GIDAN MIJINA

124 4 0
                                    


*_______________________________________*

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

Story & written by

MAMAN AFRAH

     Page
    
    40

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

    "Ba su kad'ai aka kai ba gyatumarsu ta je dasu shi ne ta shuka rashin arzik'i ta taho ta baro su a can"Ummulkairi ta ce tana kanne ido d'aya.

"Bangane ba ita Aysha ce ta je ta yi rashin mutunci" Kb ya ce da mamaki.
Aysha kwa da ke tsaye sakin baki ta yi galala tana kallonsu.

"Eh mana  har fa zagin Hajia ta yi"

"Zagi "ya fad'a a zafafe.

"Wlh kwa dan Hajia har da hawaye ta yi na takaicin zagin da Aysha ta mata...
 
Ai kafin Ummulkhairi  ta kai aya ya yi kan Aysha kamar zai kai mata duka, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, Aysha tana so ta masa bayani ya k'i saurarenta, Fauzy ma da zata yi magana ya dakatar da ita kai a tak'aice sai da Kb ya zagi Aysha ta uwa ta uba .Aysha kawai hawaye ke zuba a idonta itama Fauzy  ba, a barta ba a baya dan tana da wayo sosai kuma tasan ba,a kyautawa mahaifiyarta  ba, ta kuma san Mamanta bata zagi Hajia ba tana so ta yiwa Abban bayanin yadda aka yi amma yaki ya saurareta. Ummulkhairi  kwa ranta fari kal ta had'a ta ji dad'i dan da sanin Hajia ma ta taho ta yi had'in wannan.

  Wannan shi ne abin da ya janyo Kb ya sakeni lallai namiji duk hak'urin da nake k'unsa a cikin gidansa amma bai gani ba sai da ya ci wa iyayena mutunci!

  Da asuba bayan na yi sallah  na yi azkar, karamar trolly na d'akko na sanya kayana a ciki tare da abubuwan da zan buk'ata, fitowa na yi na je d'akin hindu mai kula min da yara na sanar mata zan tafi ta kulamin da yara na, na dauki kud'i masu yawa sosai ta ji babu dad'i jin sakin da na ce mata yaa shiga tsakaninmu. Haka na shiga d'akin yaran na gansu suna ta barci abinsu, na fito jin hawaye na neman kufce min ni kuma bana buk'atar yin kukan yanzu. Sashe na na dawo na dauki jakata da akwatin sai wayana, fitowa na yi na bude  kofar na fita mai gadi na ta bani hak'uri domin ya san ba lafiya bace za tasa na fita da akwati da sassafen nan kuma ba tare da yaro ko d'aya ba.

  Ina fitowa bakin titi na samu napep dan lokacin  gari ya yi haske sosai akwatin na sanya a xiki nima na shiga na zauna na fad'a  masa in da zai kai ni. A dede kofar gidan mu nasa ya tsaya na biyashi kudinshi  na kinkimi akwatina na shiga buga kofar gidanmu, wata iya salame da suke zaune tare da Umma a gidan kanwar maman Ummance ita ta bude min kofar gani na da akwati yasa jikinta yin sanyi, jakata ta karba ni kuma na shigo da akwatin Umma dake shara ta yarda tsintsiya ta tsaya fuskarta da tsahin hankali  tana kallona, jikina ne ya k'ara  yin sanyi ganin damuwa k'arara a fuskar Ummana. D'aki na shiga da akwatin na ajiye, haka muka zauna jugum jugum na fad'a  musu duk abin da ya faru ina fad'a  ina kukan takaici dan gaba d'aya  sai nake jin kamar ma yanzu ake min duk abin da aka mini.

   BAYAN WATA UKU

  Lokacin har Aysha ta yi iddah, dan haka kawu habibu yasa ta yi jamb kuma Allah  ya taimaketa ta ci aka nema mata admission a B. U. K nan take Aysha ta fara karatu  babu kama hannun yaro, dan dama tana son karatu  gata da bala, in k'ok'ari sannan kuma ta hadu da k'awaye wayayyu suke koya mata komai na rayuwa dan  idan  ka ga Aysha ba zaka ganeta ba. Kamar ma ba ita ta haifi yaranta ba ba wanda zai ganta yace ba budurwa bace. Ta kwantar da hankalinta tana yiwa y'ay'anta addu, a tana karatun ta hankali  kwance. Sai dai  samari da manyan Alhazai da ke mata tururuwa ita kuma tana sallamarsu dan babu sha, awar aure a ranta yanzu dan kayan d'akinta ma tuni aka kwaso ta sai da wasu wasu ta jerawa Ummarta .Sannan ta kan sari takalma da pad ta mata da kayan shafa tana tafiya dasu makaranta tana siyarwa abinta.

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now