JIDDO (Gidan aurena) Part 12

5 0 0
                                    


            *JIDDO*
    *GIDAN AURE NA*
               *BY*
  *MAMAN NABEELA*

*Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y

*Page* 1️⃣2️⃣

Ban ankara ba kawai naji ya chafki dukiyar fulanina yana sha kamar wani jariri, duk da gaf nake da fita hayacina, saboda azabar da cikina keyi.  Buɗe idanuna nayi cike da tashin hankali ina ce wa “innalilahi wa inna ilaihirraji un na shiga uku!, Suwiɗi anya kanka ƙalau kuwa”? Nayi maganar ina kiciniyar kwatar kaina.
Sake chakumar dukiyar fulanina yayi yana daɗa yi musu wata mahaukaciyar zoƙa wanda tsananin tashin hankali bansan sanda na da-da dage na kurma wani uban kuka ba ina kuma  faɗin“innalilahi wa inna ilaihir raji un Allahuma ajirini filmusibati, wannan wace iriyar musifa ce yau nake gani?. Suwiɗi anya kuwa a hayyacinka kake? Nonon da jariri yake sha fa kake zuƙewa! Lah haula walaƙuwata illah billah. Dan darajar Allah ka sake ni” na ƙare maganar cikin kuka ina kai masa duka.  Ko nuna alamar yaji me nake faɗa beyi ba sai da ya zoƙe min Nono tasss sannan ya kyaleni dan kansa.

Bana ganinsa sosai saboda duhun Ɗakin amma lokacin da ya ɗaga ni sai naga kamar hannunsa riƙe da wani kyalle yana ɓoyewa  a bayansa yana murmushi.

Ko kallona bau sake yi ba naga ya koma gurin da jaririna yake,  ya ɗaukeshi yayi hanyar ƙofa cike da tashin hankali nake ƙoƙarin tashi ina ce wa“ina zaka kaimin yaro?  Ka dawo ka..... ” ban ƙarasa maganar ba  ya fice da Hussain ina tashi dafe da cikina da yake jini ina ƙoƙarin binsa,  hajijiya ta kwasheni na zube a gurin ban sake sanin me yake faruwa ba.

Buɗe idanona nayi da suka yimin nauyi ina bin gurin da nake da kallo ganin su Salma da Asma'u da su Abdul duk sun zagaye ni.  Ina ƙoƙarin tuna abinda ya faru dani ganin har ruwa aka juna min.
“Ammy sannu ya jikin?”
Asma'u da na gani a gefena tayi maganar.

“Da sauƙi”? Na amsa mata da kyar saboda maƙogwaro na daya bushi. Su Salma ma duk sannu suka yimin, na amsa musu da ka.

Gabana kawai naji ya faɗi sanda ƙwaƙwalwata ta tuna min abinda ya faru cikin tashin hankali  nace “ina Hussain? ” ina waigawa ko wane lungu da saƙo na ɗakin haɗi da yinƙurin tashi.

Asma'u da Salma ne suka yi saurin maida ni kwance Asma'u na ce wa“Ammy yana bayan Umman su Salma fa, ki kwantar da hankalinki Dr- Hajar ta ce jininki yayi mugun hawa ga gurin da aka yi miki aiki shima yana neman buɗewa Dan Allah Ammy ki kwantar da hankalinki. Wai me ya sameki ma kika shiga wannan halin? Kinga faɗan da Dr- Hajar tayi dana kirata a waya tazo taga halin da kike ciki!
Saboda ta matsa da tambayar sai an faɗa mata me ya sameki kika shiga wannan halin fa cebwa nayi ina shigowa naganki a sume inaga faɗowa kika yi. kinga yadda tayi ta faɗa ai ga Salma nan har tana cebwa bama kulawa dake in kin mutu mu zamuyi asara.
Asma'u tayi maganar cikin ɗan jin zafin abinda Dr ta faɗa mata.
Dr- Hajar ɗaya daga likitocin da take kula da ita ce lokacin da aka yi mata tiyata a *MAI NASARAH Hospital* basu da nisa da ita  lokacin da za'a sallamesu sukayi musayar number waya da ita.

“Dan Allah Ammy ki kwantar da hankalinki wlh sosai Dr tayi faɗa kamar yanda Asma'u ta faɗa miki”.

Binsu nake da kallo ina gyaɗa kaina ba wai dan hankalin nawa da suke faɗin na kwantar zai kwanta ɗin ba sai dan su nasu hankalin ya kwanta,  ganin irin damuwar da suke ciki akan rashin lafiyar tawa.

Taya hanakalina zai kwanta mudi ina tuna abinda yake faruwa bayan dawo wata gidan.

Da kuma abinda ya faru yau ai hankalina ba zai kwanta ba dan ko a fina-finai da littattafan hikaya ban taɓɓa jin irin haka ta faru ba.

