JIDDO (Gidan aurena) Part 23

4 0 0
                                    

*JIDDO*
(Gidan Aurena)

_Story by_

*MAMAN NABEELA*

(_TEAM JAJURTATU 5_)

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*HAƊAKA PALACE GROUP*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*
_Sannan da  akwaI airtime   na;MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE_

'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''

Page 2️⃣3️⃣

Kwana biyu da kawo ni gida jikina ya fara kyau don muryata sosai yanzu tana fitowa sakamakon yadda nake samun kulawa sosai. Saukar alƙur'ani kuwa kullum sai anyi ba sau ɗaya ba dan almajirai Baba yasa suke saukewa ana basu sadaka, hatta ruwan da nake sha bayan dawo wata zam-zam Babanmu ya siyo ake haɗɗashi da ganyen magarya ana karanta ayoyin  karya sihiri a ciki ya zama ruwan sha na.

Duk wanda ya shigo yaga yadda na koma sai ya zubda hawaye, Suwiɗi kuwa babu mai yi masa Addu'ar alkairi  dan sosai mutane ke la'antarsa da yi masa mugayen Addu'o'i.

Baba tsohu kullum sai yazo gidan tunda na dawo  yana ruƙon na yafe masa,  a  cewarshi shi yayi sandin shigata duk halin da na shiga daya haɗa aurena da Suwiɗi ba tare da wani ƙwa-ƙwaran bincike a kansa ba.

Sosai ya bani tausayi ganin duk  ya damu da irin halin da nake ciki, duk da shi ɗin yana da iko a kaina amma yake neman yafiyata harda zubda hawaye.

  Cikin hawayen daya suma zubowa daga fuskata  nace masa na yafe masa,ya kuma dena faɗar haka Allah ne ya ƙaddara aurena da Suwiɗi na cikin ƙaddarata.

Yau ma kamar kullum tun bayan da aka dawo dani gida sai ga Baba tsohu da kawo Auwalu sunzu, bayan Anna ta gaishisu suke tambar jikina tace musu da sauƙi.
Gaishesu Azima tayi bayan sun amsa nima da nake zaune an jigina ni da bango na gaishesu suka amsa suka yi min ya jiki nace da sauƙi'.
Baba tsohune ya miƙawa Anna wata leda yana cewa“Halima ungo wannan ki fara yi mata shi maganin irin larurarta ne da na yiwa   abokina Baushe bayani ya  haɗamin da bayanin yadda za'ayi amfani dashi duk a ciki in kin duba, ki fara yi mata daga yau sannan duk abinda kika ga tayi karki tsorata ki cigaba da yi mata zuwa jibi idan ya haɗa sauran zaizo da kansa ya kawo sannan yaga yanayin jikin nata”
Baba tsohu yayi maganar yana miƙa mata ledar.

Karɓa Anna tayi tana cewa „toh Baba angode Allah ya ƙara girma, insha'Allahu zan yi mata”Anna tayi maganar tana karɓa.

Basu jima da zuwa ba sai ga Baba da Yaya Ahmad suma sun dawo,  a lokacin ne naji suna maganar kai ƙarar Suwiɗi da Yaya Ahmad yayi saboda yaje har gida washe garin da aka dawo dani yace ya sakeni yace bazai sakeniba.  Mamaki ya kamani jin duk sun bashi goyon baya wannan karon  har suna yin maganar ɗaukan Lauya.

Suna cikin tattaunawar aka kira wayar Yaya Ahmad, bayan ya gama amsa wayar naji yana cewa da su ya ƙaraso ban san ko waye ya ƙaraso ba amma ina kyauta zaton yana da nasaba da case ɗina.

Tashi su kayi gaba ɗayansu suka fita bayan fitarsu ne Anna ke bani labarin irin rigimar da Yaya Ahmad da Suwiɗi suka kuma yi wannan karon ma da yaje masa da maganar sakina, har yana faɗin bai ga wanda ya isa yasa ya sakeni ba ko da kuwa wannan ruɓɓaɓen tsohun ne da yayi sanadin auren.

  Sosai ran  Yaya Ahmad ya kuma  ɓaci wanda sanadin hakan ya shigar da ƙararsa,  take aka turasu kotu  bayan an turawa Suwiɗi takardar gayyata,  wanda zuwa ranar Litinin za'a fara sauraran ƙarar.

Naji daɗi maganar sosai don ni kaina ahalin yanzu  idan na tuna da auren Suwiɗi a kaina nakanji kamar zuciyata zata buga don ƙonci.

★★★★★★★

Suwiɗi lokacin da Ahmad Yayan Jiddo ya bar gidan bayan ya gama yi masa maganar ya saki jiddo, wata kafurar dariya ya saki yana faɗi a fili
“tabbas ko zan sake ki Jiddo sai na tatse duk ɗan arziƙin danginku” yayi Maganar yana sheƙewa da dariyar mugunta.

“Ni da nayi Maganin Jazuli ma bare ku ƙananun alhaki”ya kuma maganar yana kuma tuntsirewa da dariya.

Jazuli lokacin da ya dage  kan ya dawo gidan kenan,  sai Suwiɗi ya rabu dashi yayi kamar ya kyaleshi yayi shigewarsa cikin gida.

Ɗakinsa ya shige harda murza key, sannan ya durƙosa ƙasan gadonsa ya ciro wata baƙar akwati ya buɗeta.

Wani jan kyallene ya bayyana take ya yayeshi wani abu kamar mudubi ya bayyana ɗagoshi yayi yana karanto wani yare take wata kujera ta bayyana ɗauke da shugaban ƙongiyarsu zaune akanta.

Ƙasa ya kuma yi da kansa cike da girmamawa yana cewa“shugabanmu maganin kukanmu, duk wanda yazo gareka damuwarsa ta ƙare" Suwiɗi yayi maganar yana ƙara yin ƙasa da kanshi kamar zai sijjada.

“Hhhhhh! Mai cece damuwarka? Yanzu ayi maka maganinta” sautin wata mummunar murya ya fito daga cikin mudubin haɗe da dariya. 

“Ina so a nisanta tantiri da gidan nan saboda zamansa babbar matsala ne gareni don ya fara bani matsala tun yau, ƙarashen aikin da zan ƙarasa ma ya rusa min shi.” Suwiɗi yayi maganar cike da girmamawa har sannan kansa a ƙasa......

'''🤔Oh ni ƴasu Suwiɗi anya kuwa! Ba nayi ta kaina na gudu kar ka juyu  ka gani kace ina yi maka laɓe 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️

Allah ka tsaremu aikata shirka kasa mufi ƙarfin zuƙatanmu, masu hali irin na Suwiɗi Allah ka shiryesu in masu shiryuwane Allahumma amin.'''

 
_Pls share & comments Habibaty_ 🙏🙏🙏

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now