JIDDO (Gidan aurena) Part 20

6 0 0
                                    


            *JIDDO*
    *GIDAN AURE NA*
               *BY*
  *MAMAN NABEELA*
 

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*

7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank

*Page* 2️⃣0️⃣

_______Suwiɗi zare idanunsa yayi yana jijiga kai  haɗe da  ke cewa da wata mahaukaciyar dariya yana cewa“ke ni zaki yiwa ƙaryar Aljanu!  Dan ubanki ko angaya miki ni ɗin ina tsoransu ne? Har   kike kira na ƙaramin alhaki?  A matsayina na ubanki!” Yayi maganar yana tashi daga gurin da yake cikin faɗa.

“Au! Kai har ka isa muyi maka ƙarya!, Toh yanzu zamu nuna maka zahiri a aikace...” tayi maganar tana daga inda take har sannan bata motsa ba.

Dariya ya daɗa kece wa da ita yana cewa“kun daɗe baku nuna min zahirin ba an gaya muku ni ko fitowa kuka yi muraran zaku firgi..... ”

Cak maganar Suwiɗi ta ɗauke ji kake kauuu-kauuu ƙarar sautin mari na tashi, tamkar wata fanka haka Suwiɗi ya fara juyawa yana dafe kuncinsa. Da ya saka hannunsa a kuncin hagu sai yaji mari a kuncinsa na dama  ya daddage zai kurma ihu bakin ya tsaya cak a buɗe bai ankara ba jikake hajijiya ta kwashe shi ya faɗi  timm. Yana faɗowa ƙafarshi tayi wani irin ƙara ta karaya, sai a lokacin ya iyayen wani kafirin ihu da ya cika gidan gaba ɗaya.

Har rige-rige ake gurin shigowa tsakanin Lubabatu da su Salma, Harisu ma yau da be fita da wuri ba sai gashi cikin ɗakin kamar an hankaɗo shi ya shigo.
Gaba ɗaya suka yi kan Asma'u da idanunsu suka sauka a kanta ganinta shimfiɗe a ƙasa...

Suwiɗi ne ya daddage ya kuma zunduma ihu jin ana kuma zuba masa bulalai a jikinsa.
Da gudu Harisu yayi kansa yana faɗin “Baba lafiya!  Mai ya sameka? ”
Harisu yayi maganar yana kamashi ganin yana ta mutsu-mutsu,   zaro idanunsa yayi lokacin da idanunsa suka sauka fuskarshi, ganin yadda fuskar Baban nasa tayi wani mugun kumburi tamakar fulawar da tasha yeast yana kuma tambayar mai yake faruwa?

Su Lubabatu ma duk gurin suka dawo suna tambayar mai yake faruwa cike da tashin hankalin ganin yadda fuskar Suwiɗi ta koma kamar wanda yayi axcident.

Suwiɗi babu bakin magana dan sai uwar zufa yake haɗawa tsabar azaba  tamakar wanda ya haɗiyi Kunama. Kamashi Harisu ya fara ƙoƙarin yi!  Ya ɗagashi ganin yaƙi magana sai gumi ne yake tsiyaya a jikinshi.
Suwiɗi girgiza masa kai kawai yake alamar kar ya ɗagashi,  amma Harisu bai fahimci mai yake nufi ba ya ɗagashi. Wata razananneyar ƙara ya saki yana lokacin da Harisu ya ɗagashi wadda tasa Harisu sakinshi ba shiri take ya kuma faɗuwa ƙafar ta kuma yin ƙara ya sume a gurin.

JIDDO
“Wai mai yake faruwa nayi maganar ina daga gurin da nake kwance wanda tun da ga sanda naji magan-ganun da Asma'u da Suwiɗi suka yi na cika da tashin hankali ina faɗin Aljanu kuma a jikin Asma'u? Wanda ni tunda nake da ita ban taɓɓa ganin wata alama ta jinnu a tare da ita ba.
Ganin Suwiɗi yana katantanwa yana dafe kunci hankalina ya ƙara tashi ina daga kwance na rasa ya ya zanyi gashi duk maganar da nake basa jina saboda har sannan muryata bata fita da kyau Salma ce ta matso kusa da gadona na kuma mai-maita tambayar da nayi ta mai yake faruwa?  Allah yasa ta ji ni ta juyu tana cewa“Ammey Babane fa da alama karyewa yayi! Ko da zai fita ya faɗi!  Bamu sani ba amma gashi nan kamar wanda yasha duka fuskarsa duk ta kumbura”.

Ina daga kwance na cika da al'ajabin abinda ya faru wani sashe na zuciyata na murna yayin da wani ɓangaren kuma ke jin rashin daɗin lamarin.

Sai da Harisu ya kira Mai gadi ya temaka masa sannan suka ɗauki Suwiɗi aka fitar dashi falo,  wanda zuwa lokacin ƙafar Suwiɗi ta kumbura sosai.
Mai gadi na ganin ƙafar yace karaya ce da alama ma ba karaya ɗaya ba dan haka a nemo mai gyara, Harisu ne ya tafi ya nemo mai gyaran karaya wanda zuwa lokacin Lubabatu ta shafa masa ruwa ya far-faɗo.

Ana fara gyaran ƙafar Suwiɗi ya fara zunduma ihu yana tsinewa Aljanun Asma'u haɗe da cin alwashin ba zai kyalesu ba. Sai a lokaci su Lubabatu suka san menene sandin koma warsa haka! Wa toh aljanun Asma'u ne suka yi masa aika-aika.

Yasha ihu kamar ba Babba ba kafin a gama gyaran ana gamawa bacin wahala ya kwashe shi a gurin.

JIDDO
Bayan fitarsu ina kwance har sannan ina jin-jina abinda ya faru motsin Asma'u da ta fara yasa na juya kaina gurin da Salma ta dawo da ita ta kwantar.
“Ammey yaushe nayi baci? Wa ya kawo ni nan? Ina Baba har ya fita ne? ” tayi maganar tana kallona.

Rasa mai zan cemata nayi saboda na daɗa tabbatar da Aljanu ne suka shiga jikin Asma'u na tausayinta ya kamani idanuna suka fara tsatsafu ruwan hawaye nace mata “ya fita”

Tashi tayi ta shiga banɗaki bayan ta fito ta gyara min kwanciyata tana tambayata ko ina buƙatar wani abun na gir-giza mata kai Ruwa ta ɗauko tayi min Addu'o'i a ciki ta ɗago kaina ta bani sannan ta fita falo.

Suwiɗi ne kaɗai kwance a falon  yana bacin wahala take idanunta suka sauya kala ta nufi gurinshi, tana zuwa yana buɗe idanunshi.
Zabura yayi zai yi ihu  ta sakar masa wani mugun murmushi tana ɗora hannunta a saman baki
“shiiii”ta furta tana kecewa da dariya kafin ta gintse fuska ta ƙara gaban kujerar ta durƙusa ƙasa-ƙasa ta fara magana“Shaiɗani ina sheɗancin naka yau bari kaji idan har baka war-ware abinda kayi mata ba baka fara shan wahala ba ma tukunna dan ni da kake gani duk wani Azzalumi na kan iya maganinsa!” tayi maganar tana zuba wani makirin murmushi.

“Baba mai ya sameka?  daga bene ka faɗo?”ta sauya a kalar maganarta ganin fitowar Lubabatu tana matso hawaye.

“Asama'u kin tashi! ”Ummansu Harisu tayi maganar tana ƙarasuwa cikin falon.

“Eh! Mai ya samu Baba haka! Hatsari yayi? ” ta kuma yin maganar tana ƙin kallon Lubabatu saboda kar ta gane ba asalin Asma'u bace.

“Toh gashi nan dai har yanzu bamu san mai ya sameshi ba yaƙi faɗa mana”Lubabatu tayi maganar tana zama kujerar dake can gefe da su.

Wani murmushi ta jefawa Suwiɗi tana tashi tace “toh Allah ya kyauta nufi ɗakin da suke kwana.

Lubabatu sakin baki tayi tana kallonta har ta shige saboda taga sanda take yiwa Suwiɗi murmushi tana yin wata alama da hannu. “Na shiga uku ni ɗiyar Barau Yarinyar nan yanzu fa shikenan ta zama rabi Mutum rabi Aljan dan da alama yanzu ma ba ita bace Aljanunta ne! ” Lubabatu tayi maganar cikin ranta tana daɗa kallon ɗakin da ta shiga.

Suwiɗi mugun mamaki ne ya kamashi jin lokaci guda ta koma  tambayar mai ya sameshi cikin tausayawa, dama Aljanu ma sun iya makirici yayi maganar cikin ranshi har bai san sanda ta bar gurin ba.

★★★★★★

Kwana uku da karyewar Suwiɗi wasu mutane suka zo suka ɗaukeshi suka tafi dashi a Mota Ranar su Asma'u sun tafi makaranta Ummansu Harisu kuma ta shigo ɗakina tana fita taga bata ganshi ba duk inda ta duba baya nan daga ƙarshe taje gurin mai gadi tana tambayarsa yake faɗa mata Uban gidansa ne ya turo aka ɗaukeshi. Ta cika da mamakin waye Uban gidans? Dan ita bata san yana da wani mai gida ba haka ta koma cikon gidan ta faɗawa Jiddo yadda suka yi da mai gadi.

Banyi mamaki ba dan nasan  ba wani Uban gida bane sai na gurin tsafe-tsafensu Addu'ar neman tsari daga sharinsu na ringa yi ina fatan Allah ya kawo ɗaya cikin Yaya Ahmad ko Jazuli duk da shi Jazuli bai san inda muka dawo ba.

Sati na ɗaya a kwance sai ga Jazuli da bamu san waya faɗa masa inda muka dawo ba, ansha daga tsakaninsa da mai gadi dan hanashi shigowa yayi a cewarsa bai sanshi ba.  Gashi wannan karon ma da riɗa-riɗan karnukan nan nasa ya tahu, Yaronsa ne ya zare wata lafceciyar wuƙa na sheƙi ya danna a wuyan mai gadin yana cewa “buɗe mana ƙofa ko yanzu Uwarka ta haifu wani! ” Babu shiri mai gadi ya buɗe ƙofar ya basu hanya harda karnukan suka shige cikin gidan zuwansa babu jimawa sai ga Suwiɗi Motar da ta ɗaukeshi ta dawo dashi.

Abin mamaki sai gashi ya fito da ƙafafunsa tamkar ba wanda ya karye ba mai gadi kansa kallonsa ya tsaya yanayi cike da al'ajabi..... ✍️

_Pls share & comments_ 🙏🙏🙏

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now