JIDDO (Gidan Aurena) part2

28 0 0
                                    

*JIDDO*
    (_Gidan Aurena_)

          *STORY*&

               *BY*

*M@M@N N@BEEL@*
   
*Dashen Allah writers association*

_Ina kuke 'yan kasuwa Maza da Mata ga dama ta samu, ga mai son a tallata masa hajarsa cikin farashi me sauk'e da rahusa sai ya tuntu'beni ta wagga number.👇_
07042808467

_JIDDO LABARI_ me d'auke da darrusa masu d'umbin yawa....

*H-P PALACE GROUP*

Bismillahirrahamanirrahim

Babi na biyu

__________Kukan yaran yasa Lubabatu dawo wa haiyyacinta shaf rud'o yasa ta manta suna
gurin,  rasa ta ina zata fara lallashinsu tayi ta zuba musu ido kawai tana tunanin abinyi.
Sallamar Maln Suwid'i da Salma yasa ta saurin kallon 'Kofa.
Buguzum-buguzum Maln Suwid'i ya k'arasu gurin da suke Babbar rigar jikinshi har neman kadashi take  wuyansa ga wani k'aton charbi, ba'kar fuskarsa me d'auke da dara-daran  tsagu sai maik'o take jajayen idanonsa ya zube kan Jiddo dake kwance kamar gawa, k'an'kance k'ananun  idanonsa yayi yana duban Lubabatu yace"ke Luba me Salma Ke fad'amin haka!, suma tayi ko me? Da har kuke fad'in ta mutu?"

Tabbas tasan ko rantsuwa tayi ba za tayi kaffara ba da ba'a ce ta mutu ba ba zai zo ba.

Sharce hawayin fuskarta Lubabatu tayi tana Cewa "Maln ina zaune ni da Salma   kawai muka ji fad'owarta,Malan  mun shiga uku kaja mana masifa ina tsuron mutuwa ta ina tsuron Amadun Jiddo wallahi yana samun labarin Jiddo ta mutu sawa zaiyi a kamamu,tun da dama ya fad'a maka duk abinda ya sameta ba zai bari ba. Malan ka tai maka ka samu mota mu kaita Asibiti ko Allah zai sa in  dogun suma tayi ta far fad'o!"
Lubabatu ta Kai k'arshin zanchan tana jan Majina.
k'ara k'ank'ance idanuwansa Malan Suwid'i yayi yana cewa"kaji zanchan banza Lubabatu ruwa aikin me yake da baza ki kwara mata ba ? Au Had'a Baki Ku kayi A tunaninki k'wandala  zata fita daga aljihuna,har kike batun zuwa Asibiti!,toh tun wuri ma gwara kisa ta farka in suman k'arya tayi  dan sisina bazan kashe ba.
Mata nawa ne suke ciki su haihu ko k'ofar gida basu lek'a ba bare wani zuwa  asibiti!".

"Suwid'i kaji tsorun Allah,yanzu wannan halin da Jiddo ke ciki yayi maka kama da chutar k'arya,in ba rashin son a fad'i gaskiya ba  har kace mun had'a baki da Jiddo, da kake maganar matan da basa zuwa asibiti, yanzu da da ai ba d'aya bane.ko ni  wahalar da nayi ta sha a haihuwa, jini ya 'balle min nayi kamar na mutu   nasan badan Allah yayi ina da sauran shan ruwa ba da tuni wani zanchan ake . Toh na rantse da Allah babu ruwana kiran Iyayenta zanyi na sanar dasu....."

Cikin fad'a ya katseta yana fad'in"Lubabatu saboda kinga ina kyaleki duk abinda kike shine kika samu bakin fad'amin abinda kikaga dama,toh kije ki fad'awa ko ma Uban waye indai ni zan kaita asibitin sai  dai ta mutu,kuma da kike ciwa naji tsorun Allah da tsorun ki zanji wallahi Lubabatu In baki kiyayeni ba abinda zan aikata miki Allah kad'ai ya sa......."

