GIDAN MIJINA

64 2 0
                                    

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

Story & written by

MAMAN AFRAH

     Page 30--31

Sai da tasha kukanta ta koshi,sannan ta kira Hajia a waya ta shaida mata duk abin da ke wakana.Hajia taji dadin labarin da Ummulkhairi ta bata,na samun matsala tsakanin Aysha da Kb amma kuma kwata kwata bata ji dadin yadda Ummulkhairi tace ya biya Ayshan har sun tafi sun barta tsaye ,amma kuma tasan tunda dai akwai matsala tsakaninsu to tabbas da yiwuwar Ummulkhairin zata samu gurbin zama a wurin Kb.Sai dai itama Ummulkhairi ba tayi gigin fadawa Hajia cewar yana tare da wasu matan ba kamar yadda ta ji Aysha na baiwa kawayenta labari domin matukar Hajia ta san yana mu,amala da yan mata barkatai har ma yana iya rungumarsu to tabbas akwai matsala dan zata tsawatar masa ne akan abinda yake.Hakane ma ya bata damar boyewa Hajia domin tayi amfani da wannan damar tashi ta son mata ta ringa shiga wacce zai ke daukan hankalinsa har dai ta kai ga cimma nasara kamar yadda ta yiwa kanta alkawari,shisa da ta tashi fadawa Hajia tace akwai gagarumar matsala a tsakaninsu,amma kuma bata san wace iri bace.Bayan sun gama waya da Hajia a nan ta kwanta tana ta sake sake akan abinda ya faru yanzu tsakanin Aysha da Ya Kb ,tana tunanin yadda zata bullowa al,amarin har dai ta samu mafita ta tashi tana wani murmushi da ita kadai ta san ma,anarsa.

"Yaro man kaza lallai ma yarinyar nan ke har wata bariki kika iya hmmm! zaki san kin taboni"Ummulkhari ta fada tana mai tashi ta shiga bayi ta wanko fuskarta saboda kukan da tayi.tana fitowa ta bude akwatinta ta dauko wasu fitinannun riga da wando sabbi dal ,daman duk yawancin kayan sune takanas ta je ta siyo su ,sai data tako babbar akwati da kaya daker ta rufu saboda cika da tayi.Gaban madubi ta zauna ta sake sabon make up ,tana gamawa ta dauki kayan ta sanya ta fesa turare kala kala sannan ta dauko wani farin karamin mayafi tayi rolling dashi ta dauki wayoyinta ,fitowa tayi ta zauna gindin wasu bishiyoyi da aka jera kujeru a wurin domin shak'atawa,kujera d'aya ta ja ta zauna tana fuskantar inda part sin Kb yake yadda yana fitowa da ita zaiyi tozali.

Aysha kwa daurewa kawai take da ta rike Kb suke tafiya ji take kamar ta rike wuta kuma gaba d'aya sai abin da ta gani a wayarsa yake dawo mata.Haka zalika tayi hakane daman saboda Ummulkhairi,ba wai dan Kb din ba amma ganin ya bata hadin kai bai bayar da ita ba a gaban Ummulkhairi yasa ta ji dan saukin abinda take ji haka ta taimaka masa yayi wanka ta fiddo masa kaya ya sanya.yana tsaka da fesa turare wayarsa ta fara ringing daukan wayar yayi sai kuma ya maida kallonsa ga Aysha ya ga bama inda yake take kallo ba,kara kallon sunan mai kiran ya yi Zuly baby ,daukan wayar yayi ya fara magana.

"gskia ki bari sai zuwa gobe yau akwai abin da zan yi"Haka kawai yace ya kashe wayar.Maida hankalinsa yayi kan Aysha da ta sunkuyar da kanta kasa,karasawa yayi gabanta yasa hannu ya dago da kan nata abin mamaki sai ganin hawaye ya yi wani na bin wani "Eeshana me yake damunki ne?" Ya tambaya cike da kulawa.hannu tasa ta goge hawayen tare da jan hanci ba tare da tace dashi komai ba, a ranta tace

"Hmmm! Lallai namiji wato shi bai dauki wayar da ya yi a gabanta da wata macen zai iya bata mata rai ba?wato har ma tambayar damuwarta yake tabb maza sai a barsu"

"Ko bakya jin dadi ne?" ya tambayeta yana zaunawa akan gadon kusa da ita.

