GIDAN MIJINA

57 2 0
                                    

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Story &  Written by

MAMAN AFRAH

Page      
     24---25

  Kabeer ka fice min da ita daga falo nace"

"Toh"yace ya kalli humaira dake zub da Hawa ye.

''Dan Allah ki yi hkr in wani abu na miki ki yafe min"Aysha tace tana kuka.

"Ke dalla malama rufe min baki ke kuma a wa har zaki min laifi,a inama kika isa ki ganni bare hr ki min wani lefi?in ban da kabeer ya shigo dake wlh ko mai aiki baki isa in dauke ki ba,bare kuma har ki samu damar fadi in fada dani kaunarki ne bana yi ko kadan.dn haka karki kara zuwa inda nake,bada yawu na aka aureki ba ko Kaya da aka Hada na lefe ba sa Hannu nah a ciki tun da kince sai mai arziki to aiko bazaki samu zama lpia ba"tace tana nuna mata kofa da Hannu.
Aysha da gudu ta juya tana sa hannu ta rufe bakinta sabo da kuka da yaci karfinta

Kb ne ya juya da sauri zai rufa mata baya.
"Kar ka kuskura ka fita"hajia tace rai bace gannin kb dk ya wani rikice.

"Hajia ki yi hkr bata da laifi wlh"

"Wato bata da laifi wai kai mai mata to ka bini a hankali wlh"Tace ta samu 1seater ta zauna tana wani hade rai.kb kuwa a kasa ya zauna ya sunkuyar da kai kasa yana mamaki na can jawar hajia dan ya auri matar da bataso.dk da bata son talaka amma bai zaci Abin ya kai haka ba.

"kaga matar da nake so ka aura in hr kanaso mu dai daita "tace tana nuna masa ummulkairi data sakko daga stairs tana wani murmurshi.
"Toh"yace yana ji kamar ya je ya make ummul khairi domin haushi.

"Ya kb yaushe zan zo muku hutu"ummulkhairi tace da izgilanci dan ta kara bata masa rai ta faki idon hajia ta kashe masa ido daya.

"duk ranar da kika shirya "yace a takaice yana cije lebenshi na kasa .

"ummulkhairi zo zauna za muyi magana"hajia tace tana nuna mata wurin zama.
Dab da kb taje ta zauna a maimakon inda hajia ta nuna mata.

  aysha na fitowa ta kama hanyar da zata sadata da get din din gidan,tafiya take tana kuka har hawaye na neman hanata ganin gabanta.sosai taji maganganun hajia sun taba mata zuciya tabbas tozarci bashi da dadi ko kadan da ace tasan abinda zata tarar da ko karyar rashin lpia tayi dan kar tazo a ciwa iyayenta mutunci abinda ba,a taba mata ba a rayuwarta lallai yau da ace watace ba surukarta ba bazata taba kaleta ba wlh sai  inda karfinta ya kare,dan duk hakurinta da rashin son fadanta bazata yarda a ciwa mahaifanta zarafi ba ko zuly da taje gidansu tayi rashin kyautawa dan bata nan ne amma koda bazataci riba ba sai iya inda karfinta ya kare.ita kawai so take taje taga shin hajia kamarsu daya da kabeer dinta ko kuma basa kama ita ko a mafarki bata taba kawo cewa surukar tata bata ko son ganinta,ashe daman shi yasa kb bai kaita ta gaisheta ba amma hakan bai sa tayi wani tunani marar kyau ba akanta ba.domin yana da kyau ka yiwa mutum kyakkyawan zato ,Allah sarki rayuwa kenan kowa da irin tashi kaddarar.ita kuma da kaddarar suruka aurenta yake domin bata hango sassauci ko na second daya ba a fuskar mahaifiyar mijin nata.wasu zafafan hawayen ne suka kwaranyo mata tunawa da tayi a haka zata rayu duk da ba tare zasu zauna ba kuma ba ita ke aurenta ba amma ai dole ita ke da iko akan danta.sannan ga wannan ummulkhairin itama kai abin sai dai addu,a.

"kanwata"

Aysha dake kokarin bude karamar kofar get din zata fita ta jiyo sautin kiran a bayanta,saurin sa hannu tayi ta goge hawayen dake fuskarta ta juyo tare da kakaro murmushi.

"ya abdullahi"tace tana gyaran murya jin sautin maganarta bai fito sosai ba muryarta ta dan shaqe kadan.

"ina zuwa kuma naga kina kikorin fita?"yace yana rufe murfin motar.

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now