Sallamar da aka rafko tare da shigowa yasa maganar Malan Suwid'i katsewa.
Maimuna ce yayar Jiddo ta shigo cikin gidan da gudu Asma'u da k'aneneta sukayi kanta rungumeta sukayi suna dad'a sakin kuka.
Cikin tashin hankali take duban yaran yadda suka mak'alk'aleta suna kuka me ta'b'ba zuciya,zabura tayi tana tunu irin mugayen mafarkan da kwanakin nan take ta yi da 'Yar'uwarta Jiddu, wanda sune silar tahuwarta tun daga kaduna inda take Aure,sakamakon hankalinta da yak'e kwanciya ko gidansu bata je ba Direct tace Drivern daya kawota suyo nan. Cikin sar'kewar harshe tace"Husn....nah! lafiya meke faruwa? Ina Ammeyn taku?"

"Momy ga ta chan a kwance,bata motsi Ummansu Salma tace wai ta mutu.Momy dan Allah kizo kice taa tashi karta mutu!".
Asma'u tayi maganar tana  k'ara sakin kuka.

Momy Maimuna tana jin furucin Asma'u jakar hannunta ta saki k'asa a sukwane ta nufi gurin da Lubabatu da Suwid'i suke,dan ita shaf bata kula ma dasu ba bare wadda ke kwance a gabansu  sai  da Asma'u tayi maganar, dire Guwwoyinta 'Kasa tayi tana tallafu kanta dake cinyar Lubabatu, hanunta ta kai kan jijiyar wuyan Jiddo jin tana harbawa cikin sauri tace"Husnah maza kirawo min 'Danladi Driver yazo ya taimaka mana mu d'auketa muje  asibiti bata mutu ba".

Asma'u da gudu tayi waje kiran 'Danladi Drive.

"Ke! Memuna gidanwa kike fad'in k'aton gardi ya shigo, babu ko neman izini ?"

Suwid'i yayi maganar yana k'ara had'e fuska.

Momy Maimuna wani kallon shek'ek'e ta yiwa Suwid'i tana cewa "izini kake magana,gurinwa zan nemi izinin? Dama ka d'auki iyalinka da darajar da zakayi kishinsu,oh da yake ka gaji da ita kana son ganin bayanta shene bak'ar muguntarka zata sa ka fad'i haka! bari kaji wannan karon wallahi bazamu zuba ido ka k'arasa kashe mana Jiddo ba, Yarinya k'arama sanadinka har hawan jini gareta."

Jikin Suwid'i har tsuma yake na 'bacin rai,tamkar zai kaiwa Maimuna duka ya fara balbala masifa idanonsa har rufewa suke "Ke fitsarariya ko me zaki fad'a gida nawa ne karki ga kina auren d'an majalisa kiyi tunanin zuwa har gidana ki fad'an abinda kika ga dama.Jiddo matatace idan naga dama babu uban da zai fita da ita daga gidan nan"

Lubabatu ganin cecekuce tsakanin Suwid'i da Maimuna na k'ara gaba ga jini ya fara biyu 'kafar Jiddo, yasa tayi Saurin rik'o hannun Maimuna dake k'ok'arin mayarwa da Suwid'i martani.
"Haba Memuna ko kin manta halin da 'yar uwarki ke ciki ne duba kiga jini Ke biyu k'afarta yanzu mu fara nema mata lafiya daga baya ayi duk abinda za'a..."

"Innalilahi wa inna ilaihir rajiun, wallahi baza mu yafe maka ba,mugu,azzalumi  " Maimuna ta fad'a tana yin kan jiddo manya-manyan idanuwanta irin na Jiddo da suka gado gurin maifiyarsu na k'ara girma tsabar tashin hankali.
Cike da k'arfin hali ta cici'beta ita da Salma suka nufi hanyar waje,a cikin soru sukai kacibus da Asma'u da 'Danladi.
" 'Danladi koma ka bud'e mana mota", da sauri 'Danladi ya juya yana fad'in "toh Hajiya....."

To be continue...✍️

_Pls shere and shere and shere Habibatis_ 🥰🥰🥰

*Maman Nabeela ce*✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Donde viven las historias. Descúbrelo ahora