GIDAN MIJINA

65 4 0
                                    

🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

Story & written by

MAMAN AFRAH

     Page
38--39

"Daddy lafiya?" Ummulkhairi  taa fad'a hankali tashe dan gaba d'aya yanayun nashi ya bata matuk'ar tsoro. Daddy dai bai ma san tana yi ba sai sunayen Allah  yake ta ambata, ji yake kamar kanshi zai rabe gida biyu can kuma sai ya ta ga ya fara bin jikin bango yana dafawa yana d'aga kafafunsa daker kamar wanda suke a d'aure. Gaba d'aya Ummulkhairi  ta gama tsorata, sai binsa take da kallo har ya shiga bayin dake can karshen falon daga korido, sai jin k'aran amai ta ke yana ta kolon amai ji tayi daman bata fad'a masa  maganar ba, gashi yanzu ta janyo ya shiga wani yanayi wanda dole Hajia ta san me ya faru.

  "Ummulkhairi "ta jiyo muryar Daddy kamar daga sama, dago idanunta tayi take kallonsa, abin mamaki da k'afafunsa yake tafiya ba tare da ya dafa bango ba. Ruwane a fuskarsa da alama wanke  fuskar ya yi.

"Ina Hajia?"ta ji ya tambayeta  duk da bata amsa kiran da ya mata ba sai binsa kawai da take da kallo.

"Ba ta tafi Abuja ba" ta bashi amsa jikinta a sanyaye dan tun da ta ji ya ambaci ina Hajia take to tabbas ya dawo hayyacinsa, tun da dai ai yasan Hajia ta tafi Abuja biki to mesa yake tambaya.

"Abuja kuma lafiya tayi tafiya bata sanar min ba? "

"Biki ta tafi kuma ta sanar maka" jim ya yi yana d'an nazari sai kuma ya ce

"Okay bari na hau sama"ya juya ya hau matakalar benen a nutse kuma kana ganinshi kasan ya dawo Daddy na asali domin lokacin da baya hayyacinsa  ko  magana yake sai ka ga alama kamar dai wani zautacce.Binsa Ummulkhairi  ta yi da kallo har ya b'acewa ganinta.

"wayyo  ni na b'allo ruwa na jik'awa Hajia aiki, kai hatta nawa aikin ma ya jik'e gashi Daddy ko ta kan maganar dana fad'a masa bai bi ba"ta ce tana mik'ewa ta fito daga part din daddy ta nufo na Hajia. Jamila ta tarar zaune tana shan ice cream tana kallo sai wani yatsina fuska take, kallo d'aya Ummulkhairi  ta mata ta haye sama ba tare da ta kuma bi takanta ba.
 
Bayan dawowar Hajia

A lokacin  da ta dawo Daddy ya fita dan haka wanka ta yi ta huta abinta hankali kwance. Shima Daddy da yake haushinta yake ji yana gani ta yi tafiya bata sanar dashi ba sai kawai bai bi takanta ba ya wuce sashensa ya watsa ruwa ya kwanta tunda lokacin  har karfe tara na dare ya yi, ganin Daddy bai je inda take ba tunda tasan itace da gidan shi yake mata abinda takeso tun da ta gama dashi. Sannan ko da Jamila ta sanar da ita Ummulkhairin  ta je kd bata kawo komai a kai ba tun da tasan tana xikin damuwar mutuwar aurenta, kuma tunda ita tayi tafiya bazata ji dad'in gidan ba tunda ba wani shiri suke da Jamila ba.

Tashi tayi ta nufi part d'in Daddy, sama ta haura ganin duk fitilun a kashe yasa ranta k'ara b'aci, tana ganin kenan har ya kwanta ba tare da ya damu da ya ganta ba. Kunna fitilun ta yi, ta je ta tsaya a kansa k'ememe Daddy kwa ba barci yake ba yana jinta ya watsa yinta. Hannu ta mik'a ta janye bargon da ya rufa dashi.

"Gaskia ne wato har ka samu damar kwanciya ba tare da ka je ka min sannu da zuwa ba? Ka kuma duba na dawo lafiya ko akasin haka" ta fad'a rai bace tana wani masa fad'a  kamar wata gyatumarsa. Mamaki ne ya rufe Daddy wanda hakan yasa ya kasa ko da motsi.

"wai ba magana nake maka ba? Ta zafice shi kamar mai k'ok'arin kai masa duka. Tashi zaune Daddy ya yi a nutse sannan ya dubi Hajia yace

"Kin ci albarkacin y'ay'a kuma sa'arki d'aya  bana k'aunar yin saki sabo da Allah bayaso kuma duk lokacin da aka yishi sai al, arshin Ubangiji ya girgiza amma wlh da a yau sai na datse igiyar da ke tsakani na da ke!!! "Daddy ya ce yana nunata da yatsa.
Gaban Hajia ne ya bada rass, ta hadiye wani yawu dank'ararre a mak'oshinta, lokaci  daya wata zufa ta fara jik'a mata jiki. Gani ta yi Daddy ya koma mata kamar wani  zaki mutumin da sai yadda ta yi dashi amma yau yake mata ikirarin zai iya sakinta.

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now