JIDDO (Gidan aurena) Part 28

3 0 0
                                    

*JIDDO*
(Gidan Aurena)

_Story by_

*MAMAN NABEELA*

(_TEAM JAJURTATU 6_)
*BAYAN RAI (KHADIJA ISHAQ)*
*JIDDO GIDAN AURENA(MAMAN NABEELA)*
*JINANE(ZAITUN MAMAN FAUZAN)*
*IN BA KAI(OUM AFREEN)*
*SAIFUL ISLAM(OUM AMRA)*
*NURHAAN(SHUATY)*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*HAƊAKA PALACE GROUP*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*

'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''

*PAGE* 2️⃣8️⃣

__________Kaduna nake shirin tafiya gidan Anty Maimuna da take ta son na je tunda na samu sauƙi,  amma Anna da Baba suka hana saboda ban gama idda ba.

Safiyar  shekaran jiya Tahir mijinta ya kira yake faɗa mana ta haihu.
Murna sosai muka yi jin Allah ya sauketa Lafiya  ta samu Ɗa namiji.
Tun a jiya Anty Maimuna taso na tafi amma Anna ta ce na bari sai yau idan ta ƙarasa haɗa abubuwan da za'a tafi mata da su.

“ Anna   na gama shiryawa“ na yi maganar ina saka ƙaton hijab ɗina da ya kai min har ƙasa haɗe da ɗaukar jakar da ƴan komatsai na ke ciki.

“To yi wa Yayanku magana ya zo ya kai ki tasha” Anna tayi maganar tana zuge zif ɗin jakar da a ka zuba abubuwan da zan tafi da su.

“To” na amsa ina fita tsakar gida na nufi ɗakin Yaya Ahmad na yi masa magana,  ce min ya yi gashi nan fitowa, baro ƙofar ɗakinsa na yi na dawo falo“Anty Jidda don Allah ki shafa min kan jaririn nan ki ce kuma ina gaishe shi kan nazo,  Allah don dai hadda nake bayar wa da dani za'a tafi”Azima ta yi maganar cike da son zuwa ita ma.

“Ban da abinki  autar Anna jariri ina ya san a ce ana gaishe shi!  Zan dai shafa kan nasa kafin ku zo, kiyi ƙoƙari ki gama bada hadda kafin lokacin suna yadda da kin faɗa Malan ustaz ɗin naku zai bari kiyi fashi” na yi maganar ina murmushi.

“Na ma fa kusa gama bada haddar ai in sha'Allahu ana ya gobe suna zan tahu, anjima ma zan kira Asma'u na faɗa mata” Azima ta yi maganar tana ɗaukan kofin ruwa ta kai bakinta.

“To Allah ya yadda” na yi maganar ina miƙewa ganin Yaya Ahmad ya shigo.

“Ina kayan tafiyar? Ko wannan ne? ”Yaya Ahmad ya yi maganar yana nuna jakar kayan.

“Eh ita ce ka yi maza  ka kai ta Allah yasa ta samu Mota da wuri bana son tafiyar dare” Anna ta yi maganar tana miƙa min kuɗi.

Karɓa na yi shi kuma Yaya Ahmad ya ɗauki jakar kayan ya nufi ƙofa.
“Anna na tafi” na yi maganar ina rataya jakata a kafaɗa.

“To ki kula Maijidda ki gaishe da Maimunan da Hajiyar Tahir ɗin”

“To Anna in sha'allah zasu ji” na yi maganar ina fita jin Yaya Ahmad har ya ta da babur ɗinshi.

Ina fita na hau bayan babur ɗin Yaya Ahmad Azima da ta rakoni har ƙofar gida ta fara ɗaga min hannu ni ma ina ɗaga mata sannan yaja babur ɗin muka tafi.

Ina zuwa tasha cikin ikon Allah na samu Motar da mutum biyu ya rage ta cika ina shiga ban jima ba a ka samu cikon ɗayan da ya rage.

Yaya Ahmad bai bar tashar ba sai da ya ga Motar mu ta tashi, bayan ya miƙo min wata leda babba ya ce na kai wa Anty Maimuna.

Motar mu na ɗaukan hanya na kira Anty Maimuna na ce mun taso fatan iso wa lafiya ta yi min ta ce da mun shiga Kaduna na kirata  zata tura driver  ya ɗauko ni daga tashar.

Amsa ma ta na yi da to ina katse kiran.

★★★★★★★★

*KADUNA*

Kamar yadda Anty Maimuna ta ce da mun shiga Kaduna na kirata haka ko na yi, muna shiga na kirata na faɗa mata.
Number drivern ta turo min ta ce yanzu zai tahu.

Muna isa tasha muka fir fito daga Mota, gefe na koma kan wani benci na fara dube-dube ko zan hango drivern Anty Maimuna amma ban hango shi ba.
Ƙoƙarin kiran number da Anty Maimuna ta tura min ta driver na fara yi.

