JIDDO (Gidan aurena) Part 26

10 0 0
                                    

*JIDDO*
(Gidan Aurena)

_Story by_

*MAMAN NABEELA*

(_TEAM JAJURTATU 6_)
*BAYAN RAI (KHADIJA ISHAQ)*
*JIDDO GIDAN AURENA(MAMAN NABEELA)*
*JINANE(ZAITUN MAMAN FAUZAN)*
*IN BA KAI(OUM AFREEN)*
*SAIFUL ISLAM(OUM AMRA)*
*NURHAAN(SHUATY)*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*HAƊAKA PALACE GROUP*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*

'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''

*PAGE* 2️⃣6️⃣

“Anty Maimuna sannunku da zuwa kiyi a hankali kinga ba ke kaɗai bace ba” na yi mata maganar ina ƙoƙarin share hawayen idanuna ganin Mai gidanta Tahir ya shigo.

Tashi tayi ta zauna sosai amma tana riƙe da hannuna ƙam tamkar za'a ƙwace  ni idan ta saki hannuna, share hawayen idanunta tayi tana ƙara kallo na....

“Barka da rana Anna ina wuni ya mai jikin?” Tahir mijin Anty Maimuna ya gaisheta bayan ya zauna ƙasan kafet ɗin dake ɗakin cike da kamala da girmamawa.

“Lafiya lau jiki da sauƙi, ya hanya? Ya gurin su Hajiya kuma?”

“Lafiya lau ta ce a yi wa mai jiki sannu kafin tazu” Tahir yayi mata maganar... 

“Ina wuni Yaya Tahir” na gaishe shi.

“Lafiya lau Jidda ya jikin naki? ”

“Da sauƙi ya su Ihsan da Haidar? ” Na amsa masa haɗe da tambayarsa Ƴaƴansu shi da Anty Maimuna.

“Lafiya lau Allah ya ƙara sauƙi,  ai  suma suna nan tafe, ina tuna nin ma idan Hajiya zata zo tare zasu taho su duba ki” Tahir yayi maganar yana dubansu ita da Matarshi Maimuna cike da jin-jina ƙaunar da suke wa junansu,  ganin har sannan  suna  riƙe da hannun juna.

“Amin Allah ya kawo su lafiya" na yi maganar ina kallon su Asma'u da Azima da suke gaishe shi.
Amsa wa yayi da amin sannan ya amsa gaisuwar da su Asma'u ke masa.

Abincin da a ka yi a ka kai masa sitroom, ba'a jima ba sai ga su Baba da Yaya Ahmad sun dawo a can suka gaisa da Tahir ɗin, ko da ya tashi tafiya saboda shi a ranar zai koma Anty Maimuna kuma sai washe gari kuɗi da bamu san adadinsu ba ya ajiye gefen filo na, Anna ba yadda ba ta yi da shi ba a kan ya rage kuɗin sun yi  yawa amma yaƙi.

Wani abin mamaki ma sai da zai tafi ya saka Yara suka shigo da kayan abinci masu uban yawa, wanda dama kusan duk abinda Anty Maimuna ke yi wa su Anna da ni kai na shi yake bata saboda ya san iyayenta basu da ƙarfi a wannan karon Baba ne  kansa ya magantu yana  ce wa, “wannan kaya sunyi yawa abinda kullum ana yi don za'azo dubiya ma sai a ce sai an kuma yin wahala” yayi maganar yana fita ƙofar gida  wanda yayi dai- dai barin Motarsa daga layin. 

Da da dare Anty Maimuna ce ta shafa min maganin da a ke shafa min a jikina a lokacin kuma a ke bata labarin irin wahalar da nasha wanda yanzu Alhamdulilah tunda yanzu wasu sassa na jikina sun fara motsawa.

Kuka sosai tayi tana faɗin mai zai hana kawai ayi ƙarar Suwiɗi a nema min haƙina saboda zaluncin da yayi min?