"Ba komai"tace ganin ya zauna kusa da ita har yana tambayar damuwarta wannan yasa ta ji ranta ya dan yi sanyi.haka suka zauna a falo suna d'an tab'a hira yace yana son yaci kosai da kunun gyada sosai ta ji dadi ganin bai da niyyar fita kamar yadda yake yi idan ya dawo daga kasuwa ya dad'a ficewa sai kuma lokacin kwanciya zai dawo.haka ya kamo hannunta suka tafi kicin domin ya tayata aiki dama tana da wake a gyare jikashi kawai tayi ta markada gyada kwa markadata suke kamar ta yin k'uli a ajiye in za,ayi amfani sai a dauka.Tana aikin suna hira abinsu a cikin hirar ne yake tambayarta zuwan Ummulkhairi take bashi labarin har da kayanta,dariya kawai yayi dan ya san shirin Hajia ne ita dai bazata canja hali ba.Har ta kammala ya tayata rikon tea flask din me kunu a ciki suka nufi part dinsa suna hira da yar dariya abinsu.Ummulkhairi ganin sun wuceta ko kallo bata ishi Kb ba ranta ya yi matukar baci,dan ita da farko tayi tunanin Kb fita zai yi shine Aysha ta rakoshi tana hangosu ta fara gyaggyarawa dan niyarta ta san duk yadda za tayi su fita tare amma sai taga sunyi hanyar kicin tana nan zaune suka fito tare suka nufi part din Kb .Bin su da kallo kawai take kamar taje ta shak'osu gaba d'ayansu haka take ji.sukwa akwala suka yi Kb ya jasu sallar magrib sannan suka ci abincin tare itama Aysha taci k'osan da kunun sosai a nan suka zauna suka sha hirarsu amma kuma ba,a minti sha biyar cikakke sai wata ta kira wayar Kb daga karshe ma sai wayar ya kashe gabaki d'aya.Cikin hirar tasu take tambayarshi zuwa gida wuni gobe ya amince mata haka sukayi sallar isha,i sukayi wankansu tare suka kwanta barci tare da gabatar da sunna,sosai Aysha ta shiga farinciki saboda rabonta da ta samu kulawa haka tun kan ta samu ciki.
Ummulkhairi kwa ana zaune anyi kwam akan kujera ana jiran fitowar Kb ,tunda ta ji Aysha na fadawa k'awayenta  kullum ya dawo kasuwa yana sake fita.Anan ta zauna har magriba sannan ta tashi rai bace ta hankada duka kujerun suka watse a kasa ta bar wurin ta koma daki😜cike da takaicin wannan rana amma kuma hakan bai sanya ta karaya ba kwafa take tana fadin "Allah kaimu gobe🙃

Washe gari da safe sai da Ummulkhairi ta dai daici lokacin fitar Ya Kb ya yi ta shiryo tsaf tana zuba kamshi direct part dinsa ta nufa ganin tun da Aysha ta hada break fast ta bar mata nata a kicin sai can taje ta dauka,da taji yunwa ta dameta dama da dare ma lemo tasha ta kwanta.Ganin sunki fitowa yasa ta je take buga kofar da karfi,Aysha ce tazo ta bud'e mata,kallon Aysha ta tsaya sama da kasa ganinta kamar wata ba india sanye take da fakistan riga da wando bakake kanta ko hula babu tayi kwalliya a fuskarta sai shek'i take abinta kayan sun amsheta sosai.Harara Ummulkhairi ta gallawa Aysha dan duk haushinta take ji kafin ta budi baki tace

"Ba wurinki na zo ba malama ,wurin d'an uwana na zo ko shima bazan samu damar ganinshi ba??" Ta tamabaya tana mata kallon up & dawn.Dariya ce ta so subucewa Aysha ganin shigar da Ummulkhairi ta yi sanye take da doguwar rigar atamfa atamfar green mai ratsin yellow sai ta yafa karamin mayafi yellow ansha kwalliyar nan,ba komai bane ya baiwa Aysha dariya sai yadda rigar ta yiwa Ummulkhairi kamar wanda aka dauki buhun hatsi aka sanyawa riga🤣.

"In ki ka yi hak'uri ma yanzu zai fito"Aysha ta fada tare da juyawa ta rufo kofar dan kar dariya ta kwace mata ta ballo ruwa hallaw.Tsaki ta yi tare da komawa gefe guda ta kama k'ugu ta tsaya.Jim kadan sai gasu sun fito tare.

"Barka da safiya Ya Kb"ta fada tana wani tsuke baki.

"Barkanki dai"Ya Kb ya fada hankalinsa akan Aysha.

"Yaya dama inaso ka sauke ni a gdn su wata friend dina"

"Hakan ba zai samu ba "Ya fada tare da sanya hannu a aljihu ya dakko kudi ya mika mata.

"Gashi ki hau napep "ya juya suka jera da Aysha da zata rakashi gun motarshi.itakwa  Ummulkhairi kallon kud'in ta tsaya saroro haushi tare da tarin bakin ciki sun mamaye mata zuciya.Tana nan tsaye har motar Kb ta bar gidan Aysha ta dawo  dai dai zata shiga daki Ummulkhairi tace

"Duk jarabar mutum dai bai isa ya raban da dan uwana ba" murmushi kawai Aysha tayi ta shigewarta daki ba tare da ta tanka ta ba.itama dakinta ta shige tayi jifa da jakarta da kudin da Ya Kb  ya bata.

Aysha kwa shiri ta sake cikin less mai shegen kyau ta yafa mayafi ta dakko keys din part dinta dana Ya Kb ta rurrufe ta fito ta tari napep ta tafi gidansu.Ta tarar gidan babu lpia domin kwa Abbanta ne bashi da lpia wani abu ya fito masa a gadon baya dan ko fita ma baya yi.Amma idan suka yi waya Umma sai tace kowa lpia k'alaw kai ko Abban ma sukan yi waya amma bata taba fahimtar baya jin dadi ba.


     BANI CAJI🙄

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now