Tabbas nima na  fara ɗorawa Suwiɗi ayar tambaya? Da gaske zariginsa nake, zargi kuma wanda in har ba sanin ainahin abinda yake aikatawa nayi ba hankalina ba zai taɓɓa ƙwanciya ba.

“Ina Babanku? ” na tsinci bakina da tambayar su Asma'u.

Asma'u tana ƙoƙarin yin magana Lubabatu ta shigo.
“Ashe kin farka! Ya jikin? Wai Suwiɗi kike tambaya ai be kwana a gida ba yau” Lubabatu tayi maganar tana kunto Hussain dake bayanta ta miƙawa Asma'u.

Zaro idanuna nayi cike da sabon tashin hankali na ce“be kwana a gida  ba fa kika ce? Umman Harisu ”

“Eh Ammy be kwana a gida ba tun da sa-safe nida Salma muke zuwa ƙofar ɗakinsa amma a rufe yake”
Asma'u tayi maganar tana duban Ammy zuciyarta cike da saƙe-saƙe.

“Ai ni wallahi yanzu sha'anin Suwiɗi daɗa tsoratani yake sam yanzu fa baya zama, ina faɗawa Harisu ma sai ce wa yayi ya samu labarin wai wasu ke ɗaukarsa suyi wajen Gari a wata dalleliyar Mota. Duk yanda kuma ya kai ga son ganu ina suke zuwa ya kasa. Masu zuwa gurinsa ma neman temako kusan kullum sai sun zu yanzu har sun gaji sun rage zuwa, Allah dai yasa ba wani mugun abun yake yi ba a inda yake zuwan” Lubabatu tayi maganar cikin damuwa tana tausayawa rayuwarsu saboda  sanin halin Suwiɗi da tayi.

Da amin Jiddo ta iya amsawa zuciyarta tana daɗa faɗawa cikin tunani iri-iri.

Ruwan da aka saka min ne ya ƙare Asma'u da likitar ta nuna mata yadda zata cire,  ita cire min.  Bawa Salma Hussain tayi ta temaka min ta rakani ƙofar  banɗaki tsayawa tayi har na fito sannan ta temaka min na koma ɗaki.

Bayan na zauna Asma'u ta jingina min filo a bayana dan naji daɗin zama. Ruwan zafin da Ummansu Harisu ta kawo Asma'u ta haɗa min shayi me kauri ta miko min na fara sha, bayan na shanye Hussain daya tashi Salma ta miƙo min karɓarshi nayi na fara bashi Nono sai da yasha ya ƙoshi sannan nace da Asma'u ta miƙo min ruwan rubutu na da nake sha. Kamar da wasa Asma'u ta fara dubawa amma babu ruwan rubutu babu dalilinshi ko ruba ɗaya babu.
Abin mamaki baya ƙarewa dan ni nama rasa me zance tsabar kaina ya kulle taya za'ace ruwan rubutun da aƙalla ya kai roba biyar wadda bansha ba ta ɓace ɓat.

“Asma'u ko dai kin sauya masa guri ne?  ki kuma dubawa” nayi maganar ina duba gefe da gefe na.

“Ammy wallahi a nan gurin dai anan na ajiyeshi ban sauya masa guri ba”
Asma'u tayi maganar tanaleƙawa har ƙasan gado.

“Gobe sai kuje da Salma ku amso min wani ”

“Ammy ai yanzu ma zamu iya zuwa tunda bawani nisa ne da gidan ba, Ammy ba na tambayi Zainab da Abdull ko sun ɗauka kin sansu da kwaɗayin ruwan roba”

“Eh tambayesu muji Allah sa basu lalatashi ba” nayi maganar ina ƙoƙarin a jiye Hussain da ya koma bacci.
Ko gama ajiyeshi banyi ba naga jikinsa ya fara wata jijiga kamar an juna masa lantarki idanunsa sun ƙaƙafe.

“Innalilahi wa inna ilaihirraji un! " na faɗa ina ɗagoshi, salatin da nayi yasa Asma'u, Salma, Mamansu Harisu duk suka matsu suna tambayar lafiya......?

**********

Wani ƙaton gidane me ɗan karen girma  cikin wani ƙongurmin jeje, wasu mahaukatan geta-getai ne a ƙofufin shiga gidan.

Sautin dariya na wata murya ne mara daɗi ya fara tashi yana karaɗe ilahirin dajin, kafatanin dajin ne ya fara  amsa amun wanda har ƙasar dajin da bishiyo ke motsawa.

Mutane ne aƙalla sunkai kusan hamsin sunyi durƙoso tamakar masu yin ibada tsirara haihuwar Iyayensu kansu rantal babu gashi sautin muryar ne ya kuma karaɗe gurin....... ✍️

Pls
_Share & share fisabililah_ 🙏🙏🙏

 

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now