Idanun Anna a waje take faɗin“Maimuna ai tunda muka samu ya sake ta ba tare da an kai ga zaman kutu ba sai mu gode wa Allah, ai irin waɗɗan nan mutanen kina ganin zasu zuba ido shari'a tayi aikinta! Ga Ƴar nan Husna ta girma gaf take da ta samu manema wannan matsalar sai ta iya hana mata aure  domin duk wanda ya fito tsaf ƴan guntsiri tsoma zasu ƙyasa masa  Uwarta har Babanta ta kai ƙara ko kuma kiji ana butun ai Matsafi ne Ubanta, a yanzun ma dai kawai Allah ya kiyaye ” Anna ta yi maganar cike da tausayin su Asma'u don tabbas ta yarda ƙaddara ta haɗa auren Maijidda da Suwiɗi tunda duk auren da Baba tsohu yake haɗawa ba'a taɓɓa samun wadda ta shiga makamanciyar matsalar gidan aure irin ta  Jiddo ba.

“Haka ne Anna Allah ya bata lafiya su kuma Allah ya basu maza na gari waɗɗan da duk abinda za'a faɗa ba zai hana su auresu ba”

“Amin”Anna ta faɗa.

Sosai wannan maganar ta ƙara sani kuka ina daga kwance kamar mai baci ina sharar hawaye cike da tausayin Ƴaƴana Addu'a sosai na yiwa su Asma'u kan Allah yasa kar abinda Babansu ya keyi ya bibiyi rayuwarsu kafin daga baya ban san lokacin da baci ya ɗaukeni ba.

★★★★★★★★

Washe gari yau ma kam Alhamdulilahi  jikina ya kuma ƙara sauƙi don yau da kaina nayi alwala da a ka kai ni banɗaki, bayan nayi sallah ma da kaina na ci abinci farin cikin da nake ciki kuwa baya misaltuwa.

Anna kanta farin cikin da take ciki na ganin kullum ana samun cigaba baya misaltuwa, Anty Maimuna ma da take yin kamar bata son tafiya ganin yadda na tashi da sauƙi sosai ta fara shirin koma wa saboda Tahir tun safe da suka yi waya ya ce mata driver ya taho.

Yau ma sai da a ka yi abincin sadaka a ka raba   sannan a ka saka ayimin saukar alƙur'ani mai girma, sai wajen azahar Anty Maimuna ta tafi Kaduna  tana mai fatan Allah yasa sanda zata haihu na warke, saboda haihuwar tata a wata mai kama wa a ke saka ranta.

*BAYAN SATI ƊAYA*

Tsaye nake a kan ƙafafuna ina dafe da kafaɗar Azima   wanda yau kwanana biyu kenan da fara iya taka ƙafafuna amma bana iya tafiya ni kaɗai sai dai idan na dafa bango ko na dafa kafaɗar wani cikinsu, jikina ya yi kyau sosai duk wannan muguwar ramar da nayi ta fara ɓacewa.

Sosai hankulanmu yanzu suka ƙara kwanciya,  tsakar gida na ce Azima ta temaka min na fita na ɗan ta taka muna fitowa Anna da ta fito daga kicin ta fara murmushi gani na na fito.

“Maijidda kin fito ai gwanda ki ringa ta takawa ko ƙafar ta ware daga jimawar da ki kayi baki taka ta Allah dai ya ƙara baki lafiya” Anna tayi maganar cike da farin cikin da baya iya ɓoyuwa duk lokacin da taga Jiddo tana ƙara samun sauƙi.

“Amin Annarmu eh nima saboda na ɗan ƙara jin daɗi na ce ta temaka min na fito” nayi maganar nima cike da farin ciki.

Da ke tsakar gidanmu tana da ɗan girma sai da na ta taka sosai sannan na zauna kan tabarmar da Anna take, wanda ya yi dai-dai da sallamar da a ka yi haɗe da shigowa.
Salma ce bayanta su Zainab da Abdull suna hango ni da gudu suka tahu gurina zasu faɗa jikina Azima tayi saurin tare su tana ce wa “kai ku bi a hankali  mana ko kun manta bata da lafiya ne......”

Baki Zainab ta turo gaba tana neman rushewa da kuka Anna tayi saurin ce wa“kinga zo nan ƙyale Anty Azima maza rungume Ammeynki” Anna tayi maganar tana murmushi.

Ƙan ƙame Jiddo tayi tana sakin dariya ta ce “Ammeyna”

Dariya dukansu suka sanya Salma ta ce “ka ga cingom ɗin Ammey, kullum fa sai ta ce a kawota harda kuka take” Saa tayi maganar tana dariya.

Dariya kawai na yi ina shafa kanta.
Gashi da Anna Salma tayi sannan ta gaishe ni tana yi min ya jiki.......✍️

_Pls share & comments_ 🙏🙏🙏

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now