JIDDO(Gidan aurena) part 6

6 0 0
                                    

*JIDDO*
( _Gidan aurena_ )

By

*MAMAN NABEELA*


*D. A. W. A*

Page;6️⃣


Zama Anna tayi gefen gadon tana cewa "haba Mejidda yawan tunani ko saka damuwa a zuciyarki shin zai miki maganin halin da kike cikine? "

Cikin kuka ta girgiza kai tana saka hanu ta rufe bakinta saboda wani kukan da yake kuma tahu mata.

Anna ce ta suma yi mata faɗa Momy Maimuna na taya ta, a stoation ɗin da take sam ba'a son tana yawan shiga damuwa da tunani saboda ba wai ta gama dawowa normal bane.

Sai da ƙyar suka samu tayi shiru ta share hawayenta. Anna ce ta miƙa mata charbinta tana cewa da taji tunani da damuwa zasu dawo mata ta ringa faɗin "Inna lillahi wa inna ilaihirraji un, ta kuma yawaita yin Salatin Annabi da istigifar, Mejidda Allah yana sane dake kuma zai kawo miki ɗauki kinji! "

"Toh, ina Asma'u? " Jiddo tayi maganar tana karɓar maganin da Momy Maimuna ta ɓallo tana miƙa mata.

"Taje gida zata tahu da Abdull da Zainab" Momy Maimuna tayi maganar tana kuma ɓallo wani maganin tana miƙa mata.

Sosai yau jikinta ya ƙara sauƙi, masu zuwa dubiya nata zuwa.

Jaririnta aka kawo tabashi Nono wanda zuwa yanzu akan kawo mata shi akai-akai wanda wani lokacin har goyon gaba likitar dake kula dasu kan sakata tayi masa. Karɓar shi tayi tana saka masa abincinsa a baki.

Hajju matar Kawo Auwalu dake kallonsu cike da tausayi tace"Suwiɗin yazu ya gansu ne Maman Ahmad? " ta faɗa tana kallon Anna.

Girgiza kai Anna tayi tana cewa "ina fa ai bana tunanin zaizo, kin manta haihuwar Abdull da tayi a Asibiti ko leƙe bamu ganshi ba har aka sallamemu. Yadda Asama'u ma ke faɗa min Abokiyar zaman Mejiddan tanaso ta zo ya hana yace babu me zuwa, ita kanta Asama'un Babban ɗansa yasa ya barta take zuwa ba'a son ransa ba"

"A gaskiya wannan mutum anyi ɗan iska mara mutunci, ko dake duk laifin Baba tsohune duk waɗɗanda yayiwa wannan auren me kama da na sadaka wallahi Jiddo tafi kowa zama abin tausayi a gaskiya ya kamata wannan karon ko me yake taƙama dashi a nuna masa iyakarsa, haba yarinya ta fige ta lalace" Hajju ta kai ƙarshen maganar cikin faɗa dan dama ita zafi gareta.

Ammaa ƙanwar Anna dake zune ba tayi magana bace ta karɓe zanchan da "Hajju kema kya faɗa ni bansan ko suma ya tsafacesu ne shiyasa suka kasa ɗaukan wani ƙwa-ƙwaran mataki a kansa, ko kuma jira suke idan ya kashe musu yarinya sannan zasu ɗau mataki" Ammaa ta kai ƙarshin maganar cike da takaici!.

"Jamila bazaku gane ba lamarin gidan auren Jiddo adu'a kawai yake buƙata, Ahmad fa ba yadda beyi ba kan lamarin daga ƙarshe dole ya kyale saboda yadda Mejiddan ta barkici " Anna tayi maganar cike da ɗacin zuciya na tausayin halin da ƴarta ke ciki.

"Ai kuwa indai hakane daga Asibitin nan gidan Malan Ummar sani fagge zan wuce nayi masa bayanin matsalar ya bamu tufin da yake ta ringa sha nasan insha'Allahu za'a dace"
duk sunyi na'am da maganar Ammaa inda suka cigaba da shawar-warinsu kan yadda za'a ɓulluwa lamarin.

*BAYAN KWANA UKU*

Kafatanin abinda suka zo Asibitin dashi suke harhaɗawa saboda saka ran sallama da suke a yau litinin, shigowar Likita tare da wasu Norse su biyu yasa Anna dake haɗa kayan dakatawa.

Gwaje-gwaje suka sake yi mata da tambayoyi Likitan na rubutu cikin file ɗinta, ganin babu wata matsala Likitan ya rubuta magungunan da zasu kuma siya waɗɗanda zata sha in sun koma gida tare da sallama bayan sati biyu kuma zata dawo a sake dubata da Babynta.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now