JIDDO (Gidan aurena) Part 14

5 0 0
                                    


           *JIDDO*
    *GIDAN AURE NA*
               *BY*
  *MAMAN NABEELA*

*Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y

_Chat me on_ :07042808467

*Page* 1️⃣4️⃣

Fiton da sautinsa ke ƙara kusanto mu yasa gaba ɗaya hankulanmu ya ƙara komawa ƙofar shigowa.

Wasu ƙosasun riɗa-riɗan karnuka da suka shigo kusa guda biyar, suna zazzaro hareshe idanunmu suka sauka a kansu.

Wancakalar da zogalen da muke figa Ummansu Harisu tayi tana kwasa da gudu tayi hanyar ɗakinta ta shiga ta banke.
Duk da bana ko ƙaunar ganin kare dan mugun tsoransa nake ban motsa daga gurin da nake ba. Jazuli ne ya shigo yana riƙe da sarƙar dake wuyan karnukan shigar jikinsa babu kyan gani,  ga wani irin aski irin na tantirai a kansa.

“U.... u..wata sa..sa..nu da gida, ai i..ina ta...taso na...naje ha...har A...asibiti na...na...duba ki A...Allah be...beyi ba, sai...sai ya... yanzu Ya...yarooonna ya...yake fa...faɗaaa min kin...kin da.. dawo ” Jazuli yayi min maganar yana nufar wani tirke dake nesa da ni kaɗan ya ɗauresu.

Dawo wa yayi gurin da nake ya zauna banda tashin warin shaye-shaye babu abinda yake, tausayin halin da ya tsinci kansa a ciki na shaye-shaye ya daɗa kamani a zuciyata ina yi masa adu'ar shiriya murmushi nayi ina cewa “Ai saƙon dubiyarka ya iso gareni Jazuli, daga ina kake haka na ganka da waɗɗan nan tiƙa-tiƙan karnukan?  kasan fa Malan bayaso kana zuwa dasu! ” nayi maganar ina kwashe zogalen da Ummansu Harisu ta zubar.

“Da...da...daga ma...majaliisa ma...mana, ga...gaisuwa su...suma za...za suyi.    Wai....wai wa ya...ya mutu a...a gidan nan? a...a...an ce mu....mun a...anyi mu...mutuwa na...na...ɗauka ma shi....shi ya...ya wula,  na...nazo a...araba ga..gado abani ka...kasuna. ”

Idanuna na zaro ina kallonshi cike da mamaki n maganar shi nace“Jazuli mahaifin naka kake faɗin kayi tunanin shi ya mutu kazo abaka kasun ka na gado?

“Eh! Ma...mana wai...wai waye ya...ya mutu to..toh? Ku..kuma ba ku...kuda wa...wani abin ta...taɓaaawa ne a...a...gidan? ” Jazuli ya kuma yi min maganar kai tsaye cikin muryarsa ta in-ina ba tare da wata damuwa ba.

“Ƙaninku ne da aka yimin tiyata aka ciro Allah ya yiwa rasuwa” nayi masa maganar ina tashi na nufi ɗaki na na ɗauko masa abinci.

“Kai dai wallahi anyi tambaɗaɗe, inba gantalewa ba ƙaton gardi kamar ka ya zauna yana jiran gado! Ko kunya baka ji kuma kake neman abinci toh!  Nawa ka kawo da za'a ɗibi abinci abaka? Oh!  Ko da yake naji labarin ance ɗauke-ɗauken da kuke ƴan Bijilanti sun fara taka muku burki suna lallasaku.  Toh mudai bamu da abincin bawa ƙaton banza dan haka sai a tashi a nemi na kai kar rayuwa ta ƙare a ɓal-ɓance babu tsuntsu ba tarko”Lubabatu dake zuru kanta ta wendon ɗakinta ke maganar tana wurgo masa harar.

“Wa....wa...wallahi ma...matar nan in....in...baki fita da...da....daga harka ta ba sai.....sai na....na saka Migyambo da....da Bingo su...su...sun miki ya....ya...yagun rashin mu.....mutunci su....sun miki ka....kaca-kaca, in....in....in kuma ki.....kin i...isa ki....ki fito ki....ki gani! " Jazuliyayi maganar yana cicije baki yana kallon inda take.

Fitowa nayi da kwanon abinci a hannuna naji rigimar da akeyi tsakanin Jazuli da Ummansu Harisu miƙa masa kwanon abincin nayi ya karba ya fara ci babu ko bissimillah, janye kwanon abinci nayi ina cewa“Haba Jazuli kai da nake adu'ar ka dawo hanya ka ringa tsawatarwa da ƙanenka in sunyi ba dai-dai ba! Ya ya kuma cin abinci babu ko bissimilah itafa bissimilah tana saka abinci yayi albarka ko da kaɗanne idan kayi kaci,  sai Allah yayi masa albarkar da zaka ji ka ƙoshi. Dan Allah ka dinga yin  bissimillah idan zaka ci abu ko zaka sha kaji? ”
Nayi maganar ina mayar masa da kwanon gabansa.

