JIDDO (Gidan Aurena) Part 3

11 0 0
                                    

*JIDDO*
    ( _Gidan Aurena_ )

*Dashen Allah writers association*

        _Ina kuke 'yan kasuwa ga dama ta samu, ga mai son a tallata masa hajarsa cikin farashi me sauk'e da rahusa sai ya tuntu'beni ta wagga number.👇_
09031865693

_JIDDO LABARI_ me d'auke da darrusa masu d'umbin  yawa......

Bissmillahirrahamanirrahim.

Babi na uku

Da mugun sauri 'Danladi driver ya juya dan bud'e k'ofar motar.

Asma'u matsawa tayi ta basu hanya suka k'arasa fita.Bin bayansu tayi waje tana kamu hannun Momy Maimuna dake k'ok'arin shiga mota bayan sun saka Jiddo,cikin kuka tace" Momy tare zamu tafi ko?"

"A'a Asma'u ki koma ki had'd'a kayan Ammynku wad'd'an da za'a buk'ata a asibiti. 'Danladi bayan ya kaimu zai dawo ya d'aukeki".

"Toh'Momy"Asma'u ta fad'a tana sakin hannunta.

Cikin gida bayan fitar Momy Maimuna Suwid'i da yake jinsa kamar zuciyarsa za tayi  gobara dan 'bacin rai k'wafa yayi yana jijiga kai,lokaci d'aya ya saki murmushin da shi kad'ai yasan ma'anarsa.

Lubabatu ce ta fito daga d'aki tana kokawar saka hijabi  tayi hanyar soru "Lubabatu  ina zaki?" Suwid'i yayi maganar,yana watsa mata jajayen idanuwansa.

"Haba Malan wace iriyar tambayace haka!kaima ai kasan Asibiti zanje mu Kai Jiddo,tunda ba'a tafi Ba wani cikinmu  ba?"

"Toh bazakije ba,yadda fitsarariyar yarinyar nan tazo ta k'are min tanadi ta tafi da ita. Babu me bin bayansu,taje ta kai ta duk inda zata Kai ta tana samun lafiya kuma dule ta dawo da k'afarta dumin ni Suwid'i duk wanda yaci tuwo dani miya yasha,kuma ba'a nuna ni da yatsa ban karyashi ba.Itama fitsarariyar ba kyaleta zanyi ba sai ta gane ni suwid'i ba kanwar lasa bane..." Yayi maganar yana dad'a sakin wani makirin murmushi.

Lubabatu da ta saki baki da hanci tana kallonsa tana dad'a cika da tsorun abinda zai aikata,sanin mugun halinsa da tayi yasa ta dawo ta cire hijabin da ta saka.

Asma'u dake tsaye shigowarta kenan bayan tafiyar su Momy tanajin duk abinda Babansu ya fad'a wata iriyar tsanar halin Babansu ce taji tana taso mata daga zuciyarta.
Ba tare da tayi magana ba ta kama hannun k'anenta  ta nufi d'akinsu "Ke Ma'u Ina Salma?"
Malan Suwid'i ya jifa mata tambayar tana gaf da shiga d'akin, cikin danne abinda ke tasu mata ta tausasa harshinta tana cewa "tare suka tafi asibitin Baba"tayi maganar tana share hawayen da ya zubu daga idanonta.

"Lubabatu ke kika saka Salma ta bisu ko? Daga ke har ita zanyi maganinku...."

"Gya..gya.gyara kintsii Old man, wa...wa ya ta'b'ba ka kake  ta...ta faman haushiii ?"
Jazuli Babban d'ansa d'an matarsa ta farko wadda ta rasu, wanda ya zamu tantirin d'an daba yayi maganar yana k'arasa shigowa shi da k'aton karensa dake ta zaru harshe.

_Hospital_

Mommy sun isa wani pravet hospital da yafi kusa da inda suke aka turo gadon d'aukar marasa lafiya aka d'au Jiddo akayi cikin Emergency da ita ganin yana yin da take ciki.

Sai a lokacin Momy ta samu damar kiran gidansu ta sanar da Mahaifiyarsu,bayan ta gama waya da Mahaifiyarsu Mijinta ta Kira ta Sanar dashi abinda ke faruwa,tambayarta wane asibiti suke ya yi? Tace su na asibitin MAI NASARAH".

"Maimunatu ai asibitin A.RASHED ne, Abokina"

"Honorable, A.Rashed dai dana sani mijin murgayiya Sakina?"

"K'warai kuwa shi nake  fad'a miki,kinsan be dad'e da ginashi ba a nan kano.Bari kiga na kirashi dan  a k'ara bata  kulawa sosai".

