GIDAN MIJINA

65 1 0
                                    

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

Story & written by

MAMAN AFRAH

     Page
36--37

A gigice Ummulkhairi take kallon fuskar Kb tana zazzare idanu, nan take hawaye ya fara zarya a kumatunta.

"Ahayye to yanzu dai ba mijinki bane sai asan nayi umma ta gaida ashshe"Zuly tace tana fashewa da dariya.
Juyawa Ummulkhairi  tayi ta kalleta ga zafin mari ga na saki sannan itama tana kara mata da wani abin haushin.

"Baby zo mu wuce uzurinmu tunda komai ya kare kuma"Zuly tace tana kama  marfin motar ta shiga. Shima juyawa ya yi ya shiga ba tare da  ya k'ara magana ba. Jan motar ya yi a 360 suka bar layin. Ummulkhairi  jin jiri na d'ibanta yasa ta karasa jikin motar ta jingina, da taimakon dafa jikin motar ta karasa ta ciro makullin motar rufe motar ta yi, tasa kulle d'an sahu ta tsaida dan kwata kwata ba zata iya tuk'i ba.
 
Tun da ta shiga d'an sahun take aikin kuka, kuka take sosai dan ta rasa dame zata kwatanta halin da ta shiga yanzu cikin lokaci k'ank'ani, mai napep d'in ke bata hak'uri akan koma me ya sameta ta fawwalawa Allah.

"Dalla malam ka yi abin da ke gabanka"ta fad'a a zafafe.

"Ikon Allah, Allah  baki hak'uri"ya ce tare da maida hankali kan tuk'insa. Banza ta masa .dai dai k'ofar gidan data nuna masa ya tsaya a ransa yana kissima lallai dole tayi abin da take so indai a gidan nan take," to ko me yasa ba, a yawo da ita a mota? "ya tambayi kansa. Sauka tayi ta bude k'aramar kofar zata shiga,

"Hajia baki sallame ni bafa" ko waigoya bata yi ba bare ya sa ran zata masa magana, bare har a kai ga bashi  hak'k'insa da ya buk'ata.

"Allah  ya isa ki je na barki da Allah "ya ce tare da jan dan sahunsa ya bar wurin dan ua san ko shiga gidan ya yi yace a biyasa ba lallai hakan ya samu ba karshe ma ido  ua juye da mujiya.

  Tana shiga gidan da wani uban ihu ta hau stairs domin cimma Hajia, d'akin Hajia ta shiga babu ko sallama.

"Lafiya dai na ganki haka waye ya mutu?"

"Hajia wallahi  ya sake ni"ta ce tana fad'awa kan cinyar Hajia.

"Ya sake ki garin yaya haka ta faru?"
Nan Ummulkhairi  ta kwashe komai ta fad'a mata.

"Me ya kai ki, bayan kinsan sharadin da boka ya gindaya? "

"Wallahi  na manta Hajia"ta ce tana k'ara fashewa da kuka. Haka Hajia ta yi ta lallashinta ta ce zata san abin yi bayan tasan bokan ya ce duk wanda  ya yi kokarin maida auren sunan shi gawa.

*********

A can gida kwa lokacin da ake ta tafka wannan  kitimir mira, ita kwa Aysha tana can ta baiwa Hanatu Fauzy tana zaune da littafin addu, o i a hannunta tana karanta azkar din yamma bayan ta gama ta dinga jero addu, o i akan Allah ya shiga lamarinta dan ta san ba mantawa ya yi da ita ba yana sane da halin da take ciki. Gamawarta ke da wuya ta aji ye littafin ta jiyo dirin mota amma ba tasan ko motar waye  ba tsakanin Ummulkhairi  da Kb dan tasan duk din su basa nan. Ta ji lokacin da ya fita, yana fita itama ta fita a tata motar.

"Assalamu Alaikum " Kb ya ce wanda basu je ko ina da Zuly ba ya ji yana so ya ga Aysha shi ne ya ajiye Zulyn ya nufo gida. Jin muryar Kb cikin falonta, da mamaki kwarai a fuskarta take kallonshi mutumin da a shekara biyu bai shigo dakinta ba amma yau shi ne ya shigo har da sallama  fuskarshi a washe kamar gonar audiga.

"wa alaikumus salam"Ta amsa har lokacin bata bar mamaki ba.

"Eesha nah "ya fada yana rungumota jikinsa difff ta yi kamar an dauke wuta jin ta jikin mijinta da rabon da ya rabeta tun kan Abbanta ya bar duniya, tun cikin Fauzy bai da girma, tun sanda ta je gidansu yini ta dawo ta tarar dashi a d'akin Ummulkhairi. Kokarin kwace kanta take daga gareshi jin hawaye na neman sakko mata, riketa ya yi da karfi yadda ba zata iya k'wacewa ba.

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now