GIDAN MIJINA

78 4 0
                                    

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

    Short story

  Story & written by

   MAMAN AFRAH

MARUBUCIYAR
RAYUWAR MARYAMU
     
AND NOW

GIDAN MIJINA

Alhamdulillah I am back again🤗

*SADAUKARWA GA  BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏*

     Page  9_10

  
            "Magana fa nake miki aysha kinyi shiru"kawu habibu ya fada yana saurarenta
Tsayawa tayi da cin abincin take juya spoon din a cikin a bincin kawai ,dn ita bata san me zata ce masa ba.

"Wai humaira mesa ke kullum idan mutum yana bukatar amsarki sai yasha fama.

"Wlh umma kamar yanda na fada banma san waye ba a cikin motar ba,dan ni juyawa nayi kawai na tafi ba tare dana jira ganin mamallakin motar ba"cewar aysha taci gaba da cin abincinta dn so take tayi sauri ta tafi dan karfe uku saura yanzu,kar ta Makara islamiya.

"Shikenan ni daman nasan ba a fada aka watsa mata kwatar nan ba,dan ba halin aysha bane fada"cewar umma atika tana cigaba da tankadan garin tuwo.

"Hmm aunty ay kinsan mutane ne ynzu kansu kawai suka sani basa tunanin wani,indai mutum yasan yana da abin duniya to taka wanda bashi dashi ba komai bane.dan dai tace yayi attempting dn tsayawa,ta taho alamar zai bata hakuri yasan ya aikata ba daidai ba, Amma Wlh badan haka ba idan da zan yi ido hudu dashi sai na masa fiye da abinda ya mata.su masu kudi gani suke talaka bashi da gata shi ba kowa bane"kawu habibu ya fada yana cika yana batsewa.

Murmushi aysha tayi tana tashi ta ajiye plate dn data ci abinci ta shiga daki domin dakko jakar islamiyarta.

"Yanzu dai ay shikenan tunda wacce aka yiwa abin ita ta hakura,tunda kai bakada hakuri komai aka maka sai ka dau fansa,fisabilillahi rayuwa ta iyu a haka habibu,komai fa na duniya dan hakuri ne,duka ma duniyar nawa take"abba da fitowarsa kenan daga bayi ya fada yana ajiye butar hannunsa.

"Wannan haka yake Allah dai yasa mufi karfin zukatanmu" cewar umma.

"Amin"abba da kawu habibu suka fada a tare.

Aysha ta fito ta musu sallama domin tafiya islamiya,sakon gaisuwa ta bada a fadawa kakaninta.fita tayi ta barsu suna dan tattaunawa,ita kuma ta kama hanyar makaranta.

   A Bangaren kabeer da zuky kwa bai zame ko ina ba sai a kofar gdnsu  zuly,tun da suka baro Inda ya fallatsawa yarinyar kwata bai kuma cewa uffan ba.itama zuly ganin babu fuska yasa ta kama bakinta,sai dai lokaci zuwa lokaci takan juya ta kalleshi.tunda suka taho babu abinda yake sai cika baki da iska yana hurar da ita,sai kuma ya sauke ajiya zuciya.yana tsayar da motar ya koma ya jingina da kujera,Zuly ce ta juyo gaba daya ta kalleshi  Kafin ta fara mgn.

"Haba kb wai dn allah mesa ka damu kanka da abinda ya faru,kwata ce fa kawai ka watsa mata shima bawai da gangan ba,to amma kuma kazo kana damun kanka kamar wani wanda ya kade mutum ya mutu,kawai ka manta da ita ka dawo Normal ,yarinyar da ganinta kasan yar gdn talak.....

"Stop it! Dalla malama fitar min a mota"ya mata rai bace yana hayayyako mata.

Zuly data saki baki tana zuba kamar lalataccen fanfo,jin ya doko mata wata tsawa ya sanya ta tsorata.saurin bude kofar ta fita a hanzarce,ta rufo masa kofar jiki na rawa dn tasan halin kb ba mutuncci yanzu sai ya shuka mata tsiya.
Ganin ta bar masa jakarta ya bude kofar ya iyo cilli da ita,rufe kofar yayi,reverse yayi ya figi motar a 360.

    Zuly da har ta kama karamat kofar get din gdnsu,taji faduwar wani abu dimm,dake ko karan bude kofar da kb dn yayi bataji ba sbd tana rufe masa kofar ta juya tayi tafiyarta,dn tasa ba karamin aikinsa bane ya bula mata kasa ya kara gaba abinsa.ganin jakarta ce ya jefo mai tarin buks da handout wadanda take siya take ajiyewa dan ba wanda take karantawa daga ciki kawai tana siyane dn ta yiwa iyayenta basaja.dan bata shiga ko shiga class iyakarta bn samari,suyi ta zuwa Shopping da zuwa wajejen shakatawa daga karshe a dawo da ita gida.

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now