Cike da farin ciki tace "toh Habibina muna mutuk'ar godiya".

Cikin k'ank'anin lokaci aka sauyawa Jiddo d'aki aka maida ta wani ke'bantacen guri  me d'an karen  kyau da tsari ga na'ururi ko ta ko ina suna aiki.Gurin be yi kama da Asibiti ba dan  yafi kama da gida.

Cikin lokaci k'ank'ani likitoci suka rufu a kan jiddo dan ceto  rayuwarta.

"Kai dan  baka  da mutunci nine nake  haushin ?  Kuma  ba nace  karka  kuma zuwa gidan nan da wannan abun ba!"
Suwid'i yayi maganar yana yin baya  ganin karan na  kallonshi yana zaro harshe.

"Hah...ha..haba Old man,indai  zan...zan..saka k'a...k'afata a guri  ai  dule  Bingo ya...yasa tashi shi...shima,ku...kuma ba fad'a kake  tayi ba tun...tun daga  wa..waje ana ji...jiyuka kana ta 'ba..'ba...'batu ai shi.. shine ha..ha..haushin".
Jazuli yayi maganar yana yin ball da butar dake gabanshi yayi hanyar kichin d'in gidan karensa na take masa baya.

Sakin baki Suwid'i yayi yana binsa da kallo Dan duk rashin mutuncinsa yana shakkar wannan ifritun yaron Jazuli,cumin duk wani aiki idan yayi akayi rashin sa'a aikin ya samu matsala toh kusan kansa abun yake komawa shiyasa ya zamu fand'd'arare Maraji gashi yafi sons a fiye da kowa a 'ya'yansa.

Asma'u tana shiga d'aki da k'anenta ta raba abincin data kar'bo na sadaka biyu ta basu rabi suka zauna suna ci had'd'a kayan da zata asibiti tayi cikin leda viva sannan ta juye sauran abincin a k'aramin plas shema tasa a ledar.
"Anty ke baza kici abincin ba ?"Abdull k'aninta yayi maganar yana kallonta.

"Abdull zanci mana amma sai naje asibiti gurin Ammey"

"Amma damu zaki ko?"
Abdull ya kuma yi maganar.
"A'a sai naje idan zan koma sai na sai na koma da Ku!" Asma'u tayi maganar tana saka hijabinta taci gaba da cewa "Abdull ka kula da Zainab kurku yi rashin ji kar kuma ku tafi gidajen mutane,kuma kuyi tayiwa Ammey adu'a Allah ya bata lafiya kunji".

Kansu suka gyad'a suna fad'in "toh Anty ".

Tsakar gida ta fito hanunta rik'e da ledar kayan da zata asibiti, "ke Ma'u ina zaki?"
Suwid'i yayi maganar.

"Baba asibiti gurin Ammey zani"Asma'u ta fad'a saga inda take.

"Toh baza kiba nace baza kiba ai babu me binsu asibitin nan itama Salma da ta bisu ina nan ina jiranta ba kyaleta zanyi ba".Suwid'i yayi maganar cikin fad'a dan abinda Maimuna tayi masa ya mugun tsaya masa a rai.

"Wa..wa... waye a asibiti?"
Jazuli daya fito daga kichin hannunsa rik'e da tukunya ya fad'a.

"Ammeyn mu ce"
Asama'u ta bashi amsa.

"Ha..ha...haba Old man ya..ya...ya...zaka ha..hanata zu..zu...zuwa gurin ma...ma...mahaifiyarta,a..a...ai ba...ba...a raba d'a da...da.... Mahaifanshi.ke...ke....wuce ki...ki tafi ki.. kice i..i...ina mata sa...sanu".
Jazuli yayi maganar yana zama.

"Kai Jazuli ka kiyayeni kar ka...." kasa k'arasa maganar yayi saboda ido hud'u da yayi da Karen  Jazuli a gabansa yana zazaro harshe.

K'ok'arin barin tsakar gidan yayi tun matsiyacin karen tak'adirin nan be masa wani abu ba charab yaji anyi ram da rigarsa......!

_Hospital_

Sai da likitoci suka kwashe sama da away d'aya a kan Jiddo sannan cikin ikon Allah suka samu komai ya dai-daita inda akayi nasarar yi Mata tiyata aka ciro bakwainin d'a namiji.....✍️

🤣🤣🤣🤣Wayoo ni Jazy da alama kaine maganin uhm bari dai nayi 🤐


_Pls share & share & share Habibatis_ 👏👏👏

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now