GIDAN MIJINA

93 8 0
                                    

_______________________________________

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

Story &  Written by

MAMAN AFRAH

Page      
     28--29

  " 'Dakin da zaki zauna kuma?". Aysha ta tambaya fuskarta cike da alamun fargaba da kuma mamaki.

"E mana! Ko ba za ki nuna ba,in zabi d'akin da ya mini? dan ma kin samu har na kulaki na tambayeki,a matsayinki na mai jire gida"   Ummulkairi ta fad'a ta na wani yatsine fuska tare da d'ad'daga kai.

"Ba haka bane ". Aysha ta fad'a a sanyaye.

"To yaya ne? Koma dai menene ke kika sani"

Wucewa aysha ta yi ta nunawa direban wani daki mai dauke da toilet a ciki da komai na buk'ata,d'akin gyare yake tass kamar ma a kwai mutum a ciki.Bayan ta juyo ta ga Ummulkairi a inda ta barta tsaye,kallonta ta yi sanye ta ke da riga da wandon jeans gaba d'aya jikinta a d'ame sai karamin mayafi da tayi rolling dashi sai glases kwalba a idonta ,da hand back d'inta sak'ale a hannu d'aya hannun kuma wayarta ce.

"Ya dai? Kin ga shiga wacce ba ki iya irinta ba ko?Hmmm! Ai duk laifin Ya Kb ne daya kasa tsayawa ya za'bi macen da ta dace da shi,banda rashin sanin ciwon kai ace har karfe sha biyun rana mace ta na kwance tana barci sanye da kayan barci,maimakon a dau wanka na fitar hankali kafin miji ya fita kasuwa shima ya gani ya san ya ajiye mace ta nunawa sa'a a cikin gidansa, hmmm!"   ta ce tare da juyawa ta fara tafiya a yangance ta na wani yauk'i da kwarkwasa kamar tana gaban namiji.

Ita kuwa Aysha kallon jikinta ta yi sannan ta girgiza kai ta cigaba da tafiya za ta shige dakinta ta jiyo maganar Ummulkairi.

"Ki sama mun abin da zan saka a cikina domin yunwa na ke ji"

"Ban jin dadi"

Aysha ta fad'a.

"Kamar ya ba kya jin dad'i? Ai aikin bariki tilas ne". Ta ce ta juyawa ta kama hanyar d'akin da a ka kai mata kayanta ciki.Itama Aysha juyawa ta yi ta shiga d'aki tana jin kamar zata fadi ga damuwa, ga rashin karfin jiki ,ga kuma zuciyarta dake tashi kamar za tayi amai dan k'amshin turaren ummulkairi sosai ya kara tasar mata da zuciya.

  Haka ta daure ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta dauki doguwar riga marar nauyi ta sanya,dan yanzu duk tafi jin dadin sanya su.Sallar azzahar ta gabatar dan lokacin har d'aya da mintina, addu'a ta zauna tayi sosai sannan ta tashi ta linke hijabin da sallayar ta ajiye,wayarta ta dauka ta kira no Hafsa k'awarta jinta a kashe yasa ta kira ta Husna,ba a d'auka ba har ta katse sake kira tayi a karo na biyu sannan aka dauka bayan sun gaisa ta sanar da ita dan Allah idan ta samu lokaci ta iyo mata iloka da alewar madara,sannan ta siyo mata goruba sosai Husna tayi ta dariya tana tsokanarta wai d'an baba ya yi kira dole ne tazo, a yau da yamma ta kawo mata.Haka su ka yi sallama ta kashe wayar sannan ta dauki wani dankwali ta daure hancinta dashi ta shiga kicin ta dorawa Ummulkairi indomie mai attaruhu da albasa ,ta juye sannan ta fasa kwai guda uku ta sanya albasa da maggi da curry ta soya mata ta juye ta dakko su ta ajiye a falo ta zauna tana kallo a tv gyangyad'i ta ke yi dan wani barcin ta keji sosai kamar ma ba ta yi ba, dan cikin barci da kuma kasala yake sanyata ga kuma zazzabin dake gewayata jingina ta yi a kan kujerar har hular kanta ta zame daga kan nata gashin da ta sanya ribon ta daureshi ta kama karshen ta tufke jelar ta sauka har gadon bayanta sai wani sheki yake ya bayyana.

Ummulkhairi da yunwa ta hana ta sakat ta d'akko tsummar k'afarta ta nufo sashen Aysha,ko sallama babu haka ta afko falon tana shigowa idanunta su ka sauka a kan farar kyakkyawar fuskar Aysha da ta yi fayau da ita ga hancin nan kamar wanda a ka kara masa tsawo,baka hango komai sai gashin idonta da su kaeyi zagar zagar suka kwanta kamar ma ba barci take ba,gashin girarta kwantacce da kuma sajenta ,da gashin dake gaban goshinta duk sun kwanta sun kawata fuskar sosai ganinta haka ya tada hankalin Ummulkhairi kamar dai yau ta fara ganinta,ai idonta na sauka a kan gashin daya mata kama dana larabawa ko kuma indiyawa sai da zuciyarta ta yi wani tsalle kamar zata fito daga k'irjinta,sosai tayi mamakin ganin gashin Ayshan yarinya kamar wata yar shugaban kasa gabadaya alamomin jin dadi ne a tare da ita sai kawai taji ta raina kanta, gaba daya ayshan ta fita komai da komai kyau ,diri da cikar kirji anya kuwa ya Kb zai yarda ya aureta dan wanda ya ajiye mace kamar wannan me zai yi da ita kuma? tunowa da ta yi Hajiya za ta saka shi dole ya aureta sai ta ji hankalin ta ya dan kwanta,dan yanzu ma Hajiya ta aiko ta tazo ta yak'i soyayyarta ta samu gurbin zama a zuciyar yayanta dan idan yana ganinta yau da gobe dole zai ji yana sonta dan hakane ma suvka yiwa Daddy karyar Kaduna zata je shine ta tattaro kayanta ta taho nan.Wani haushi ne ya turniketa ta yi kan Aysha a zafafe kamar zata hauta da duka

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now