JIDDO(GidanAurena) part 4

8 0 0
                                    

🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
            _*JIDDO*_
    _*(GIDAN AURE NA)*_
               _*BY*_
  _*MAMAN NABEELA*_
🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷🪷
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
        _*DASHEN🌲ALLAH*_
  _*WRITER'S✍🏻ASSOCIATION*_
'''Ƙungiyace ta shahararrun marubuta haziƙai kuma tsayayyu masu aiki da baiwar da Allah yayi musu wajen ganin sun kawo muku zafafafan littattafai masu faɗakarwa wa'azantar wa da ilimantar wa gami da nishaɗantar daku masoyan mu'''
    _*ALLAH SHINE GATAN MU*_
  _*AL'ƘALAMI✍🏻YAFI TAKOBI🗡*_
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

_*PAGE*_4️⃣

_JIDDO LABARI_ me d'auke da darrusa masu d'umbin  yawa......

*Assalamu alaikum a bisa ƙorafe-ƙorafen da ake akan rashin postin ko yaushi, insha'Allahu zanyi ƙoƙari na dinga yi kullum ko ba yawa.*
*Amma fa ana yin comments sosai in ba haka ba ku nemeni ku rasa* 😇

_Masoya na haƙeƙa Maman Nabeela na matuƙar godiya da yadda kuke bata ƙwarin guwiwa Allah ya bar ƙauna i love you lodi-lodi_ 🥰🥰🥰

_Kai jama'a yanzu haka zaku yiwa Suwiɗi babu me kawo masa ɗauki_ 😂😂😂😂

Bissmillahirrahamanirrahim.

______Sai da likitoci suka kwashe sama da awa ɗaya, akan Jiddo sannan cikin ikon Allah suka samu komai ya dai-dai ta  numfashinta ya dawo.
Jinin da take zubarwa ma da kyar suka samu ya tsaya,ganin  zata iya rasa rayuwarta ita da abinda ke cikinta yasa likitoci suka bawa Momy Maimuna shawarar ayi mata tiyata. Ba tare da ɓata lokaci ba ta amince,Mahaifiyarsu ma da zuwa lokacin ta ƙarasu Asibitin  tare da Ahmad Yayansu Jiddo suma duk amincewa su kayi.

Yaya Ahmad dake ta cika yana batsewa saboda halin da Ƴar uwarsu ke ciki. Cike da alwashi kan Suwiɗi ya saka hannu kan takadar da za'ayiwa Jiddo aiki sanna ya wuce gurin ɗaukar jinin da za'a ƙara mata.

Sai da aka gwada jinin mutum uku duk basuyi dai-dai dana Jiddo ba, Momy Maimuna kuma da jininsu yake iri ɗaya sunce baza'a ɗibi nata ba saboda ƙaramin cikin jikinta.

“Dr idan akwai na siyarwa zamu siya asaka  mata” Yaya Ahmad yayi maganar yana duban likitan. 

“Ba sai an siya bama in ba damuwa akwai wanda Oga A.Rashed ke bayarwa duk ƙarshen wata  yau ɗin nan ya bayar kan yayi tafiya,in kun amince Sai a saka mata saboda shi za'a iya sakawa ko wa!” Likitan ya faɗa yana dubansu.

Ba tare da ja ba suka amince nan aka shiga yiwa Jiddo tiyata.
Anyi nasarar ciro jarirai Maza guda biyu sai dai ɗaya ya riga ya mutu tun a ciki ɗaya ne me rai,wanda shima gashi bakwaini ga  bashi da  cikakiyar lafiya. Likitoci ne suka karɓeshi  sukai wani ɗaki dashi dan bashi taimako.

Gadon da Jiddo ke kai aka turo aka mai da ta ɗakin hutu,inda aka bawa mahaifiyarta da Momy Maimuna damar zama a ɗakin bayan likitoci sun gama yiwa Jiddo abinda zasu yi mata a lokacin.

Anna mahaifiyarsu Jiddo tana shiga ɗakin hawayen tausayin ƴarta ya fara silalo mata. Momy Maimuna ce ta riƙo hanunta zuwa kujerar dake kusa da gadon Jiddo tana kwantar mata da hankali.

“Wayyo!!  Allah na,wayyo!!  Annata” Jiddo tayi maganar ƙasa-ƙasa idanonta a rufe.

“Maimunatu kamar Jiddatu ce tayi magana fa?” Anna tayi maganar tana kama hanun Jiddo.

“Anna  ai tiyatar ido biyu suka yi mata ina tunanin wadda ake alurar kashe zafi” Momy Maimuna tayi maganar itama tana leƙa Jiddo.

