JIDDO (Gidan aurena) Part 21

4 0 0
                                    

*JIDDO*
    *GIDAN AURE NA*
               *BY*
  *MAMAN NABEELA*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASOCIATION*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*

7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank

*Page* 2️⃣1️⃣

______Jazuli na shiga Direct hanyar da ya gani kamar ta falo ya nufa yana  fito, Yaronsa tsayawa yayi daga barandar falon tare da Karnukan,  shi kuma Jazuli ya buɗe ƙofar ya shiga.
Zama yayi saman kujerar falon yana kallon ko ina na cikin  falon, Lubabatu dake cikin Kicin ce ta fito hannunta riƙe da flas na abinci, bata kula da Jazuli da ya hakince yake ƙarewa falon kallo ba sai da tazo tsakiyar falon idanunta suka sauka a kanshi yana saka   karan sigari a baki  yana ƙyasa leta.   Zaro ido waje tayi tana shirin kwasa da gudu maganarsa ta dakatar da ita faɗi take cikin zuciyarta wane ɗan neman jidalin ne ya nunawa tantirin nan gidan da suka dawo..?

“Ha...haba U...u...uwar Harisu sa...sai ku....kuyi ƙaura ba....ba sanar dani, ku...ku....kunzo kuna ci...cin du....duniyarku da...da tsinke a...a cikin sa...sa...sabon gida ku....kun manta da...dani! ”
Yayi maganar yana ƙareta da zuƙar sigari yana fesarwa.

Lubabatu da jikinta har tsuma yake ca ta ke  abinda tayi masa tun suna tsuhon gida ne be manta ba zai ɗau mataki akanta, ajiyar zuciya ta saki jin abinda  yace! Cikin washe  baki tace“haba wane mu mu manta da kai, ai munyi tunanin ya faɗa maka a matsayinka na Babban wa saboda mu ma tashin haka yazo mana babu shiri”
Lubabatu tayi maganar cike da ƙarfin hali tana neman hanyar da zata gudu daga gurin, cikin zuciyarta kuwa duk sanda zai busa hayaƙin sigarinsa  sai ta zuba Allah ya isa.

Cikin ƙan-ƙanin lokaci falon ya fara turniƙewa da hayaƙin sigari.
Ƙara zuƙar sigarin yayi ya fesar sannan yace
“toh a....a....aikuwa ni....nima na....na...dawo ke....kenan, sa....sa....sai a....a....gyara min Ɗa....ɗa....ɗakina dan....dan....nima dole a...aci a...arziƙi dani, wa...wa....wai ina U....uwar Maa'u? ” Jazuli yayi maganar yana kashe sigarin da ya zuƙe.

Tunda ya fara magana Lubabatu ta zaro idano faɗi take shikenan sun shiga uku in wannan tantirin ya dawo gidan! Cikin zuciyarta. Ta buɗe baki  zata yi masa magana aka buɗe ƙofar falon......

★★★★★★★★★★

A bakin get Mai gadi tun bayan da ya buɗe get Motar da ta kawo Suwiɗi ta shigo ya ganshi ya futo da kansa yake cike da al'ajabi domin shi dai tunda yake bai taɓɓa ganin Mutumin da ya karye,  ya kuma warke lokaci ƙanƙani kamar yadda yanzu ya ga uban gidansa ya miƙe garau ko sanda babu  ba.

“Kai ko dai yau idanuna ba dai-dai suke gani bane? Ga wancan ɗan shaye-shayen da ban taɓɓa ganinsa ba yazo yana neman yanken maƙogwar!, In shi be kashini ba yanzu kuma ai wannan abin al'ajabin sai yasa kwanyata ta dena aiki, kai ko dai abinda ake faɗe akan Mutumin nan gaskiyane!  Na yana aiki da matsafa?” Duk maganar da yake a cikin ranshi yake cike da fargaba tuna babu mai bashi amsa.

Buɗewa Motar get ɗin yayi ta fita,  ya mayar ya rufe yana nufar bencin zamansa zai zauna.

“Kai! Lurwanu zu nan! ”
Suwiɗi ya rangaɗa masa kira.

Da sauri ya tahu gurinshi yana risinar da kai yace“Alhaji barka da dawo wa ya ƙarfin jiki?”

“Ba wannan yasa na kira ka ba waɗɗan can abebaɗan waya kawosu gidan na? ” Suwiɗi yayi maganar yana nuna Karnukan dake  ƙofar shiga falo suna kaɗa jela da zaro harshe.

JIDDO(Gidan Aurena) Donde viven las historias. Descúbrelo ahora