JIDDO (Gidan aurena) Part 27

4 0 0
                                    

*JIDDO*
(Gidan Aurena)

_Story by_

*MAMAN NABEELA*

(_TEAM JAJURTATU 6_)
*BAYAN RAI (KHADIJA ISHAQ)*
*JIDDO GIDAN AURENA(MAMAN NABEELA)*
*JINANE(ZAITUN MAMAN FAUZAN)*
*IN BA KAI(OUM AFREEN)*
*SAIFUL ISLAM(OUM AMRA)*
*NURHAAN(SHUATY)*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*HAƊAKA PALACE GROUP*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*

'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''

*PAGE* 2️⃣7️⃣

“Da sauƙi Salma ya su Ummanku?” Na amsa gaisuwarta ina tambayarta.

“Lafiya lau Ammey,  sai dai gidan fa ba daɗi da bakya nan” salma tayi maganar tana karyar da kai.

“Aikuwa gwanda ma ku saba don ita dai Allah ya yanke mata sake komawa gidanku” Azima tayi saurin tarar numfashinta tana maganar haɗe da zabga mata harar.

“Azima kanki ɗaya kuwa mai nene haka ki ke yi? ” Anna tayi maganar saboda ba wanda bai ga harar da ta yi wa Salma ba.

“To!To!! Ni Anna mai na yi    amsa fa kawai na bata” Azima ta yi maganar tana turo baki gaba don ita fa yanzu bata ƙaunar ko ganin wanda ya haɗa hanya da Suwiɗi ko su Asma'u ma bata ko sun ta tuna shi ne mahaifinsu.

“Ba dai na son irin haka ki tashi ki kawo musu abinci da ruwa kuma” Anna ta yi maganar fuskarta babu alamun wasa.

Tashi ta yi ta nufi kicin tana kuma turo ɗan ƙaramin  bakinta irin na JIDDO.

“Anna da kin kyale abincin mun ci a gida kafin mu taho” Salma ta yi maganar zuciyarta cike da tunanin maganar da Azima ta faɗa yanzu,mai hakan ke nufi! Ko dai sakinta Baba Malan yayi?. Ta yi maganar cikin ranta...

Anna ta buɗe baki za ta yi magana sallamar Asma'u  da ta dawo daga gidan Ummar sani fage karɓo ruwan Addu'a, tasa ta da kata.

Da gudu Zainab da Abdull suka ruga suna rungume ta.

“Oyoyo Anty Asma'u” suka haɗa baki suna faɗe.

“oyoyo ƴan albarka yau shi kuka zo? ” Asma'u tayi maganar tana kama
hannunsu suka nufi tabarmar da suke zaune.

“Yanzu  muka zo”Abdull ya bata amsa lokacin da take zama gefen Ammeyn su.

Anna ta miƙawa robobin rubutun tana amsa sannun da muka yi mata.

“Beisty ai yanzu nake shirin tambayar ina ki ke sai ga sallamar ki” Salma ta yi maganar tana dariya.

“Ke dai faɗi gaskiya abinda tunda na taho ko kirana ba kiyi ba”Asma'u ta yi maganar tana yi mata hara rar wasa.

“Allah kuwa kin san halin gidan namu katin sakawa ma a wayar wuya yake kuma wayar tawa ma wallahi lalace wa ta yi, ko Umma tana son ta samu wayar da zata kira taji ya jikin Ammey amma bata samu ba kin dai san halin Baba yanzu ma bai san munzu nan ba ” Salma ta yi maganar tana kallon Asma'u.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now