“Assalamu alaikum ranki ya daɗe kyakyawa in ban takura miki ba ko zaki zo mu rage miki hanya tunda mai ɗaukarki bai iso ba ba girmanki bane tsayuwa a nan mutane na kallonki”

Jin sallam haɗi da magana a kusa da ni yasa ni dakatawa da kiran da nake ƙoƙarin turawa na ɗago manyan idanuna da suke cike da gajiyar tafiya na sauke kan mai yi min magana. 
Matashi ne fari tass daga ganinsa ka ga ɗan hutu sai dai kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci wayaye ne na gaske duba da yanayin shigarsa dama askin kansa.  Kallo ɗaya na yi masa na ɗauke kaina ina tura kiran drivern Anty Maimuna haɗe da ce wa “Amin wa'alaikassalam mai  ɗaukata yana hanya na gode ” na yi maganar ina matsawa daga gurin.

Tunda ta fara motsa ɗan ƙaramin bakinta tana magana ya kafeta da kallo har wani lumshe idano yake jin sautin zazaƙar muryarta, ganin ta matsa daga gurin shima ya koma daga gefe jikin Motar shi yana kallon duk wani motsinta magana ya juya yana yi wa wanda suke tare “kai kaga wata haɗaɗiya kuwa gaskiya ni dai yau na gamu da matar da zan iya aura....” matashin ya yiwa abokin tafiyasa maganar.

“Kai dai faɗi gaskiya Faisal ni inba gani na yi an ɗaura an kai maka ba ai bazan taɓɓa yadda ba”

“Aikuwa zan baka mamaki Haisam don wannan ba kalar waɗɗan can ba ce,  don Allah maza shiga Mota mubi bayansu kaga suna ƙoƙarin fita” Faisal ya yi maganar yana  buɗe Mota ya shiga.

JIDDO
Ina kiran wayar drivern na hango shi yana nufu inda nake jakar kayan ya ɗauka muka ƙarasa gurin Motar shiga na yi bayan ya saka kayan a Motar muka nufi ƙofar fita daga tashar.
Sosai Ɗanladi driver ya ke gudu cikin ƙanƙanin lokaci muka isa unguwar su Anty Maimuna horn ya yi a ƙaton get ɗin gidan, a na buɗe get ɗin ya shigar da Motar.

Bayan ya yi perking fitowa na yi daga Motar na nufibƙofae shiga gidan, kaciɓus na yi da Ihsan da ta tahu da gudu tarata faɗawa jikina ta yi tana ce wa “ga Ammey na ga Ammey na”

Murmushi na yi ina rungumeta  na ce “oyoyo daughter Ammey”

Dariya ta yi tana karɓar jakar hannuna,  ƙarasa shiga cikin falon gidan muka yi wanda ya yi dai-dai da saukowar Anty Maimuna daga upsters rungume juna muka yi cike da ƙaunar juna...

“Faisal wai ina zaka kai mu ne sai faman za gaye muke nifa na fara gajiya na faɗa maka sun riga sun ɓace mana wa ya sani ma ko Aljana ce yau ka yi gamu da ita garin son matanka na tsiya, look tsaya na sauka sai kaje ka yi ta neman Aljanar da ka yi gamu da ita,  ni bazan iya ba ina da abin yi” Haisam da ransa yayi mugun ɓaci saboda za gayen da Faisal ke ta yi dasu sakamakon Motar da suke bi ta ɓace musu ya yi maganar cikin ɓacin rai.

Tsaki Faisal ya buga yana dukan stearing Motar shi ma rai ɓace. .
“Don Allah ka ƙyale ni da abinda ya dameni, tabbas ko ba yau ba sai na ganta ” ya yi maganar yana ɗauko karan sigari yana  kunnawa.

Haisam sakin baki ya yi yana kallonshi ganin ya fara banka musu hayaƙi cikin Mota sauke glass ɗin Motar ya yi yana jan mugun tsaki cike da takaicin halin abokin nasa wanda bashi da aiki daga shaye-shaye sai bin matan tsiya saboda sangarta shi da Iyayensa suka yi sakamkon shi ɗaya suka haifa.

Dalilin zuwansa tasha ma saboda saƙon da zai karɓa ne sai kuma gashi ya yi gamu da da wadda yake iƙirarin yana so....

Tsaki Haisam ya kuma ja tuna yadda ya katse masa aiki kan ya raka shi ya karɓo saƙon yanzu kuma gashi sun :ige da zagayen gari neman wadda ko sunanta basu sani ba bare gidansu.

“Kai ka fa dameni da tsakin tsiya idan  baza ka taya ni adu'ar mu ganta ba ka yi shiru.” Faisal ya yi maganar yana yi wa sigarinsa wani wawan zuƙa haɗi da fesarwa.

Sai da yasha karan sigari uku kafin su ƙarsa ya sauke Haisam a ƙofar gidansu ya nufi nasu gidan yana kunna kiɗa a Motarshi sautin waƙar Davedo ya fara fita yana yi yana bin waƙar yana kaɗa kai......... ✍️

_Pls share & share_ 🙏🙏🙏

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now