************

Juyawa yayi dan ganin me ya riƙe masa riga idano huɗu su kayi da Karen Jazuli daya Kama rigarsa da bakinsa,za gaya tsakar gidan suka fara yi she da karen duk yanda yayi Karen ya sakar masa Riga yaƙi ya saki. cikin hakin da ya fara da juwar da ke neman kadashi yace”Jazuli anya kanaso ka gama da duniya lafiya kuwa? Baza kayiwa tsinanen karenka magana ya sakar min Riga ba,ina ubanka ka tsaya kana kallo na,wallahi kazo kasa ya sakar min Riga  kuma ka tafi ka bar gidannan karka kuma dawowa"
Suwiɗi yayi maganar yana kuma kaiwa rigarshi warta.

Jazuli dake zaune yana cin abinci dariya ya sheƙe da ita yana cigaba da cin abincinsa.

“Toh! Tantiri abincinka ne kake cinyewa wallahi Sai ka biyani,kai babu abinda kake kawo wa Sai dai kazo ka cinye.......”
Lubabatu da ta fito daga banɗaki take maganar ganin Suwiɗi da kare suna ta zagaye gida yasa   tayi saurin yin shiru tana faɗawa ɗakinta ta banko  ƙofa.

Sai da ya kusa cinye abincin sannan ganin Abdull da Zainab na ta kuka suna kallonshi daga ɗakinsu ga Suwiɗi na neman faɗowa yasa yayi wani ɗan fito haɗi da Kiran karen,da gudu Karen ya saki rigar Suwiɗi da har ta fara yagewa ya dawo gurin Jazy yana karkaɗa jela.

“Timm” kake ji Suwiɗi ya faɗi  da rarafe ya shige ɗakin Jiddo ya rufu ƙofa faɗi yake“ Allah wadaran halinka  Jazuli idan ka tafi karka kuma dawowa gidannan na kureka,ɗan iska mara mutunci Allah ya tsinewa matsiyacin Karen nan naka albarka,washh! bayana”.
Suwiɗi yayi maganar yana dafe bayansa.

Sai da ya juyewa Karen sauran abincin ya ci sannan ya buɗe Randar ruwa yasha sannan ya juya yana faɗin “to...to..toh Old man s...sa..sai wani ji...ji...jik'on,a...a...ace i...ina,yi..yimata sa..sannu u..u...uwar Ma'u”
Jazy ya faɗa yana karta wuƙa a ƙasa yana sakin fito.

“Baza a faɗa ba Dan ubanka idan ka damu da  sai ka mata sannun ka bita Asibitin mana,wallahi kaji dai na faɗa maka karka kuma dawomin gida.Banda kazama ɗan da yake da wani matsayi a zuciyata wallahi da ko tambayarka hanyar gidan nan akayi baza ka iya faɗe ba”

Suwiɗi dake ɗaki a rufe yake ta zuba maganar.

_Hospital_

Likitocin dake kula da Jinjirin Jiddo wanda gama dubashi suka sanyashi cikin kwalbar saka bakwaini.
Anna da Momy Maimuna sunje sun ganshi inda Yaya Ahmad ya karɓi Jinirin da bezu da rai ba ya nufi gidan Suwiɗi dashi........

Yaya Ahmad na zuwa gidan Salma da suka tafi da ita yace tayi masa magana da Babansu  Suwiɗi.

Tana shiga soru ta leƙa ɗakin sorun tana kiran“Baba malan! Baba malan!!”shirun da taji yasa ta zura kanta tana haska wayarta saboda duhun yammaci da ya fara yi ganin baya ciki yasa ta nufi cikin gidan. 

Tana shiga taga tsakar gida fayau ba kowa “Ummarmu! Ina kike? ko bakya nan ne?” Tayi maganar tana ƙarasa shiga cikin gidan.

“Salma  kin dawo ya jikin Jiddo  ɗin?” Lubabatu ta faɗa tana buɗe ɗakin ta.

“Da sauƙi!  lafiya Umma kika shiga ɗaki kika rufe?”Salma tayi maganar tana duban Ummansu da ta haɗɗa zufa.

“Hhmmm!, Salma wannan tantirin ne yazo,  baki ganshi a waje ba?  yanzu ya fita”
Lubabatu tayi maganar tana buɗe Randar ruwansu tana kwan-kwaɗa.

“Ummarmu ni ban ganshi ba, ina Baba malan? Na duba ɗakin soru baya ciki, kuma da kawun Asama'u muka tahu yana son ganinshi!”

“Nayi masa uban me? Shima zuwa yayi ya ƙaremin tanadi ko me? Washhhh!! Allah bayana”

Suwiɗi yayi maganar yana riƙe bayansa...... ✍️


Pls share & share &share Masoya na amana much love🥰🥰🥰🥰

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now