GIDAN MIJINA

89 4 0
                                    

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

    Short story

  Story & written by

   MAMAN AFRAH

MARUBUCIYAR
RAYUWAR MARYAMU
     
AND NOW

GIDAN MIJINA

Alhamdulillah I am back again🤗

*SADAUKARWA GA  BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏*

     Page 7_8

Kururuwa saleh Keta faman yi ,yana neman agaji da kuma dauki daga Jama,a,bubbuga gidajen dake makotaka dasu yake,ya buga nan ya dawo ya buga,can kan kace meye wannan mutane sun taru ana ta kokarin kashe wutar.wasu ruwa suke dakkowa daga gidajensu wasu kuma da ruwan kwata suke kashewa,kafin kace me an kusa kashe wutar,dan lokacin da yan fire Service suka zo kadan suka tarda wutar

   Bayan an kashe wutar aka shiga fito da gawarwakin,domin gdn yayi kurmus sai kaurin hayaki dake tashi,haka aka fito dasu gaba daya sun kone babu wani mai sauran rai a cikinsu🥲(UBANGIJI KA MANA TSARI DA WUTA,YA ALLAH KA HARAMTAWA WUTA CIN NAMAN JIKINMU DUNIYA DA LAHIRA AMIN).mutane kowa na fadin albarkacin bakinsa,wasu suce ko tsakace ta hada gobarar ,wasu kuma suce wutar nepa ce tayi spark,Allah ne masani .shi dai saleh yana kan gawarwakin a durkushe yana kallon ikon Allah.kuka yake dk ya zama kamar tabi tabi dn ma dai yana ambaton" innalillahi wa inna ilaihir raji,un"Gasu nan a laye akan babbar tabarma  dake gdn makocinsu aka shiga dasu,yaya salisu,iya a,i zainabu,da kuma ihsan.tab lallai dan adam ba kowa bane shi ,shine ke daukan kanshi wani abu.

   Washe gari aka musu sutura aka kaisu makwancinsu,tun a ranar da daddare  m.rabi,u ya ya tafi da saleh gdnshi dan daman kawai a kofar gida aka dn zauna ake karbar ta,aziyya.suma yan uwan zainabu a can gidansu zasuyi zaman makoki ,sbd gdn bashi da kyan gani ma.haka saleh ya dawo wani shiru shiru dashi dn sosai mutuwar ta tabashi,sai dai ya zauna yayi shiru sai da m.rabi,u ya dage sosai akanshi da Addu,a tare da nasiha sannan ya dn fara sakarwa yana dan walwala

     Bayan wata takwas da rasuwar su salisu, dole m.rabi,u ya matsa masa akan ya fara sana,a domin zama haka babu dadi,dk da m.rabi,u bai taba gajiya da daukan dawainiyar sa ba .daman akwai kudi 40k da mai gdn da salisu ke haya ya kawo masa ,kudin hayar da salisu ne ya bada na shekara 80k to kuma shekarar daya biya kudin nata bata kare ba,Allah ya masa rasuwa ,to shine  ya kawo masa rabin kudin.dake mutumin dattijo ne mutumin kirki.wandan nan kudin sune m.Rabi,u ya bashi yaja jari dasu tunda yanzu baya son tukin napep dn.

  Saleh ya yanke shawarar fara sana,ar kayan miya sune yaga babu a anguwar,sai an je  can bakin titi ake siyowa.runfa aka buga masa ta kwano da bencina,ya saro kayan miya dasu salad cabej d.s.nan kasuwa ta bude sosai ake ciniki dn dama mutanen anguwar sun gaji da zuwa bakin titi siyayya.

  Zaman saleh a gdn m.rabi,u shine sanadin kulluwar soyayya,tsakaninsa da atika,atika diya ce a wurin m.rabi,u sai kaninta habu.wannan soyayya itace takaisu ga aure .sunyi aure suna son junansu a inda wannan sana, a ta kayan miya itace take rike da saleh da matarsa atika cikin rufin.dan ci da sha zuwa sitira dk  baya gagara da ma sauran abubuwan bukata na rayuwar yau da kullum,har ma
ya kan taimakawa uba kuma sirikinsa m.rabi,u.

Cikin zaman takewar auratayyarsu ce,Allah ya azurtasu da diya mace,saleh ya sanya mata sunan kakarsa iya a,i. wato aysha,suna kiranta da humaira. Yarinya ta taso cikin gata da kulawa dai dai karfinsu.

Aysha yarinya kyakkyawa ajin farko a kyau,gata da shiga rai dan dk layinsu kowa yasan aysha.akwai natsuwa ,hankali uwa uba hakuri. Dan tun tana karama bata da yawan hayaniya,har dai ta isa shiga scul aka sanya ta Anan wata scul dake  cikin anguwarsu, MUFTAHUL ILM dan daga gdnsu babu nisa dan haka a kafarta take zuwa tana dawowa,dan idan ta tafi da safe to takan dawo gida kafin karfe uku tayi ta koma islamiya dan duk hade suke boko da islamiya.

GIDAN MIJINAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt