GIDAN MIJINA

120 6 0
                                    

AN AFRAH♥️🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

    Short story

  Story & written by

   MAMAN AFRAH

MARUBUCIYAR
RAYUWAR MARYAMU
     
AND NOW

GIDAN MIJINA

Alhamdulillah I am back again🤗

*SADAUKARWA GA  BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏*

  Page 3_4

Tana nan tana sake sake da maganganu ita kadai, ta zauce kamar dai wata marar hnkali,kallon agogon bangon dakin tayi wanda yake aiki babu jira ko kakkautawa.domin shi lokaci tafiya yake baya jira kwata kwata Kuma matukar lokaci ya wuce to kwa ya wuceni har abada bazai sake dawowa ba,sai dai wani makamancinsa mai irinsa ma,ana mai sunanshi Amma lokaci dayane tak kuma in ya wuce baya dawowa baya.
  10:45 haka lokaci ya nuna wani bacin ran ne ya kara lullube wanda take ciki dk da ba yau bane karo na farko da kabeer ya kai wannan lokaci a waje ba,amma yau sai taga lokacin baya yin sauri hkn kuma baya rasa nasaba da jiran dawowarsa da takeyi dk da takan jira dawowarsa a dk sa,ilin da yayi dare dn kota kwanta ma barcin Bayard zuwa ,sai dai wani lokaci barcin yakan dauketa ba tare data sani ba,domin ance shi barci barawo ne.dan wani lokacin ma har yakan kai sha daya gashi dai tun dab da magriba ya dawo daga kasuwa,wanka kawai yayi yaci abinci wannan sabanin ya shiga tsakaninsu,shine ya kama hanya ya fice,itama wacce tazo ta hada mata sabanin ta tafi gashi ita sun barta da ciwon rai.kwafa tayi tana jijjiga manta alamar ay zaka dawo gida dk tsawon lokacin da zaka dauka a wajen.dk da ba yau bane ya fara dadewa.

  Tana nan a haka can sai taji karan bude get din gdn,saurin duba agogo tayi lokacin har sha daya tayi da minti biyar,maida idanunta tayi ta rufe sannan ta budesu dai dai nan taji tsayuwar motarshi.saurin kokarin tashi zaune tayi dan a lokacin ne zuciyarta ke kara azalzalarta akan aikata dk abubuwan data gama saka mata ,domin yau tabbas ba gudu babu ja da baya.kantane ya wani bala,in sara mata wanda hkn yasa tayi saurin komawa ta kwanta.tana jin lokacin daya shigo cikin gdn,domin tana iya jiyo maganarsu shi da mai gadi,tasan bai wuce kaya ne mai gadin ya dakko masa daga mota.dake bangarensa da nata a kusa da juna suke ,ba a jere suke da juna ba sai dai suna kallon juna. tana jin lokacin daya bude kofar falon nasa ya shiga,ita dai tana nan a yadda take.
    Bangaren kabeer kwa daya shiga Part dinsa mamaki ne fal ransa,daya ga bai ga aysha a cikin dakinsa ba ,da farko daya bude kofar falon bakinsa dauke da sallamq ganin bata falon sai bai kawo komai a ranshi ba.dn yasan yakan sameta a falo indai ya kai lokaci irin wannan koda kuwa ba kallo take ba haka zata zauna ta jirashi,idan kuma ta gaji da zaman falon takan koma can bedroom dinsa ta kwanta ,hr sai ya dawo,wataran barcin ya kan dauketa Amma hkn da wuya dan bata iya rintsawa idan bai dawo ba ,dk da kuwa ba wani tarba mai kyau zata samu daga gareshi ba.ganin bata kn bed dn kawai sai ya cire mamakin rashin ganinta a tunanisa ko ta shiga bayi,kayan jikinshi ya shiga ragewa da Tunanin in ta fito daga bayin ya dn watsa ruwa.bayan ya kammala cire kayan sai ya dauki tawul ya daura a kugunsa ya koma kn gadon ya
dn kishigida,yana Jiran fitowarta dan shi kwata kwata yama manta da abinda ya faru tsakaninsu,bayan ya dawo kasuwa.jin shiru bata fito ba Kuma baya jin motsi ko karan ruwa yasa ya tashi domin dubawa,kwankwasawa yayi domin karya fara budewa ta tsorata Tunda batasan ya dawo ba dk da yasan mawuyaci ne ace bataji zuwan nashi ba,yana tura kofar yaga wayam babu alamarta,sororo yayi yana bin bayin da kallo kamar dai yana son gano rashin wanzuwarta a wurin,saurin banke kofar yayi ya maido kallonsa cikin dakin yanaso ya gano iya lokacin data dauka bata dakin shin sakanni ne ko kuma mintina ne kai kodai awanni ne ma? Yake yiwa kansa tambayar,ganin ya gagara gano amsar yasa ya baiwa kansa amsa da cewar tana dakin yara may be ko wani. cikinsu ba lpy.jallabiya yasa ya fito ya wuce dakin su Fauzy dan yasan babu abinda aysha zatayi a dakinta.ganin wutar dakin a kashe sai abin ja daure masa kai dk da hkn bai yi kasa a gwiwa ba ,sai d yaje ya bude dakin ya kunna kwan dakin yaga kowa akan katifar sa yana barci hnkali kwance,wai hausawa suka ce dare mahutar bawa.

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now