“Na...na gode ke...ke...ka...ka...ɗai ce kike fa....faɗamin na...na...nayi ba dai-dai ba. Za...zan di...dinga yi ku...kuma” Jazuli yayi min maganar yana yin bissimilah ya ci gaba da cin abincin.

“Oh! Ni Lubabatu ina ganin abu duk sanda yazo ko gajiya bakyayi kamar  uwarsa gurin gwalan gwasun nuna masa yayi kaza ya bar kaza amma da ya tashi yake watsar da abinda kika faɗa masa. Yoh ni da wata tsiya ce dashi sai nace murarsa kike, Allah ma dai ya kiyaye ƴaƴanmu su zauna wannan tantirin yayi musu faɗan sunyi ba dai-dai ba, can kaje ka ƙare da faɗa da ƙwayar wiwi da sholisho dama su aka haifuwa kai” Lubabatu da bata matsa daga jikin windon ba ta kuma tsumo baki tana kwaɓowa Jazuli  maganar.

“Haba Ummansu Harisu haka fa ba girmanki bane ai Ɗa na kuwa ne ba wai sai wanda ka haifa ba ki dena faɗar haka shima ai bashi ya ɗorawa kansa ba Allah ya kan iya yayi masa a sanda yasu ya jarrabi wanda kuma ba'ayi zato ba a sanda yasu, dan Allah ki dena faɗar haka!” Nayi maganar cike da takaicin abinda take faɗa.

Ina gama maganar naji ƙarar abu kamar dutse,da ihun Ummansu Harisu.  Kallon Jazuli nayi da yake cika yana batsewa idanunsa sunyi jajir yana ƙoƙarin kuma saita wani dutsen nayi saurin riƙe hannunsa ina dakatar dashi.

“Wayyooo! Bakina Allah ya tsine maka shige gantalalen Insha'Allahu a haka zaka ƙare tambaɗaɗe kuma wallahi bari su Harisu su dawo wallahi sai sun saka an kulleka gantalale dabe tsinanawa kansa komai ba bare ya tsinanawa wani” Lubabatu tayi maganar dafe da bakinta da nan take ya kumbura yayi suntum saboda dutsen a saitin bakinta  ya sauka.

Rintse idanunsa yayi da suka ƙara yin ja ya tashi yayi hanyar ɗakin Lubabatu yana zaro wata sharbebiyar wuƙa.

Saurin bin bayansa nayi ina faɗin “innalilahi wa inna ilaihirrajiun Jazuli me zaka yi haka?  Dan Allah dan ma'aikin Allah ka mayar da wannan abar” nayi maganar ina ƙoƙarin dakatar dashi.

“Wa...wallahi na...na rantse da...da sarkin da...da ya bu....busan  numfashi sai...sai na...na keta ma....mata rigar ra...rashin mutunci, ya...yanda ko....ko inuwata ce...ce ta...tazo guri ba...ba zata sa...sake  gi....gi...gin yi mata ka....karanbani ba”

Duk yanda na kai ga magiyar karya karya ƙofar Ɗakin Ummasu Harisu ƙin haƙura yayi dan ran ƴan Maza ya ɓaci.

Ganin ya fara ƙoƙarin karya ƙofar duk ban haƙuri na yaƙi haƙura nayi hanyar soru tuna wani Lokacin yana zuwa da wasu a cikin yaransa.
Ina lekawa kuwa na hango yaronsa da naji yana kira da Nakati na yafitoshi da hannu zuwa yayi nayi masa bayanin abinda yake faruwa, wanda suke tare ya kuma ya yiwa magana suka tahu tare shiga cikin gidan suka yi ina bayansu da kyar da suɗin goshi suka samu suka ƙwace wuƙar hannunsa suka yi waje dashi yana tuturjewa. 

Ajiyar zuciya na sauke ina nufar ɗakina ko da na shiga ban jima ba na fito na ɗauki buta na nufi banɗaki, ina fitowa Lubabatu na fitowa daga ɗakinta baki suntum tana  raba idanu tana kalle-kalle....... ✍️

''''Wallahi naso nayi muku da yawa amma gaba ɗaya kwanakin nan bana samun lokaci, yanzu ma dan kar kuji shiru ne yasa nayi squeezing time nayi muku. '''🙏

_Pls share & comments_ 🙏🙏🙏


*MAMAN NABEELA CE...* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now