JIDDO(Gidan aurena) Part 34

27 2 2
                                    

JIDDO
(Gidan aurena)

Story by
MAMAN NABEELA

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATIONS

JIDDO
_______Tunda suka shiga ciki suka barni a gaiding ɗin na faɗa duniyar tunanin wannan bawan Allahn,  idanunsa masu haske da kyawu ga uwa uba kwarjini ga kya-kyawan murmushinsa da suka shige cikin kwanyata suka zauna daram nake sake tunawa, wanda ban farga ba na tsinci kaina ina faman zuba murmushi.

Kyawawan beauty  point ɗin kumatunsa da suka loɓa ya yin da yayi murmushi, na kuma tunawa ina kuma murmushi cike da yaba kyawunsa“uhm amma fa akwai mugun tsahu” na yi maganar a fili ina dariya sosai tuna yadda naga Tahir ya zama wani gajere a kusa dashi.
“Don ma yana da kauri toh da ya za'a ganshi? ” na kuma maganar a fili kamar wani zai bani amsa.

“Amma kuma  indai yana da kyan hali duk Macen da ta sameshi ta mure” na kuma maganar ni ɗaya kamar wata mai taɓin hankali cikin murmushi.

Jidda Mai ya shafe ki ne!  Kin zaƙe da yawa fa daga ganin Mutum? To dai yafi ƙarfinki' wani sashe na zuciyata ya tunatar dani abinda nake ƙoƙarin tsunduma kaina.  

Take na fara ƙoƙarin yaki ce wa kaina tunaninsa saboda ni karan kaina nasan ba'ajina bane ko ɗaura masa ni aka yi a ƙafa ai ya kunce. Wayata na ɗauka na fara buga game ina cikin yi Ihsan da Jannat suka dawo.
“Ammey mai ki ke yi? ” Jannat da ta ƙarasu tana leƙa wayar ta yi magana.

Murmushi na yi ina ce wa“ Jannat game nake...” ban kai ga rufe baki ba tayi saurin karbar wayar tana matsawa gefe.
Dariya na kuma yi ganin yadda ta koma gefe ta nutso, Ihsan ma dariya ta yi tana ɗauko littafanta ta dawo kusa da ni tana cigaba da aikinta.
Littafin biology da camistry ta ɗauko tana yin aikin tana yi min bayanin abinda aikin ya ƙonsa. Sosai nan  take naji tsohuwar soyayyar da nake yiwa aikin likitanci na taso min, bansan da sauran gurbin ɗauƙe abu a kwanyata ba sai da naji duk abinda ta faɗa na zama min ɗam a cikin kaina.

Kiran sallar la'asar da aka fara yi yasa muka tashi muka nufi cikin gida zuciyata cike da nishaɗi.

Ina zura kaina cikin falo da ƙamshinsa na fara cin karo, sai dai kuma babu kowa cikin falon  sai tarun kayan da suka ci-ci abinci a cikin falon.

Dakin da yake  nawa na nufa don gyara jikina ya yinda Ihsan itama ta nufi ɗakinta don yin sallah, ina shiga ɗakin  kayana na fara ƙoƙarin cirewa  sannan na shiga banɗaki sai da nayi wanka na gyara jikina sannan na fito
Rigar da na cire na mayar sannan na gyara fuskata, fitowa na yi na nufi ɗakin Anty Maimuna da sallama na shiga ciki ina murmushi cike da jin kunyar wadda idanuna suka yi tozali da ita na yi ƙasa da kaina ina ƙarasa shiga cikin ɗakin.

Amsa sallamar da na yi suka yi suna murmushi.
“Sannu Ɗiyata ƙarasu nan mana ki zauna muyi hira ”
Mame dake kan darduma da alamu suka nuna idar da sallarta kenan  ta yi maganar tana kallon.

Sai da na ɗauki Babyn Anty Maimuna sannan na zauna daga gefen Mame cikin jin nauyi.

Sosai Matar ke ƙoƙarin jana da hira wanda tun ina ɗan jin nauyin mayar mata har ban san sanda na ware ake hirar tare da ni ba saboda barkwancin ta, sosai muka sha hira har tana ce wa  kan na koma kano amma zanzo gidanta? Murmushi na yi ba tare da na bata amsa ba ina mamakin sauƙin kai irin nata da sun jama'a wanda wasu masu kuɗin sam basu da irin wannan halin sai ma kyamar mutane da hantararsu  suna ganin su sunfi kowa....

“Mame in sha'Allahu zata zo kan ta tafi ta kawo miki ziyara” maganar Anty Maimuna ta katse mini zancan zucin da nake, murmushi nima na yi ina gyaɗa kai.

Wajen ƙarfe biyar muka sauko ƙasa gaba ɗayan mu saboda tafiya da su Mame zasu y, har gurin Mota muka rakasu ina riƙe da hannun Jannat da har sannan wayata take hannunta , duk da yanda gabana ke faɗowa haka na kai dubana saitin da nake shaƙo ƙamshin turarenshi.
Tsaye yake suna magana da Tahir  a jikin Motar, shagala na yi da kallonsa ganin yadda yake motsa bakinsa kamar ba da hausa yake magana ba ganin kamar zai kallo gurin yasa na yi saurin ɗauke idona daga kanshi.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now