butumi.
Yayinda Kafatanin jikina,  nake jin kamar ana zuƙe min wani abu a ciki, tamkar wanda tayi baci ko ta farko daga suma haka sautin kukansu ya shiga kunena haɗe da jijigani da ake. Zabura nayi kamar me taɓin ƙwaƙwalwa.

Na fara waige-waige ina cewa“kai lafiya naga kuna kuka?  ina Hussain? Yanzu nayi mafarki yana jijiga”

Asma'u da Salma kukan suka kuma saki harda su Zainab da Abdull da ban san sanda suka dawo ɗakin ba.

Umman Harisu na kalla naga ita ma kamar hawayin take cike da tashin hankali na kalli hannunta da take miƙo min Hussain, karɓashi nayi ina kallonshi   irin farin da ya ƙara kamar ba jini a jikinshi.

“Me ya sameshi? Dan Allah karku ce min ya mutu! Dama haka ake mutuwar? ” Nayi maganar cike da firgici kamar zararriya.

“Jiddo sai dai muyi haƙuri Allahn daya ba mushi ya karɓi abinsa, Allah yaji ƙanka Hussain ya gafarta maka. Na daɗe banga yaro me saurin  shiga rai tuna yana jariri ba kamar Hussain Allah yasa me cetonmu ne kai ɗin” Lubabatu tayi maganar tana kuka haɗi da fyace majina.
Ban taɓɓa sanin haka ake tsintar kai cikin  tashin hankalin rasa wani naka ba sai akan Hussain. Yaron da tun da na ɗora idona akansa bayan cirominshi  soyayyarsa ta zamu ta daban a zuciyata, a kullum kuma ƙara hauhawa take cikin raina.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now