GIDAN MIJINA

62 3 0
                                    

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

     Story & written by

MAMAN AFRAH

         Page 26--27

 
  Ya abdullahi ne juya ya doka mata harara.

"lefin me tayi kake harararta kar na sake gani"hajia ta fada da kashedi.

"amma hajia bakya ganin........
Sakkowar daddy itace ta katse maganar da ya abdullahi ke kokarin yi.

"Barka da sakkowa daddy"kb yace yana murmushi.

"barka dai auta ko kuma auta ya girma yanzu"daddy yace da zolaya yana dariya irin tasu ta manya.

"ay daddy yanzu ya girma ba shine autan ba"ya abdullahi shima ya fada yana dariyar

"daddy ay gaba da baya nine auta"kb ya fada yana zumburo baki.gaba daya falon dariya aka saka banda jamila da tayi karamin tsaki da ba wanda ya jita sai hajia,itakwa aysha murmushi tayi kanta har lokacin a sunkuye.

"a toh shikenan mun ji kai ne auta"cewar daddy yana samun wuri ya zauna.

Bayan kb ya gaishe da daddy aysha ma mikewa tayi  taje har gaban daddy ta tsugunna har kasa ta gaishe dashi cikin mutuntawa da kuma girmamawa.amsa mata yayi yana mai jin dadin tarbiyar yarinyar yana kuma godewa Allah daya bashi suruka kamar aysha lallai har gobe yana alfahri da ita a matsayin matar dansa kabeer.komawa tayi kasa wurin zamanta ta zauna ,a yayin da mutum uku suka bita da harara,hajia ummulkhairi,da kuma facalarta jamila suna jin haushi da yadda take.ita dama jamila ta gaishe da daddy tun sanda sukazo sai dai tana daga kan kujerar da take zaune ta gaishe dashi,

A alhamdulillah nagode Allah daya bamu rai da lpia ,ina kuma kara gode masa daya bani iko da dama na taraku domin mu tattauna magana wacce nake fata ta kawo gyara akan gyaran da nakeso ,ta kuma zama sanadin gyaruwar komai kamar yadda nake son hakan ya kasance.

gyaran murya yayi kafin yaci gaba da bayani.

wato shi ubangiji shike iko da kowa da kuma komai,shike bayarwa kuma shike hanawa.yanayin yadda yaso a lokacin daya so,duk wanda kaga Allah ya bashi to shi yaga dama ya bashi bawai dubara ko wayon mutum din ne yasa ya samu.kuma kowa dana ne yadda kowace uwa ta dauki ciki tsawon wata tara ta kuma shayar tsawon watanni tara kamar yadda yazo a  alqur,ani mai girma cewa (ciki da kuma shayarwa watanni talatinne)dan haka kowace uwa haka tasha wahar haifar danta ta kuma shayar dashi da kuma wahalta masa a rayuwa.kuma babu wata uwa da bata son danta kowace uwa ka gani akwai soyayyar danta dankare a zuciyarta,dan haka kowa da kaddararsa mai kyau ko marar kyawu.sannan kowane mutum an rubuta masa arzikinsa da ajalinsa da aikinsa sannan da makomarsa tun kan yazo duniya duk wanda ka gani da arziki Allah ne yayi nufin ya bashi,haka kuma duk wanda ka gani a talauci haka shima Allah yakeso ya ganshi dan haka wulakanta wanda kafi da wani abu ba naka bane wala ilimi daukaka,mulki ,ko dukiya .dan kaima duk wannan abubuwan daka mallaka anan duniya zaka barsu da zarar mala,ikan mutuwa ya ziyarceka shikenan daga kai sai farin llikkafaninka wanda dashi ake kai kowa kabari mai kudi ko kuma talaka.kai ko ba,aje ga mutuwa ba wata rana zaka wayi gari ka rasa koma menene kake takamar ka mallakeshi.

   Domin rayuwar nan ba tabbas ba gareta ,yanzu zaka ga mutum ana jimawa ace maka ya mutu🥲mutum ba komai bane wlh shi yake daukan  kansa wani daga an zare maka rai shikenan ka zama gawa kuma a lokacin za,ayi jana,izaarka a kai ka makabarta a saka a rami a rufe shikenan daga kai sai halinka.dan haka nake jan hankalinku nake kuma ankarar daku a matsayinku na iyalaina daku bi duniya a sannu domin bata da tabbbas ko kankani! mu guji duniya Allah zai so mu ,sannan mu guji abin hannun mutane suma mutane zasu so mu.shiru yayi yana bin fuskokinsu da kallo yana kuma karantar yanayinsu gaba daya.duk sunyi shiru da alama kuma zancen na shigarsu domin gaba daya sun yi sanyi.  
Abu na gaba da nakeso na yi magana akansa shine akan zamantakewar auratayya ,ku mata kuyi biyayya ga mazanku ,kuma mazan kuyi adalci a zamantakewarku.sannan hajia inaso ki sani cewa aysha surukarki ce kuma yarinyace mai biyayya,sannan kuma dama Allah ya rubuta ta a matsayin matar kabeer tun kan tazo duniya.dan haka ki yiwa Allah ina rokonki ki da ki karbeta a matsayin suruka.sannan inaso ki sani ba komai da mutum keso ko kuma yake son kasancewarsa ba yake samu sai abinda Allah ya kaddara.yau kusan watanni kenan da aurensu amma ko sau daya baki taba sanyata a idonki ba karfa ki manta itama 'ya ce kuma uwa da ubame suka haifeta kuma suma suna sonta kamar yadda muke son namu yayan,dan haka ina rokonki daki sakar mata fuska ki kuma karbeta a matsayin suruka domin  rayuwa bakasan mai gaba zata haifar ba.sannan baka san mai maka rana ba sai Allah."yana kaiwa nan ya koma ya jingina da jikin kujerar

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now